← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 75

Sashe 72

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiyar ta kasance mai nisan gaske, domin Bokezuwa yana can cikin karkara, a wata lungu da ke da nisa daga birni. Sun fita tun da sassafe, Fawaaz yana tuka motar, yayin da Nabeeha ke zaune kusa da shi, zuciyarta cike da tunani.

"Fawaaz, ina jin kamar in yi kuka." Ta furta a hankali, tana lumshe idanu.

Ya dan kalleta, yana murmushi. "Kuka kuma? Me ya faru?"

Ta sauke ajiyar zuciya. "Tunani nake yi… A nan ne Ammi ta girma, ta rayu da danginta. Amma yanzu babu su, babu komai."

Fawaaz ya dora hannunsa kan nata a hankali. "Ina jin ki, Nabeeha. Amma ki sani, zuwanmu nan wata hanya ce ta sabunta tarihin da ya shuɗe. Hakan ma babbar ni'ima ce."

Ta jinjina kai, tana jin wani sanyi yana ratsata.

Sun dauki kusan awa uku a hanya kafin suka iso bakin kauyen. Titin kauyen ba shi da kyau sosai, cike yake da yashi da ƙurare. Yayin da suka shiga cikin garin, sai Nabeeha ta fara karewa wuraren kallo. Kauyen yana da saukin kai, duk da cewa gine-ginen sa sun nuna cewa lokaci ya ja.

Tsaffin gidaje ne a kewayensu, yawancinsu da bulo aka gina su, wasu kuma da tubali. A gefe, akwai wata babbar rijiya da ke tsakanin itatuwa, inda wasu dattawa ke zazzaune suna hira. Wasu mata kuma suna gefen wata bishiya suna yankan ganye da wasu 'yan mata ke taya su.

Nabeeha ta cika da mamaki, zuciyarta na bugawa da sauri. " Yaa Fawaaz, kenan a nan ne Ammi ta girma?"

"Eh, a nan ne asalinta."

Wata tsohuwa da ke zaune kusa da rijiya ta lura da su, ta fara kallonsu da kyau. Ganin su a cikin mota mai kyau ya jawo hankalin mutanen kauyen da dama.

Lokacin da suka yi parking a wani yanki da ake kiran "Tashar Bokezuwa," wasu yara suka fara matsowa suna kallonsu da sha’awa. Fawaaz ya fita daga mota, ya zagaya gefen Nabeeha ya bude mata kofa.

Tana fita, tsohuwar da ke zaune kusa da rijiya ta miƙe, tana takowa da sandarta.

"Wannan ai kamar Zainabu ce!" Ta fada da mamaki.

Nabeeha ta kalleta da sauri. "Zainabu?"

Tsohuwar ta karasa kusa da su, tana kare mata kallo. "Ke ‘yar Zaytunah ce ko?"

Gaban Nabeeha ya fadi. "Eh, ni ce."

Tsohuwar ta dafe kanta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah mai iko! Dama har yau Zaytunah tana raye?"

Hawayen da ke cike da idon Nabeeha suka silalo. "Eh, tana raye."

Tsohuwar ta saki ajiyar zuciya, tana fadin, "Toh Alhamdulillah! Ai tun lokacin da aka ce ta bar garin nan, ba mu sake jin duriyarta ba."

Wasu dattawa da ke zaune a wajen suka matsa kusa, suna tambayar me ke faruwa.

Wani tsoho mai farin gemu ya karaso, yana tambaya. "Wai ‘yar wa ce wannan?"

Tsohuwar ta kalleshi da mamaki. "Wannan ‘yar Zaytunah ce, yaran da sukayi aure . Zaytunah da rumanah. Dangin makarantar allo. Sansanin marigayi malam idi bokezuwa da malam nata'ala. "

Sai murmurmurmi ya bayyana a fuskokin dattawan. "Subhanallah! Ashe dai ta rayu? Allah ya kai mu zamanin ganin ‘yarta!"

Bayan dogon hira da dattawan, sai suka nufi inda tsohon gidan mahaifiyar ta ta rayu. Duk da cewa gidan yanzu ya rufta da yawa, har yanzu yana nan da sifarsa. Gidane mai bango da akayi da tubali, a kofar sa kuwa akwai wata tsohuwar bishiya mai inuwar da ke rufe rabin harabar gidan.

Nabeeha ta tsaya tana kallon gidan da mamaki. "Ya fawaaz, nan ne Ammi ta taso?"

Ya jinjina kai. "Eh, a nan ne gidan iyayenta."

Tsohuwar ta karasa tana cewa, "Wannan gidan su dangin mahaifiyarki ne, Anan ta girma da mahaifanta kafin wannan bala'in ya raba su da juna."

Nabeeha ta dan dafa bango, tana jin wani iri a zuciyarta. Tana iya hango rayuwar da mahaifiyarta ta yi a nan.

Tsohuwar ta ci gaba da magana cikin taushin murya. "Mahaifiyarki yarinyace mai hankali da biyayya. Duk mutanen nan sun santa, sun san halinta."

Hawaye suka cika idon Nabeeha. "Nagode da kuka gaya min. Ammi ba ta taba cewa da yawa game da rayuwarta a nan ba."

Tsohuwar ta yi murmushi. "Ba abin mamaki bane. Wata rana za ku kawo ta, mu sake jin daɗin kasancewa da ita."

Bayan sun jima suna tattaunawa, suka sha ruwa daga rijiya sannan suka yi sallama da dattawan. Suka dan musu alheri na kudi.

