← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 75

Sashe 58

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kuwa Fawaaz, yana jin kamar kalmomin sun fi ƙarfin shi, amma dole ya furta. “Bana so ki rufe idonki yau da tunanin cewa kin taɓa ji, ko kin taɓa tsammani. Ina so ki san cewa komai da na ce… gaskiya ce.”

Ta kai hannu ta dafe KIRJIN ta. Soyayyar da take jin tana taso mata daga zuciyarta ta mamaye komai.

Ta jinjina kai a hankali, murya na rawa. “Na sani.”

Ya lumshe idanu, wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauka daga bakinsa. “Nagode, Nabeeha.”

Tayi shiru.

Ya sake furta cikin nutsuwa. “Nagode da kika ba zuciyata wuri.”

Sai da zuciyarta ta gama tsinkewa da kalmomin sa, sannan ta samu kanta da furta abu guda daya, cikin murya mai taushi.

"Kaima nagode, Ya Fawaaz."

Hannunsa ya matse wayar da ƙarfi, yana jin yadda zuciyarsa ta amsa da ɗan ƙaramin bugu.

Duk da cewa bata faɗi komai mai yawa ba, amma kalmomin ta sun ratsa zuciyarsa. Sun shige shi kamar iska mai daɗi, mai sanyaya rai.

Ya ɗan lumshe ido. “Sai da safe, Nabeeha.”

Ta sauke numfashi, sannan ta amsa da murya ƙasa. “Sai da safe.”

Bayan ya ajiye wayar, ya jingina kansa da kujerar gadonsa, idanu a lumshe.

Soyayya tana da wata hanya ta shigowa cikin zuciya ba tare da izinin mai ita ba. Kuma idan ta shigo, babu komai da zai iya korarta.

Zuciyarsa ta riga ta faɗa, kuma a yau ya tabbatar da cewa… babu gudu, babu ja da baya.

Shiru ne ya ratsa ɗakin Nabeeha bayan ta ajiye wayarta. Idanunta a lumshe, zuciyarta na tafarfasa da wani irin yanayi da ba ta taɓa fassara shi ba.

Soyayya.

Wata soyayya mai cike da natsuwa da zurfi. Wata soyayya da ba a furta ta da wasa ko burgewa ba. Wata soyayya da ta ji tana ratsa zuciyarta kamar iska mai laushi.

Ta murza gefen filo da hannunta, sannan ta zame cikin bargo a hankali, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauƙin kalmomin Fawaaz.

"Nagode da kika ba zuciyata wuri."

Ta lumshe idanu, tana jin yadda kalmomin suka fi ƙarfin zuciyarta.

Wata yar guntuwar murmushi ta bayyana a saman fuskarta.

Shi kuwa Fawaaz, bayan ya ajiye wayar, bai iya rufe ido ba.

Ya jingina kansa da jikin gadonsa, numfashinsa na fita a hankali.

Tunanin Nabeeha bai daina ratsashi ba. Duk lokacin da ya rufe ido, sai ya hango idanunta. Idanu masu launin nutsuwa. Idanu masu taushin da suka daɗe suna jan zuciyarsa ba tare da ta sani ba.

Ya dafe goshi da hannunsa, yana jin yadda zuciyarsa ta daɗe tana ɓoye wani abu da ba ya iya fassara wa da farko.

Amma yau, babu ɓoyewa.

Ya san abin da yake ji, kuma ya san cewa wannan soyayyar ba zai iya buɗe ido ya bar ta ta tafi ba.

A HANKALI, ya lumshe ido, yana jin wani abu mai daɗi yana mamaye zuciyarsa.

Idan ta amince da shi, idan ta bar shi ya shigo cikin zuciyarta, da gaske zai iya riƙe ta?

Murmushi ya kwace masa, zuciyarsa na bugu da wata nutsuwa mai daɗi.

Zai iya.

Ba wai don yana so ba kawai, sai don cewa ta riga ta zama ransa.

---

A cikin dare mai cike da shiru, Nabeeha ta kasa samun barci. Zuciyarta na cike da tunanin kalmomin Fawaaz, yadda muryarsa ta sauka cikin taushi, yadda idanunsa suka cika da gaskiya da ƙauna.

Ta lumshe ido tana jin yadda hakan ke shigarta. Duk da ba ta taɓa tunanin soyayya da Fawaaz ba a baya, yanzu tana jin kamar wani abu ne da zuciyarta ke ɗauke da shi, amma ba ta san lokacin da ya shige ta ba.

Soyayya ce ta bayyana kamar wata iska mai ɗanɗanon zuma—mai daɗi, amma mai firgitarwa.

