← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 75

Sashe 38

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:34_

Daren ya yi nisa, iska tana kadawa a hankali, tana haifar da wani irin shiru mai cike da natsuwa da zurfin tunani. Fawaaz har yanzu yana tsaye a inda ya tsaya, hannayensa a cikin aljihunsa, zuciyarsa cike da tunani. Bai san tsawon lokacin da ya tsaya a wurin ba, amma abu ɗaya yake ji azuciyarsa ta makale a daren nan, a kalmomin Nabeeha, a yadda hawaye suka cika idonta lokacin da take fadin,

"Idan kaddara ta so, Fawaaz, to wata rana, za mu sake haɗuwa."

Ya sauke ajiyar zuciya, yana jin wani abu na fizgarsa daga ciki. Tun farkon saninsa da ita, bai taɓa tsammanin cewa wata rana zai iya tsugunawa a gaban mace ba, ya furta kalmomin da suka fito daga zuciyarsa ba tare da shakku ba. Amma yau, ya yi hakan. Kuma a karon farko a rayuwarsa, yana jin tsoro, tsoron rasa ta, tsoron kada lokaci ya mayar da shi wani baƙo a wajenta.

"Fate will bring us together, Nabeeha," ya furta a hankali, yana jin kamar yana magana da iska. "I will find you again."

Nabeeha ta kwanta a gadonta, amma bacci ya gagara zuwa. Ta jujjuya, zuciyarta na bugawa da ƙarfi. Idanunta sun cika da ƙwalla, tunanin Fawaaz na yawo a kwakwalwarta.

"Why did he wait until now?" Ta tambayi kanta, amma babu amsa. Duk da cewa ta ji ƙaunar da yake mata, har yanzu akwai abubuwa da dama da ba ta fahimta ba. Ta san cewa Fawaaz mutum ne mai kamun kai, mutum ne da ba ya bayyana soyayyarsa da sauƙi. Amma hakan bai hana ta jin cewa yana ɓoye abu mai zurfi a zuciyarsa ba.

Hannunta ta daura saman KIRJIN ta, tana jin yadda bugun zuciyarta ke sauri. "Wata rana, idan lokaci da kaddara sun amince, zan san menene a zuciyarka da gaske, Fawaaz."

A washegari, garin ya waye da wani irin sanyi mai daɗi, alamar cewa hunturu na gab da ƙarewa. Shirye-shiryen tafiya sun kankama, kaya sun cika akwatuna,su na ta faman bankwana da juna.

Fawaaz bai fito daga sashensa ba, amma zuciyarsa na tare da su Nabeeha. Bai jin zai iya kallonta tana tafiya ba, domin yana tsoron kada idon su ya haɗu kuma ta ga SIRRIN da yake ƙoƙarin ɓoyewa.

Amma kafin su shiga mota, zuciyarsa ta kasa jurewa. Kamar wanda aka fizgo da ƙarfi, ya fito daga sashensa, ya tsaya daga nesa yana kallonta. Nabeeha ta ji motsinsa, sai ta juyo.

Idanunsu suka haɗu.

A nan ne Fawaaz ya fahimci abu ɗaya—ko da kuwa zata tafi yau, akwai wata rana a gaba da ke jiransu.

Wata rana da kaddara za ta sake haɗa su, domin soyayyar da take tsakaninsu, ba ta cikin irin waɗanda lokaci da nisa ke iya rushewa.

🎀🎀🎀

A cikin falon katafaren gidan Major General Dawud, an hallara da martabarsu. Alhaji Amiru, Alhaji Uzairu, Gwaggo Hafsatu, da Gwaggo Zainabu sun iso, kowa da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa.

Falon yana da yalwa, an kawata shi da kujeru masu kyau, hasken fitilu yana ba wa dakin wani irin kyan da ke kara girmamawa ga wadanda ke zaune a ciki. Kamar yadda ya kamata, an fara taron da gaisuwa da hirar duniya, domin kowa ya samu nutsuwa kafin a shigo da maganar da ta kawo su.

"Allah ya kara lafiya," cewar Alhaji Amiru, yana mai gyara zamansa. "

"Eh, Allah ya taimaka," major ya amsa da murmushi....."

Duk suka hada baki wajen cewa,

"Aameen"
Gwaggo Zainabu ta dan bubbuga cinyarta..

"Lokaci na tafiya"

Gwaggo Hafsatu ta yi murmushi. "Haka rayuwa take. Allah ya sanya zaman lafiya."

Major General Dawud yana zaune cikin shiru, yana sauraron tattaunawar tare da jan numfashi a hankali. Yana jiran su samu nutsuwa kafin ya shigo da maganar da ta kawo su.

Bayan ƴan mintuna na dariya da tuno abubuwan da suka gabata, hirar ta dan lafa. Sai Major General Dawud ya gyara zamansa, ya dube su da nutsuwa.

"Mun gayyace ku a nan ne," ya fara da murya mai kwarjini, "saboda akwai wani abu mai muhimmanci da ya kamata mu bayyana muku.

Shiru ya baci. Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru suka kalli juna, sannan suka mayar da hankalinsu kansa. Gwaggo Zainabu kuwa ta gyara zama, zuciyarta cike da tuhuma.

"Ba wani abu ba ne illa dangane da Hajiya Zaytunah da iyalanta," ya ci gaba. "Mun kira ku ne domin mu gaya muku cewa tun tsawon shekarun nan, suna a karkashin kulawar gidanmu."

