Sashe 25
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta tabbatar da cewa komai ya kankama, sannan ta koma dakinta ta zauna akan gado. Amma ko da ta rufe idanu, ba ta iya barci. Maganar Abubakar na daukar mata hankali—"Idan har muna son mu tsira, dole mu yi komai da zai hana mu faduwa!"
Ko me hakan ke nufi, ta shirya tsaf!
A daidai wannan lokacin, wayarta ta dauki kara. Ta daga da sauri, tana sa ran jin labari daga Abubakar ko daya daga cikin mutanenta. Amma lambar da ta bayyana a fuskar wayar ba ita bace.
Gaba daya jikinta ya dauki rawa lokacin da ta ga sunan da ke kan allon wayar. Baban Hammad! Wato Alhaji Amiru,
Numfashinta ya kusa tsaya wa. Me yasa yake kiranta cikin dare haka? Ko dai ya fara jin wani abu ne?!
Ta gyara murya, sannan ta danna amsa.
"Assalamu alaikum." Ta fadi da murya mai sanyin jiki.
"Wa alaikum salam," muryar Alhaji Amiru ta amsa, mai cike da kasala.
Duk da haka, ta fahimci cewa yana cikin wani hali.
"Ya dai, Alhaji? Lafiya kuwa?"
Ya dan yi shiru na wasu 'yan dakiku, sannan ya ce, "Rumanah, akwai wata tambaya da nake so in yi miki."
Zuciyarta ta buga da karfi. "Tambaya?" Ta maimaita a hankali.
"Eh," ya fadi, yana jan numfashi. "Jiya da dare, kin tambaye ni ko na samu labarin Hajiya Zaytunah da 'ya'yanta. Me yasa kika yi wannan tambaya?"
Jikinta ya dauki matsanancin zufa. Ta zaci cewa ta rufe komai a natse, amma yana iya yuwuwa ya fara shakku?
"Eh... Alhaji, ai kawai ina tambaya ne, saboda..." Ta yi shiru, tana kokarin tsara abin da zata fada.
"Saboda me?" Ya katse ta, yana kara matsa mata lamba.
"Saboda... ai ai..." Ta dan yi dariya kadan, tana kokarin boye fargabarta. "Kawai ina jin labarai ne daga wasu mutane, kuma na zata kila kai ma ka sani."
Alhaji Amiru ya sake yin shiru. Wani abu yana gaya masa cewa ba gaskiya take fada ba.
"Wane irin labari kika ji?"
Hajiya Rumanah ta ciza lebe. "Ba fa komai Alhaji. Kawai dai ."
"Kawai dai me?"
"Ina fatan suna cikin lafiya"
"Daga ina kika samu wannan bayani?"
Zuciyarta ta doka kamar ana busa ganguna a cikin kirjinta. Wannan tambaya bata yi tsammani ba!
"Eh... eh... ai dai. Fata na ce .." Ta sunkuyar da kanta, tana kokarin nemo wata amsa da zata rufe komai da ita. Amma kafin ta samu bakin magana, Alhaji Amiru ya ce,
"Kin san me, Rumanah?"
"Naam?" Ta amsa da wata irin murya mai sanyi.
"Na tabbata akwai wani SIRRI da kike boye min wani abu!"
Ta firgita matuka! Kawai sai ta mike tsaye a kan gadonta, jikinta yana rawa.
"B-boye maka wani abu? Me yasa zan boye maka wani abu, Alhaji?"
Ya yi ajiyar zuciya mai nauyi. "Wannan shine abinda zan gano!"
Ya kashe wayar batare da ya jira amsarta ba!
Hajiya Rumanah ta kasa motsi, wayar a hannunta. Numfashinta yana fita da wahala.
Haka kawai, ta san cewa abu ya fara baci. Idan har Alhaji Amiru ya shiga bincike da kansa, to komai zai iya tonuwa!
Dole ta dauki mataki kafin lokaci ya kure!
Hajiya Rumanah ta zube a kan gadonta, zuciyarta na bugawa kamar zata faso kirjinta. Gabanta ya gama faduwa, Alhaji Amiru ya fara zargin ta! Idan har ya ci gaba da bincikensa, babu shakka zai gano komai.
