Sashe 52
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hammad ya numfasa, sannan ya ce, "Ina son na san ka. Amma zai ɗauki lokaci kafin na iya mantawa da komai."
Nabeeha ta kalle shi, sannan ta dubi mahaifinsu. "Ni ma haka nake ji."
Uzairu ya gyaɗa kai, hawaye na taruwa a idanuwansa. "Nagode. Wannan damar ce babba a gare ni."
A wannan rana, an ɗora tushen wata sabuwar rayuwa. Ba wai komai zai dawo kamar da ba, amma a kalla, an fara mataki na gafara da fahimtar juna.
Akwai sauran rina a kaba. Amma lokaci ne zai nuna yadda abubuwa za su kasance.
Bayan taron da suka yi da Alhaji Uzairu, zuciyar Zaytunah ta cika da tunani. Ko da yake ta ba shi dama ya riƙa ganin ‘ya’yansa, hakan bai sauƙaƙa mata raɗaɗin abin da ya faru a baya ba.
Tana zaune a ɗakinta, tana kallo daga tagar da ke fuskantar lambun gidan. Hasken yamma yana haskaka fuskar ta. Tana jin wani abu mai ƙuna yana yawo a KIRJIN ta, tunani ne, shakku ne, da kuma wasu ƙananan jin daɗi da ba ta san ta yaya suka zo ba.
Major General Dawud ya shigo cikin ɗakin a hankali. Bai ce komai ba har sai da ya zauna kusa da ita.
"Zaytunah, me kike tunani?" Ya tambaya da natsuwa.
Ta ɗanyi jim, kafin ta amsa. "Ina tunanin ko da gaske Uzairu yanaa nadama."
Major General ya lumshe ido na ɗan lokaci. "Mutum na iya yin nadama, amma hakan ba yana nufin cewa za a goge abin da ya aikata ba."
Zaytunah ta kalle shi. "To yaya zan yi? Ya kamata in gafarta masa gaba ɗaya?"
Ya numfasa. "Gafara ba dole ba ce. Amma idan za ki yi, ki yi don ki sami sauƙi a zuciyarki. Idan kuma ba za ki iya ba, to kada ki tilasta wa kanki."
Zaytunah ta yi shiru, tana nazari.
A bangaren Alhaji Uzairu, zuciyarsa ta kasa samun sukuni. Duk da cewa Zaytunah ta ba shi dama ya ga ‘ya’yansa, bai jin cewa hakan ya wadatar.
A daren ranar, sai da ya tattara jikinsa, ya nufi gidan Gwaggo Hafsat. Ya san cewa ita ce wadda ta riƙe Zaytunah tsawon shekaru, kuma tana da matsayi mai muhimmanci a rayuwarta.
A lokacin da ya isa, Gwaggo Hafsat tana zaune bisa darduma tana lazimi. Ya tsaya a bakin ƙofa, ya saki ajiyar zuciya.
"Shigo, Uzairu," ta ce, ba tare da ta kalle shi ba.
Ya matsa cikin ɗakin a hankali, ya durƙusa a gabanta.
"Gwaggo Hafsat," ya kira sunanta cikin muryar nadama. "Na san cewa ba zan iya gyara abin da ya faru ba, amma ina roƙonki ki faɗa min, shin akwai wata dama da zan iya samu daga Zaytunah?"
Gwaggo Hafsat ta ɗago ido ta kalle shi da tsantsar hikima. "Uzairu, kai ka fi kowa sanin irin zaman da ka yi mata a baya. Idan har za ka iya jira, ka jira. Idan kuma ka san ba za ka iya ba, to ka bar ta da zaman lafiya."
Uzairu ya runtse ido. "Zan jira," ya ce da ƙarfi. "Ko da shekara nawa ne, zan jira har sai ta gafarta min."
Gwaggo Hafsat ta jinjina kai. "To mu gani."
A bangaren Nabeeha da Hammad, har yanzu suna kokarin fahimtar sabon yanayin da suka shiga.
A wata rana, suna zaune a cikin falon gidan, kowannensu yana cikin tunani. Hammad ne ya fara magana.
"Nabeeha, kin shirya haduwa da mahaifinmu nan gaba?"
Ta ɗanyi jim. "Gaskiya ban sani ba. Har yanzu zuciyata tana cike da shakku."
Hammad ya gyada kai. "Ni kuwa ina son in san shi, amma bana son in ji kamar muna tilasta miki."
Nabeeha ta saki ajiyar zuciya. "Zan yi tunani akai."
A daidai lokacin, wani saƙo ya shigo wayarta daga Muhammad (ɗan Hajiya Rumanah).
Muhammad: "Ina fata kuna lafiya. Yaya kuke ji game da mahaifinku?"
Nabeeha ta kalli saƙon, ta yi jim, kafin ta amsa.
Nabeeha: "Ba sauƙi. Amma muna ƙoƙarin fahimta."
Muhammad ya dawo da amsa da sauri.
Muhammad: "Ni ma har yanzu na kasa fahimtar mahaifiyata. Abin yana da wahala."
Nabeeha ta fahimci cewa ba ita kaɗai ce ke cikin matsala ba.
A gefe guda, bayan sakin da Uzairu ya musu, Hajiya Rumanah, Ladi da Karama sun tsinci kansu a cikin ruɗani.
Suna zaune a wani ɗaki, kowannensu da damuwa a fuska.
Ladi ta ce cikin murya mai rauni. "Mun rasa komai."
Karama ta gyaɗa kai. "Ba mu san inda za mu dosa ba."
Rumanah ta ja dogon numfashi. "Mu muka jefa kanmu cikin wannan hali. Amma har yanzu akwai hanya guda—muna da ɗanmu Muhammad. Dole ne mu same shi, ko da kuwa yana fushi da mu."