Lokacin da suka shiga mota, Nabeeha ta juyo tana kallo ta taga, zuciyarta cike da tunani.

"Ya fawaaz, mun taba zuwa garuruwa. amma ban taba jin irin wannan ba."

Fawaaz ya kalleta, yana riko hannunta. "Wannan ne asalinki, Nabeeha. Kuma ina fatan kin ji dadin sanin shi."

Ta jinjina kai, tana murmushi. "Eh, naji dadin sanin shi. Kuma zan dawo nan wata rana."

Ya shafa kanta cikin kulawa. "Ko da yake, sai kin gama shan kukan tunani."

Ta yi dariya cikin hawaye. "Toh ai ba zan daina jin kaunar wannan wuri ba."

Daga nan suka tada mota, suka bar kauyen cikin natsuwa, zuciyar Nabeeha cike da soyayya da alfahari da tushenta.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:64_

Dare ya zama safiya, safiya ta zama rana, rana ta zama yammaci. Lalle Allah buwayi ne gagara misali.

Kwanaki nata shudewa, kowane bangare na cikin littafin rayuwar su na tafiya dai dai Alhamdulillah. Sai dan abunda ba a rasa ba na ups and downs . Wanda baki daya rayuwa tanada nata irin jarabawar kaddarar da take zuwa Wa kowane bawa... Wala kyakkyawa Wala akasin haka.

Nabeeha ta runtse idanu, tana jin yadda kalmomin Fawaaz ke ratsata har cikin zuciyarta. Hannayensa da ke cikin nata sun ba ta natsuwa da kwanciyar hankali. Cikin rawar murya ta ce,

"Ya fwaaz, ina jin tsoro..."

Ya janye daga rungumar ta kadan, yana duban cikin idanunta. "Tsoro kuma, my love? Me ya faru?"

Ta sauke ajiyar zuciya, tana murza yatsun hannunsa. "Ina jin kamar ba zan iya ba… Ina jin kamar wannan babban nauyi ne a kaina."

Fawaaz ya dora goshinsa kan nata, yana murmushi cikin so da kulawa. "Ke dai bari, Habibty! Allah ne ke bayar da rabo, kuma shi ke saukakewa. Babu abin da zai same ki sai alkhairi. Ni zan kasance tare da ke a kowane mataki. Ba zan bar ki kin ji ƙunci ba, ba zan bari ki ji wahala ba. Zan dinga tare da ke, zan taimake ki da duk abinda kike bukata."

Ya sake shafa bayanta, yana magana cikin murya mai taushi,

"Allah ya sa ki haihu lafiya, Allah ya kiyaye ki, ya kare min ke da babyna. Allah ya sa ki zama uwar yara masu albarka. Allah ya albarkaci wannan jaririn da ke cikinki. Allah ya tsare ku, ya sa ku kasance lafiya a koda yaushe!"

Ta dinga jin addu'o’insa kamar ana yayyafa mata ruwan sanyi. Hawaye suka ci gaba da gudu a fuskarta.

"Ameen, Yaa Fawaaz... Na gode da kaunar da kake min. Ka sa na ji kwarin gwiwa. Ka sa na ji ina da matsuguni da masoyi na hakika."

Fawaaz ya kai bakinsa gefen kunnenta, ya ce cikin radadi da kauna,

"Kin kasance mafi daraja a gare ni, Nabeeha. Ko da za a bani duniya a madadin ki, ba zan karba ba. Ke ce rayuwata, kuma yanzu kin kara min wata rayuwar da zan runguma cikin ƙauna da kulawa!"

Ta rufe idanunta, tana jin yadda soyayyarsa ke mamaye zuciyarta.

Bayan sun bar asibiti, Fawaaz ya mai da hankali sosai wajen kula da Nabeeha. A kullum yana sa ido a kanta, yana tabbatar da cewa ba ta yi komai mai wahala ba. Duk inda za ta je, shi zai kai ta. Duk abinda take so, zai samo mata.

Akwai lokacin da ta fara jin yunwa cikin dare. Tana kwance a gadonsu, tana jin yadda cikinta ke kara motsi. Sai ta yi dariya a hankali, ta shafi cikinta.

Fawaaz, wanda ke zaune kusa da ita yana karanta wata takarda, ya lura da murmushinta.

"Me ya faru?" Ya tambaya, yana kallonta da kulawa.

Ta yi dariya a hankali. "Ina jin yunwa."

Ya zaro idanu da mamaki. "Yunwa da daddare? Me kike so na samo miki?"

Ta kwanta gefensa, tana kallon sa da idanuwanta masu cike da so. "Ina jin kamar zan ci lemun tsami da danyar kubewa."

Ya zaro ido. "Lemun tsami da kubewa? Wannan wace irin haduwa ce?"

Ta fashe da dariya. "Ni dai haka nake jin so."

Ya girgiza kai, yana murmushi. "Ai ba komai! Bari na je na nemo miki. Ko da kuwa zan tashi na je wajen mai sayarwa a daren nan, zan yi domin na tabbatar kin samu abinda kike so."

Ta kalleshi da so da kauna. "Nagode, masoyina."

Ya matsa kusa da ita, ya dafa cikinta a hankali, yana magana cikin taushi. "Ina yi wa babyna sannu. Ina fatan yana jin dadi a cikin Ammi?"

Ta lumshe idanu, tana jin wani irin farin ciki ya rufe ta. "Muna jin daɗi, ya Fawaaz. Ka sa rayuwata ta zama mafi kyan da na taba ji a duniya."
Chapter 72 · 0% Book details