A firgice ta sake daukar wayarta, ta kira Hajiya Karama da gaggawa.
"Karama, muna cikin matsala!" Ta furta da rawar murya, hannunta na kerma.
"Meye kuma?" Hajiya Karama ta tambaya, jin yadda muryar Rumanah ta sauya.
"Alhaji ya fara bincike! Ya fara zargin cewa ina boye wani abu! Na tabbata idan bai samu amsa mai gamsarwa ba, zai zurfafa bincike har sai ya gano gaskiya!"
Hajiya Karama ta runtse idanu, zuciyarta na tsananta bugawa. "Wannan fa bala’i ne! Kin tabbata ba wani abu kika fada da zai sa ya shiga shakku?"
"Wallahi ban ce komai mai hadari ba! Amma dai na fahimci cewa yana da shakku! Kuma idan ba mu dauki mataki ba, to fa..."
"Ke dai ki nutsu! Ba lokacin firgici bane yanzu," Hajiya Karama ta katse ta. "Abin da ya kamata mu mayar da hankali akai shine, ya za mu dakatar da shi kafin komai ya fito fili."
"Yaya za mu yi?"
Shiru ya ratsa tsakanin su. Kowannensu na jin nauyin wannan matsala.
Hajiya Karama ta numfasa sannan ta ce, "Dole ne mu karkatar da hankalinsa. Dole mu jefa masa wani sabon tunani da zai sa ya bar binciken nan. Idan hakan bai yi aiki ba, to sai dai mu dauki matakin karshe!"
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞
*PG :21*
*AREWABOOKS VVIP:👇*
https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb
__
Idanun Alhaji Amiru suka kada yayin da ya karanta wani sashi na bayanin da aka rubuta a cikin takardar binciken,
"A cewar wanda aka kama, akwai wani babban mutum da ke daukar nauyin ayyukan su. Sun ce ana basu umarni daga wata mata mai karfin iko, wadda take amfani da wasu mutane domin kare kanta daga tonuwa."
Hannunsa ya soma kerma, zuciyarsa na bugawa da karfi. Ya sake duban hotunan da aka turo masa, duk sun kasance mutane da bai taba ganin su ba, amma abin da ya fi daukar hankalinsa shine yanda wani daga cikinsu ya fadi cewa "ba wata shakka, akwai wani da ya fi kowa sanin gaskiya, amma yana boye komai saboda tsoron tonuwa."
A wannan lokacin, numfashinsa ya sauya. Wane ne wannan babban mutum? Kuma wacece wannan matar da suke magana akai?
Zuciyarsa ta tsananta bugawa. Ko akwai wata alaka tsakanin wannan bayani da tambayoyin da Hajiya Rumanah ke masa kwanan nan?
"Ba zan yi gaggawa ba," ya furta a hankali, yana jingina da kujerarsa. "Dole ne in yi bincike na kaina."
Ya dauki wayarsa ya kira Baffa.
"Baffa, kana ina?"
"Ina nan, Alhaji."
"Ina so ka samu min cikakken bayani akan wannan binciken. Ina son in san ko akwai wata alaka tsakanin barayin nan da wasu daga cikin mutanen gida."
"Na gane, Alhaji. Zan ci gaba da bincike, amma kana bukatar yin taka tsantsan. Idan da gaske akwai wata babbar fuska da ke bayan wannan lamarin, to yana da hadari."
"Ba matsala," Alhaji Amiru ya ce da kwarin gwiwa. "Bari mu fara gano gaskiya."
__________
Bayan ta gama waya da Hajiya Karama, zuciyarta ta kasa samun natsuwa. Hankalinta ya fi karkata zuwa kan abubuwan da suka faru kwanan nan. Shin Alhaji Amiru ya riga da gano wani abu? Ko dai yana kan hanya ne?
Tana cikin wannan tunani ne wayarta ta sake daukar kara.
Ta dauka da sauri. "Waye?"
