Sashe 73
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya sanya tafin hannunsa a fuskarta, yana shafa kuncinta cikin ƙauna. "Ke ma kin sa tawa ta zama mai ma'ana, Nabeeha. Kuma zan ci gaba da ƙaunar ki da renon ki har abada."
A haka suka ci gaba da soyayyarsu, cikin kula da juna da tarairaya. Kowace rana, Fawaaz yana ƙara fahimtar yadda soyayyarsa ga Nabeeha ke zurfafa, yana kara godewa Allah da Ya albarkace su da wannan kyauta.
A kullum soyayya da kulawar da Fawaaz yake wa Nabeeha na ƙara girma da zurfi. Duk inda ta juya, a shirye yake don tarairayarta. Duk damuwarta, a shirye yake don share mata ita. Duk wahalarta, a shirye yake don daukar ta a kansa.
Yanzu haka suna zaune a lambun gidan su, inda iskar sanyi ke kadawa, tana busa gashin kanta a hankali. Fawaaz yana zaune a gefenta, hannunsa rike da nata, yana wasa da yatsunta cikin kwanciyar hankali.
"Nabeeha," ya kira sunanta da murya mai laushi, "Kin san ko?"
Ta kalle shi, tana murmushi. "Me zan sani?"
Ya sake matse hannunta a cikin nasa, yana kallonta da ido mai cike da kauna. "Kin san cewa ina ƙaunarki fiye da komai a duniya? Kin san cewa tun ranar da Allah ya hada mu, rayuwata ta samu ma'ana? Kin san cewa idan har za a tsaga zuciyata, babu abin da za a samu face ke?"
Ta lumshe ido, tana jin yadda kalmomin sa ke ratsata kamar ana yayyafa mata zuma a zuciya.
"Hayatim." ta furta cikin sanyin murya.
Ya ɗora tafin hannunsa a saman cikinta, yana shafa shi cikin kulawa. "Yanzu ba ke kaɗai ba, Nabeeha. Kina da wani babban matsayi a zuciyata, amma wannan jaririn da ke cikinki… shi ne shaida ta babbar kyauta da Allah ya bani. Allah ya albarkace ni da ke, kuma yanzu Ya kara albarkata da wata ƙwarya daga gare ni. Ina son ki, Nabeeha. Kuma zan kasance tare da ke a koda yaushe."
Hawaye suka cika mata ido, ta kasa furta komai. Sai kawai ta kai kanta kan kafadarsa, ta jingina a jikin sa.
Fawaaz ya saki ajiyar zuciya, yana jin yadda jikin ta ke dumama nasa. Ya kwantar da kansa a gefen nata, yana jin bugun zuciyarta na tafiya da nasa.
"Daga yau, Nabeeha," ya cigaba da magana cikin natsuwa, "Ba zan bari ki ji wata damuwa ba. Ba zan bari ki sha wahala ba. Zan kula da ke kamar wata sarauniya. Zan dinga sadaukar da komai don farin cikin ki. Zan yi miki hidima fiye da yadda na taba yi. Domin ke ce hasken rayuwata. Ke ce farin cikina. Ke ce mafarkin da ya zama gaskiya."
Nabeeha ta dago fuskarta daga kafadarsa, tana kallon cikin idanunsa da suka cika da shauƙi. "Ya Fawaaz, na gode... Ba zan iya misalta irin godiyar da nake maka ba. Ka sa rayuwata ta zama cikakkiya. Allah ya bar ka da ni har abada."
Ya sakar mata murmushi, yana shafa kumatunta da tafin hannunsa. "Allah ya sa mu rayu tare har karshen rayuwarmu. Allah ya bar mu cikin soyayya da aminci. Allah ya albarkaci wannan rabon da Ya ba mu, ya raya mana shi lafiya."
Ta lumshe idanu, tana jin yadda addu’o’insa ke shigarta har cikin zuciya.
Bayan kwanaki, Fawaaz ya dage da kula da Nabeeha fiye da da. Idan ta tashi, yana a gefenta. Idan ta zauna, yana bata goyon baya. Idan ta yi gajiya, shi ne mai shafa mata bayanta.
Ranar da suka je ziyarar gida, Hajiya Zaytunah ta yi mamakin yadda Fawaaz ke lallashinta. Yana rike mata hannu kamar wata jaririya, yana tabbatar da cewa ba ta yi wani abu da zai gajiyar da ita ba.
Hajiya Zaytunah ta dubi Alhaji Uzairu da murmushi. "Kana ganin yadda Fawaaz ke kula da ‘yar ka? Ya fi yadda kowanne uba zai yi wa diyarsa. Wannan abu sai wanda Allah ya sanya soyayya a zuciyarsa."
Alhaji Uzairu ya girgiza kai cikin jin dadi. "Tabbas Nabeeha ta samu nagartaccen miji. Muna yi musu fatan alheri da zaman lafiya mai dorewa."
Fawaaz ya dubi Nabeeha, ya matsa kusa da ita, yana furta cikin radadi da kulawa,
"My Queen, zan iya raba jinina da ke, amma ba zan iya barin ki ki wahala ba. Ina son ki, Nabeeha. Har abada!"
Hajiya Zaytunah da Alhaji Uzairu suka kalli juna da murmushi, yayin da Nabeeha ta lumshe idanu, tana jin yadda soyayyar Fawaaz ke kara ratsa zuciyarta, tana mai tabbatar da cewa shi ne kadai wanda Allah Ya aiko mata a matsayin abokin rayuwarta na hakika.
