← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 75

Sashe 39

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Major General Dawud ya gyada kai. "Eh, ta sani. Kuma a shirye take don ta fuskanci wannan matsalar. Amma sai an yi HANKALI."

Alhaji Uzairu ya dago kansa, yana kallon Major General Dawud kai tsaye. "Ina son ganin ta."

Shiru ya sake baci a falon. Wannan kalma daya ce kacal, amma tana ɗauke da nauyin shekaru da yawa da suka shuɗe.

Gwaggo Hafsatu ta dubi Major General Dawud, sannan ta sauke numfashi. "Zai fi kyau a yi hakan a hankali. Akwai abubuwan da za a shirya kafin hakan ta faru."

Gwaggo Zainabu ta kara da cewa, "Gaskiya ne. Muna bukatar tabbatar da cewa ba za a samu matsala ba idan suka hadu."

Alhaji Uzairu ya gyada kai a hankali, amma idanuwansa sun cika da damuwa. "Ba zan gajiya ba har sai na ganta."

Duk wanda ke wurin ya fahimci cewa wannan taro ba zai ƙare a yau ba. Wannan dai hanya ce ta bude sabon babi a rayuwar Zaytunah da iyalanta. Kuma abu guda ya tabbata—komai zai canza daga yau.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:35_

Bayan wani shiru da ya dauki kusan mintuna biyu, Alhaji Amiru ya gyara zama, yana mai duban Major General Dawud da Gwaggo Hafsatu.

"Tun da dai yanzu mun samu tabbacin cewa Hajiya Zaytunah tana nan cikin kulawarku, akwai bukatar a dauki matakin da ya dace don dinke wannan barakar shekaru da suka shude."

Alhaji Uzairu ya gyada kai da karfi. "Hakan ne! Dole ne mu hadu da ita, mu ganta da ido, mu tabbatar da halin da take ciki. Ban yarda da jin kawai ba, dole na ganta da kaina."

Gwaggo Zainabu ta dubi Alhaji Uzairu da tausayi. "Na fahimce ka, Uzairu. Ka jima kana rayuwa da tunanin cewa matarka ta guje ku, ba tare da sanin abinda ya faru ba. Amma dole ne mu bi komai a hankali. Idan da gaske asiri aka mata, to hakan na nufin akwai hatsari idan ba a bi da lamarin da hankali ba."

Major General Dawud ya jinjina kai. "Mun riga mun tsara yadda komai zai kasance. Za mu tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. Amma kafin hakan, akwai bukatar mu san cewa wane hali take ciki yanzu. Har yanzu tana fama da tasirin abin da aka yi mata."

Alhaji Amiru ya lumshe ido, yana mai nazari. "Wato yanzu dai kuna nufin har yanzu ba ta gama dawowa hayyacinta dari bisa dari ba?"

Gwaggo Hafsatu ta gyada kai a hankali. "Ba wai bata da lafiya ba, amma akwai wasu abubuwan da ke damunta. Duk da cewa ta san da mu, ta san da ‘ya’yanta, har yanzu tana da wani irin tsoro da rashin kwanciyar hankali idan aka ambaci komawa gidan mijinta."

Alhaji Uzairu ya dan sake numfashi, yana mai jin wani irin nauyi a zuciyarsa. "Ba zan matsa mata ba. Amma dole ne na ganta."

Major General Dawud ya dubi Gwaggo Hafsatu, kafin ya maida kallonsa kan duka mutanen da ke falon.

"Za a iya hakan, amma dole ne mu tabbatar da cewa ba za ta samu wata damuwa ba. Idan aka matsa mata sosai, hakan na iya kawo wani sabon tashin hankali."

Alhaji Amiru ya gyada kai. "To menene mafita?"

Gwaggo Hafsatu ta gyara zama, sannan ta dubi kowa cikin falon. "Zan fara magana da ita a hankali. Zan sanar da ita cewa kun san inda take. Idan ta nuna cewa tana da karfin zuciya don haduwa da ku, to za mu shirya haduwar cikin nutsuwa."

Alhaji Uzairu ya gyada kai, kallo a idonsa yana nuna cewa yana fatan hakan ta tabbata ba tare da wata matsala ba.

Gwaggo Zainabu kuwa ta dafe hannayenta, tana mai jin wani irin tausayin matar Dan nata. Shekaru da dama ba su hadu ba, amma yanzu da yake suna daf da haduwa, zuciyarta cike take da fargaba.

Major General Dawud ya mike tsaye a hankali, yana mai da kallo ga mutanen da ke falon. "Zan dauki alhakin tabbatar da cewa an samu mafita mai kyau. Amma sai an bi komai a hankali. Na amince da shawarwarin Gwaggo za ta fara magana da ita. Idan ta shirya, sai mu shirya haduwar da ba za ta cutar da ita ba."

Alhaji Uzairu ya numfasa a hankali. A zuciyarsa, yana so ya rungume matarsa a take. Amma dole ne ya hakura. Duk da cewa zuciyarsa na masa ruri, dole ya jira har sai lokacin da ya dace.

Kowa a falon ya fahimci cewa wannan dai ba shi ne karshen maganar ba. Amma abu guda ya tabbata akwai fata.
.....

Gwaggo Hafsatu ta dan murmusa, amma cikin zuciyarta akwai nauyin da take jin zai iya girgiza zuciyar Hajiya Zaytunah. Ta zauna a gefenta, tana mai dubanta da kulawa.