Dukkansu suka yi shiru. Tabbas, suna bukatar mafita. Amma tambaya ita ce—shin akwai wani lokaci da za a iya gyara wannan lamari?
Yayin da kowa ke cikin tunani da fuskantar matsalolinsa, lokaci yana tafiya. Wata sabuwar rayuwa na tafe, amma har yanzu akwai tambayoyi da ba a samu amsarsu ba.
Shin Zaytunah za ta iya gafarta wa Uzairu gaba ɗaya?
Shin Nabeeha da Hammad za su iya karɓar mahaifinsu?
Shin Rumanah, Ladi da Karama za su iya gyara barnarsu?
Shin Muhammad zai karɓi mahaifiyarsa bayan asirin da ya tonu?
ADVERT👇
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)
INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!
🌟 Mene ne za ku samu?
Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.
Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.
Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.
Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.
Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.
Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.
📍 Adireshi:
Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.
📞 Tuntuɓe mu:
WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107
Instagram: @yerwaincense_and_more
Facebook: @yerwacollection
Twitter:Hafsaaat00
🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1
🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!
🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE:46_
Da dare ne Muhammad ke kallon faifon bidiyon, yana ci gaba da nazari kan abubuwan da suka gabata. Duk da kokarin sa na danne zuciyarsa, zuciyarsa ta kasa jurewa. Ya lumshe ido, hawaye suka sauko masa.
A cikin ransa yana jin radadin abin da mahaifiyarsa ta aikata, amma yana ganin shi ne mai laifi. Idan aka dubi fuskar sa kadai, da alama za a iya hango wannan laifi da mahaifiyarsa ta aikata. Kunya ce ta lullube shi gaba daya. Idan kaka duba fuska, zai iya ganin laifin da mahaifiyarsa ta tafka a bayyane. Don haka, ya yanke shawarar hakura da auren Nabeeha.
Yana jin faduwar zuciya, amma yana son a yafe wa mahaifiyarsa, don haka sai ya mike, ya dauro alwala, sannan ya yi sallar nafila domin neman zabin Allah. Yana mai rokon Ubangiji da ya taimaka masa ya dauki wannan mataki da ya dace.
Da safe kuwa, yana gama shiri, ya wuce gidan kanin mahaifinsa, wato Alhaji Uzairu, don ya sanar masa da shawarar da ya yanke. A tare da fuskarsa da natsuwa, ya ce. Bayan sun gaysa ne yace da shi,
"Kawu Uzairu, na yanke shawarar fasa auren Nabeeha. Ina jin cewa idan na auri Nabeeha, zan zama kamar mai cin amana. Ba na jin cewa zan iya jurewa idan aka tuno wannan lamari a kullum. Don haka, na yanke shawara zan janye."
Alhaji Uzairu ya yi shiru na dan lokaci, yana nazarin yadda zai amsa. Daga nan ya nufi wajen yayansa, wato Alhaji Amiru, ya sanar da shi wannan batu.
Alhaji Amiru ya ji mamaki, ya danne zuciyarsa kafin ya ce, "Muhammad ya riga ya dauki matakin da yake ganin ya dace, amma wannan abu ba abu ne da za a yi shiru a kansa ba. Dole ne mu tafi mu sanar da su Major General Dawud."
Ba tare da bata lokaci ba, suka rankaya zuwa birnin Noka domin ganawa da Major General Dawud.
______
A wannan rana, bayan taron da suka yi a birnin Noka, Zaytunah ta yanke shawarar amincewa da komawa gidan mijinta, Alhaji Uzairu. Duk da haka, ta gindaya sharadi daya, komawarta sai bayan bikin Nabeeha.
Gwaggo Hafsat ta kalli Zaytunah cike da tausayi. "Kin tabbatar da cewa kin shirya?"
Zaytunah ta lumshe idanu, sannan ta numfasa cikin kwanciyar hankali. "Na riga na yanke shawara. Amma sai bayan bikin Nabeeha."
A ranar dinner ɗin su Humyrah, kawayen amaryar sun shirya tsaf, kowacce ta yi ado cikin kwalliyar da ta dace da daren. An tsara cewa tawagar amarya za su shiga tare da abokan ango domin fara shagalin bikin cikin tsari.
Tun da aka fara shirye-shiryen tafiya, Nabeeha ta shirya cikin lallausan less na musamman mai kyau da tsari. Kawayenta sun yi ado iri daya da ita, sun sanya kayan da suka dace da yanayin dinner.
Amma tun kafin ta fita, Fawaaz ya jima yana kallonta da ido mai nuni da damuwa. Har ta kammala shiryawa, bai ce komai ba, amma idonsa sun bayyana wani abu da ya kasa furta.
Da ta gama, ta ɗauki mayafinta ta sanya a kafaɗarta, sannan ta ɗauki wayarta. Dake a parlorn Gwaggo Hafsatu ne..
"Yaa Fawaaz, bari in tafi. Kawayena sun kusa isa wajen."
Fawaaz bai amsa ba nan take. Ya ci gaba da kallonta, yana nazarinta tamkar yana son fahimtar wani abu.
Bayan wasu ‘yan dakiku, sai ya ce cikin nutsuwa,
"Ba za ki shiga tare da su ba."
Nabeeha ta zaro ido cikin mamaki. "Me kake nufi? Kawayena ne fa. Kowa zai shiga tare da su."
"Ke ba kowace ba ce." Fawaaz ya amsa a takaice.
Nabeeha ta cije leɓenta. "To ai ba zan je ni kaɗai ba. Dukkan amaren suna shiga tare da abokan ango. Hakan ne tsarin dinner ɗin."