Kwana-kwanan nan, rayuwar Nabeeha ta zama kamar mafarki. Fawaaz ya cika alkawarinsa na kula da ita, ba tare da ya bari ta ji wani nauyi ko damuwa ba. Idanunta sun fi koyaushe cike da farin ciki, fuskarta tana cike da annashuwa, kuma zuciyarta ta cika da kwanciyar hankali.
Rana ce ta Jumu’a, inda suka shirya tafiya gida domin kai wa iyayenta ziyara. Fawaaz ya tabbatar da cewa Nabeeha ta huta sosai kafin su tafi. Ya zabi mata kaya masu laushi da dadi, sannan ya taimaka mata ta saka hijabinta yadda ba zai dameta ba.
Da suka isa gidan, Hajiya Zaytunah ta tarbe su da murmushi mai cike da farin ciki. Nabeeha ta yi saurin rungume mahaifiyarta, tana jin yadda soyayyarta ke kara girma a zuciyarta.
"Ammi, na yi kewar ki sosai!"
Hajiya Zaytunah ta shafa kanta da kulawa. "Ni ma na yi kewar ki, ‘yata. Kina lafiya kuwa?"
Kafin ta amsa, Fawaaz ya riga ta da cewa, "Ta na lafiya, Ammi. Ni na tabbatar da hakan!"
Dariya suka yi gaba ɗaya, sannan suka zauna domin yin hira. A lokacin da Alhaji Uzairu ya shigo, Fawaaz ya miƙe da girmamawa, yana gaishe shi.
"Ya jikin Amaryar tamu?" Alhaji Uzairu ya tambaya, yana murmushi.
Fawaaz ya kalli Nabeeha da idanuwansa masu cike da ƙauna. "Lafiyarta kalau, Alhaji. Allah na tare da ita."
A haka suka ci gaba da hira, suna jin daɗin kasancewa tare.
Bayan sun gama gidan su Nabeeha, suka wuce gidan Alhaji Amiru, inda suka same shi tare da Gwaggo Zainabu. Gwaggo Zainabu ta ji daɗin ganin Nabeeha da cikinta yana girma cikin lafiya.
"Allah ya sauke ki lafiya, jikata."
"Ameen, Gwaggo. Na gode."
Fawaaz ya zauna kusa da ita, yana jinjina mata don girmamawa. "Gwaggo, ina fata kin yi sallah lafiya."
Ta gyada kai, tana murmushi. "Alhamdulillah, Fawaaz. Kai kuwa, ya mai kula da Nabeeha?"
Ya lumshe ido da murmushi. "Ni dai granny na fara ji kamar ni ne mai dauke da shi. Domin ba zan iya ganin ta cikin wahala ba. Ita ce duniya ta gaba daya."
Nabeeha ta ji yadda zuciyarta ta karye da kauna. Sai ta dan matsa kusa da shi, tana jin nutsuwa a jikinsa.
Gwaggo Zainabu ta yi murmushi, tana fadin: "Allah ya bar ku tare cikin zaman lafiya da farin ciki."
"Ameen," suka amsa a tare.
Daga nan suka shirya tafiya zuwa kauyen Bokezuwa, tushen iyayen Nabeeha. Fawaaz ya tsara tafiyar ne saboda yana so Nabeeha ta ji farin ciki da kasancewa da danginta.
Lokacin da suka isa, jama’a sun tarbe su da farin ciki. Duk da cewa shekaru sun shude, mutanen kauyen sun san su Nabeeha da labarin mahaifiyarta, Hajiya Zaytunah.
Wata tsohuwa daga cikin dangin mahaifiyarta ta rike hannun Nabeeha, tana fadin: "Kin yi kama da mahaifiyarki lokacin tana yarinya. Allah ya kara miki albarka, ‘yata."
Nabeeha ta jinjinawa tsohuwar, hawaye suna cika idonta. Fawaaz kuwa yana gefe yana kallon matarsa da wani irin shauki da ƙauna.
"Mun gode da tarba, Inna," ya fada cikin ladabi.
Tsohuwar ta dube shi, sannan ta yi murmushi. "Kai ne mijin ‘yar tawa?"
"Eh, Inna."
Ta dube shi da kulawa, sannan ta girgiza kai. "Allah ya albarkaci zamanku. Ka kula da ita, kamar yadda ka alkawarta."
Fawaaz ya kama hannun Nabeeha, ya sumbata a saman tafin hannunta. "Zan kula da ita fiye da yadda nake kula da kaina, Inna."
Mutanen kauyen suka yi dariya, suna yabawa da irin soyayyar da Fawaaz ke nunawa Nabeeha.
Bayan sun dawo daga tafiya, Nabeeha ta fara jin sauyin jikinta. Cikinta yana kara girma, kuma Fawaaz ya dinga kula da ita fiye da yadda ya saba.
Rana ce ya dawo daga aiki, ya same ta tana zaune a falo, tana kallon cikin ta da murmushi.
Ya durkusa a gabanta, ya dafa cikinta da tafin hannunsa. "Yaya babyna?"
Ta kalle shi tana murmushi. "Babynka yana cikin kwanciyar hankali. Yana jin sanyin addu’o’inka."
Ya lumshe ido, yana fadin: "Allah ya sauke ki lafiya, Nabeeha. Allah ya ba mu ikon tarbiyyar wannan yaron daidai da yadda zai zama mai amfani a duniya."
Ta furta cikin radadi da kauna: "Ameen, Fawaaz. Allah ya kara mana soyayya."
Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta a kirjinsa. "Soyayyarmu ba zata taba raguwa ba, Nabeeha. Sai dai ta kara girma har abada!"
Haka rayuwarsu ta ci gaba, cikin kulawa, addu’a, da soyayya ta gaskiya..
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_(Completed)_
*_PAGE:65_*
_(shafin karshe/The end/Episode Finale)✅_