"Zaytunah, akwai wani abu da nake so muyi magana a kai."

Hajiya Zaytunah ta ajiye littafin hannunta, tana mai dubanta da kulawa. "Ina sauraronki, Gwaggo. Menene?"

Gwaggo Hafsatu ta sauke numfashi a hankali, sannan ta dubeta da ido mai dauke da hakuri da tsantsar soyayya. "Akwai mutanen da suka zo gidan nan, kuma sun zo ne domin su gan ki. Sun dad’e suna neman ki, amma sai yau Allah Ya hada ku."

Wani irin kakkarwar zuciya ya kama Hajiya Zaytunah, numfashinta ya dauke na wasu ‘yan dakiku kafin ta iya tambaya. "Su waye suka zo?"

Gwaggo Hafsatu ta dafa hannunta cikin kwantar da murya. "Alhaji Uzairu, Alhaji Amiru, Gwaggo Zainabu… duk sun zo."

Cikin sauri zuciyarta ta buga. Idanunta suka fara cikowa da hawaye, hannunta ya dan yi sanyi kamar ba jini a ciki. Ta dafa KIRJIN ta, tana jin nauyin kalmomin da ta ji. "Uzairu?" Ta maimaita cikin wata irin murya mai rauni.

Gwaggo Hafsatu ta gyada kai. "Eh, Zaytunah. Sun zo ne domin su san halin da kike ciki. Sun dauka cewa ke ce kika guje su, ba tare da sun san abin da ya faru da ke ba."

Hajiya Zaytunah ta runtse ido, hawaye suka zubo mata. Tun shekarun da suka shude, bata taɓa tunanin cewa wani lokaci za ta sake ganin su ba. Shekaru da dama na rashin sanin me ya faru da su, na jin cewa wataƙila sun manta da ita, ko kuma sun yanke hukunci a kanta ba tare da sanin gaskiya ba.

"Zaytunah," Gwaggo Hafsatu ta kira sunanta a hankali. "Mun shirya yadda za ku hadu, amma sai da amincewarki."

Hajiya Zaytunah ta goge hawayenta, zuciyarta tana harbawa da nauyin tunani. "Gwaggo... Ban san me zan ce ba. Zan iya fuskantar su? Shin zasu yarda da ni? Shin har yanzu suna ganin ni a matsayin matar da suka sani?"

Gwaggo Hafsatu ta rike hannunta, tana mai gyada kai. "Sun zo ne domin jin gaskiya. Sun zo ne domin su fahimta. Idan kina da karfin zuciya, to lokaci ya yi da za ki hadu da su."

Hajiya Zaytunah ta dauki lokaci kafin ta iya furta kalma. Ta dubi Gwaggo Hafsatu da idanu masu cike da tausayi da tsoron ciwon zuciya.

"Gwaggo, ina bukatar lokaci. Ba zan iya haduwa da su haka nan ba."

Gwaggo Hafsatu ta shafa kanta cikin kwantar da hankali. "Babu matsala, Zaytunah. Lokacin da kike bukata zai kasance a gare ki. Amma ina so ki sani babu wanda ya manta da ke. Babu wanda ke jin haushin ki. Sun zo ne domin ki, domin su sake jin dumin ki."

Hajiya Zaytunah ta rufe fuska da tafukan hannayenta, tana jin wani irin zafi a zuciyarta. Idan har hakan gaskiya ne, to watakila lokaci ya yi da za ta fuskanci abin da ta tserewa shekaru da dama.

A gefe guda, Alhaji Uzairu yana can a dakin da aka kebe shi, yana jiran amsa daga Gwaggo Hafsatu. Hankalinsa a tashe yake, zuciyarsa tana bugawa da sauri. Shin Zaytunah za ta amince su hadu? Shin har yanzu tana tunaninsa? Ko kuwa ta manta da shi?

Duk wadannan tambayoyi suna masa yawo a zuciya. Kuma babu amsar da zai iya samu sai dai har sai lokacin da ta amince su hadu.

A wancan dare, zuciyoyi da dama suna juyawa. Kuma duk da fargaba da ke akwai, akwai fata—fata na cewa wata rana, komai zai koma daidai.

.....

A cikin dare mai cike da natsuwa, Hajiya Zaytunah ta kwana tana juyi akan gadonta. Idanunta sun ki rufuwa, zuciyarta tana ta kai da kawowa. Wani bangare na zuciyarta yana so ta hadu da su Alhaji Uzairu, ta fuskance su, ta bayyana gaskiyar abin da ya faru da ita. Amma wani bangare yana cike da tsoro—tsoron abin da zai biyo baya, tsoron ko za su yarda da ita, tsoron yadda zata iya fuskantar wanda ta dauka cewa ta rasa har abada.

Washegari da safe, bayan ta gama shiryawa, ta zauna a gefen gadonta tana tunani. Gwaggo Hafsatu ta shigo, ta zauna kusa da ita tana murmushi.

"Kin yi barci?"

Hajiya Zaytunah ta girgiza kai a hankali. "Wallahi, Gwaggo, zuciyata ba ta bani damar yin barci ba. Hankalina yana a tashe."

Gwaggo Hafsatu ta dafa hannunta cikin kulawa.
Chapter 39 · 0% Book details