"Ni ne," Abubakar ya ce da wata murya mai cike da tsoro. "Muna cikin matsala."
Gabanta ya fadi. "Meye kuma?!"
"Sojoji sun riga sun kama wasu daga cikin mutanen mu! Kuma daya daga cikinsu ya fara magana!"
Hajiya Rumanah ta zaro ido. "Mene ya ce?!"
"Ya furta cewa suna da wata babbar fuska da ke basu umarni!"
Hajiya Rumanah ta mike tsaye, jikinta yana kerma. Idan har hakan ya ci gaba, yana nufin cewa suna dab da gane cewa ita ce ta shirya komai!
Ta rufe idonta, zuciyarta na suya. "Abubakar, dole ne mu dauki mataki!"
"Me kike so mu yi?"
Ta dauki numfashi mai zurfi. "Dole ne mu tabbatar da cewa mutumin da ya fara magana ya yi shiru har abada!"
Abubakar ya yi shiru na ‘yan dakiku, sannan ya ce da murya mai nauyi, "Kin tabbata da hakan?"
"Ba mu da zabi," ta fadi a tsawace. "Idan ba haka ba, to fa komai zai ruguje!"
A wannan lokaci, Alhaji Amiru yana tsaye a gefen tagar ofishinsa, yana kallon nesa, zuciyarsa cike da nauyin tunani. Ya fahimci cewa akwai wani abu mai girma da ke faruwa, kuma yana da alaka da mutanen da ke kusa da shi.
Sai kawai ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya dauki waya ya kira Baffa.
"Baffa, yanzu na yanke shawara. Dole ne a ci gaba da binciken nan ba tare da wata fargaba ba. Duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan lamari, dole ne ya fuskanci hukunci, ko waye ne!"
A can bayan fage kuwa, Hajiya Rumanah ta gama yanke hukuncin da zata dauka. Idan har tana so ta tsira, dole ne ta dauki matakin karshe kafin lokaci ya kure.
MAJOR GENERAL DAWUD MAFIA RESIDENCE:
Daren yana lullube da wani irin sanyi mai dadi, iska tana kaɗawa cikin nutsuwa, tana kadawa da daddawa cikin lambun gidan Major General Dawud. Wata ya bayyana a sararin sama, yana haska filin gidan da haske mai taushi.
A cikin babban falonsa mai yalwa, Major General Dawud yana zaune tare da mahaifiyarsa, Gwaggo Hafsatu. Wani kwanon kwadon rama Da tacaccen lemo na abarba yana a gaban su, mai aiki ce ta kawo musu kafin ta fice.
Gwaggo Hafsatu ta dube shi da murmushi. "Dawuda, kanason kwado kamar yadda ka saba tun kana yaro."
Major General ya girgiza kai yana dariya. "Ai kwado abinci ne na musamman, Gwaggo. Yana karfafa jiki, kuma yana kara kuzari."
Duk suka yi murmushi, suka ci gaba da shan lemo cikin nutsuwa. Sai dai a hankali hirar su ta fara sauyawa.
"Dawuda," Gwaggo Hafsatu ta furta, tana gyara zamanta. "Ni dai har yanzu zuciyata na kasa samun sukuni Yakamata mu sanar da Hajiya Zaytunah halin da ake ciki."
Major General Dawud ya gyada kai. "Hakane, Gwaggo. Ya kamata ta san cewa Muhammad shi ɗan gidan Alhaji Amiru ne. Kuma Alhaji Amiru, shi ne yayan mijinta, Alhaji Uzairu."
Gwaggo Hafsatu ta dubeshi da takaici. "Kila wannan shine dalilin da yasa aka sace su tun farko. Duk alama akwai wata babbar makarkashiya a bayan lamarin nan."
"Da alama haka ne," Major General ya ce.
Sai ya miƙa hannunsa ya dauki intercom daga saman teburin kusa da shi, ya danna lambar dakin Hajiya Zaytunah.
"Assalamu Alaikum," muryarta ta fito daga cikin intercom.
"Wa Alaikum Salam, Hajiya Zaytunah. Muna son ganin ki a nan falon Gwaggo."