Wani irin shiru ya sake baci. Alhaji Uzairu ya dan zabura, yana kallon Major General da ido waje.

"Kana nufin cewa... Zaytunah tana gidanka tsawon wannan lokaci gaba ɗaya?"

Major General Dawud ya gyada kai a hankali. "Eh."

Gwaggo Zainabu ta dan dafe KIRJIN ta, tana kallon Gwaggo Hafsatu da mamaki. "Haj Hafsatu, kin san da wannan har na tsawon wannan lokaci?"

Gwaggo Hafsatu ta sauke ajiyar zuciya. "Na sani, Zainabu. Kuma ina fata zaku fahimta bayan kunji dalili."

Alhaji Amiru ya dafe gemunsa, yana mai sake gyara zama. "Wannan lamari yana bukatar karin bayani. Me ya sa aka boye mana ita? Me ya hana ta komawa gidanta?"

Gwaggo Hafsatu ta dubi dukkansu, sannan ta gyara mayafinta. Ta bude baki a hankali.

"Asiri aka yi mata."

Wani irin shiru ya sake ratsa falon. Alhaji Uzairu ya girgiza kai, alamar bai fahimta ba.

"Asiri?" Alhaji Amiru ya maimaita, yana mai fidda numfashi.

"Eh, asiri," ta tabbatar da murya mai nauyi. "Ba wai kawai an yi mata asiri ba, a'a, makirci ne aka yi mata da tsibbu aka rabata da gidanta da iyalanta. Ba don ta guje ku ba, don kuwa tana so ta dawo, amma kurciya aka yi mata har sai da ta kasa komawa. Har sai da ta zama kamar ba ita ba."

Alhaji Uzairu ya lumshe ido, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Bai taɓa sanin cewa akwai wani abu mai muni irin wannan da ya faru da ita ba.

Gwaggo Zainabu ta gyara zama, muryarta na nuna alamar damuwa. "To yanzu ya take? Da wanne hali take ciki?"

Major General Dawud ya amsa. "Alhamdulillah, tana cikin kulawa, kuma an yi mata addu'o’i da magunguna da yawa. Amma har yanzu akwai tasirin abin da aka yi mata."

Alhaji Amiru ya sauke ajiyar zuciya. "Allah ya kiyaye gaba. Wannan abu da muka ji yana da nauyi sosai."

Alhaji Uzairu ya dafe kansa, zuciyarsa cike da damuwa. Ya dubi Gwaggo Hafsatu, yana mai furta da wata murya mai rauni,

"Duk tsawon wannan lokaci, ni da dangi muna tunanin cewa ta tafi ne don ta fice daga rayuwarmu. Ba mu taɓa sanin cewa akwai wani abu mai muni da ya hana ta komawa ba."

Gwaggo Hafsatu ta girgiza kai. "Ba don ta so ba, Uzairu. Amma ka san halin duniya. Allah ya kiyaye gaba."

Shiru ya sake baci. Kowannensu na tunani. Wannan dai ba taron banza ba ne—taro ne da zai sauya komai.

A cikin falon da shiru ya lullube, kowanne daga cikin manyan da suka hallara yana nazarin abin da ya ji. Alhaji Uzairu ya dafe kansa da hannunsa biyu, yana jin wani irin nauyi a zuciyarsa. Duk shekarun nan, yana zargin cewa Hajiya Zaytunah ce ta guje su, bai taɓa tunanin akwai wani abu da ya fi karfinta ba.

"Wato haka al’amarin yake?" ya furta a hankali, yana mai duban Gwaggo Hafsatu. "Kenan duk waɗannan shekarun, tana cikin ƙunci ne ba don ranta ba?"

Gwaggo Hafsatu ta gyada kai a hankali. "Hakika, Uzairu. An yi mata asiri mai tsananin gaske, har sai da ta rasa ikon komawa gidanka. Kuma ba wai kawai hakan ya faru ba, an yi mata kurciya—wato tunani da firgici da tsoro, har sai da ta ji ba za ta iya komawa ba. Wannan shine dalilin da yasa take nan."

Alhaji Amiru ya gyara zama, yana mai fidda numfashi. "To yanzu menene matakin gaba?"

Major General Dawud ya dube shi da idanu masu ƙarfi. "Mun kawo wannan taro ne domin mu sanar da ku gaskiya, kuma mu ɗauki matakin da ya dace. Ku sani, Hajiya Zaytunah ba ta da wata matsala da ku. Tana kaunarku, tana son yaran ta tana Kuma kula da su, amma maganin da aka yi mata ya hana ta komawa."

Alhaji Uzairu ya lumshe ido na wasu dakiku, yana mai jin wani irin zafi a zuciyarsa. A matsayin sa na miji, bai kamata a ce bai fahimci halin da matarsa take ciki ba.

Gwaggo Zainabu ta gyara mayafinta, tana mai kallon Gwaggo Hafsatu da alamar tambaya. "To yanzu, Hafsatu, kina ganin akwai mafita? Ko dai haka al’amarin zai ci gaba da kasancewa?"

Gwaggo Hafsatu ta yi shiru na dan lokaci kafin ta girgiza kai. "Mafita akwai, amma dole ne a bi HANKALI. Har yanzu ba mu san su waye suka aikata wannan mummunan aiki ba. Idan ba mu dauki mataki mai kyau ba, hakan na iya zama barazana gare ta da iyalanta."

Alhaji Amiru ya gyada kai. "Hakan gaskiya ne. To amma, Zaytunah ta san da wannan taro?"
Chapter 38 · 0% Book details