Ta janyo bargonta, ta ƙudundune jikinta, amma hakan bai hana tunaninta yawo ba. Wata zuciya da ta daɗe da sanin Fawaaz da miskilancinsa, da natsuwarsa, da yadda ba ya cika magana da ita. Amma yau… ya furta mata cewa ita ce wuri da zuciyarsa ta zaɓa!

Ta bude idonta a hankali, zuciyarta na harbawa da wani sabon yanayi.

Za ta iya furta cewa ita ma hakan take ji? Za ta iya amincewa da zuciyarta da ke harbawa idan ta kalle shi?

Ta dafe KIRJIN ta da hannunta, tana jin yadda bugun zuciyarta ke gudu fiye da yadda ta saba.

Shin da gaske soyayya ce wannan?

***

A gefe guda, Fawaaz ma ba ya barci.

Ya kasa rufe ido, yana jin kamar zuciyarsa ta faɗa wani sabon yanayi da ba ta saba da shi ba.

Soyayya ba sabuwa ba ce a duniya, amma irin ta da yake ji… wani abu ne daban!

Ya daɗe yana gudun bayyana yadda yake ji, amma yanzu ya san ba zai iya boyewa ba. Idan har akwai soyayyar da zai ƙaunata har ƙarshen rayuwarsa, to ba wata bace illa Nabeeha.

Murmushi ya bayyana a saman fuskarsa, yana jin yadda zuciyarsa ke nutsuwa da tunaninta.

Duk duniya, da akwai mata da yawa, amma babu wata da za ta iya maye gurbin wacce ta fi so.

Duk da cewa ba ta furta komai ba, zai jira.

Ko da shekaru ne, ko da kwanaki ne, ko da sa’o’i ne, zai jira har sai zuciyarta ta yarda da shi.

***

Haka dare ya wuce, zuciyoyi biyu na ƙoƙarin fahimtar sabon yanayin da suka tsinci kansu a ciki…

Soyayya ce mai nutsuwa, soyayya ce ta gaske.

Cigaba yana tafe...
PAGE: 55

Washegari da safe, Nabeeha ta tashi da wani sabon yanayi. Duk da cewa jikinta ya sauka da gajiya, zuciyarta tana cike da wani abu da ta kasa fassara wa.

Ta zauna a gefen gado, ta rungume cinyoyinta, tana tunanin yanda zata fuskanci Fawaaz yau.

Zata iya kallonsa ido-da-ido bayan furucinsa na jiya?

Ta furzar da iska a hankali. Wata zuciyarta na gaya mata cewa ba abu ne mai sauƙi ba.

Amma ta san ba zata iya gujewa ba.

***

Fawaaz kuwa, yana tsaye a gaban madubi yana shirin fita. Kallon kansa yake, amma ba yadda ya saba ba.

Yau idan zai kalli Nabeeha, zai ga wani sabon yanayi a tare da ita? Zai iya fahimtar abin da zuciyarta ke shirin gaya masa?

Ya saki murmushi a hankali, ya dafe kugunsa.

Yau… zai sake gwada sa’arsa.

***

A tsakar gida, lokacin da Nabeeha ta fito daga ɗaki, zuciyarta ta harba lokacin da ta hango Fawaaz a bakin mota.

Ya jingina da motar, hannunsa a cikin aljihunsa, yana kallon ta da idanun da suka cika da abin da zuciyarta ke gudu daga ciki.

Soyayya.

Ta ɗan tsaya na wani ‘yan dakiku, kafin ta karasa a hankali.

Shi kuwa bai ce komai ba. Bai motsa ba. Sai dai idanunsa sun bi ta har sai da ta iso kusa da shi.

“Barka da safiya,” ta ce, muryarta na ɗauke da launi mai sanyi.

Murmushinsa ya bayyana cikin kamewa. “Barka da safiya, Nabeeha.”

Sai shiru ya ratsa tsakaninsu.

Zuciyarta na harbawa, taji kamar idan ta yi magana yanzu zata bayyana komai da zuciyarta ke ji.

Shi kuwa Fawaaz, ya lumshe ido sannan ya buɗe su, yana kallon ta kai tsaye.

A hankali ya furta, “Kin san mene ne abu mafi wahala a soyayya?”

Ta ɗan dago ido tana kallonsa, tana jiran jin amsar.

Muryarsa ta sauka a kasalance. “Rashin sanin yadda zuciyar wacce kake so take ji game da kai.”

Numfashinta ya ɗauke.

Ya ɗaga kai ya kallon ta kai tsaye, fuskar sa cike da gaskiya. “Ina fatan ni ba zan daɗe ina jiran hakan ba.”

Hankalinta ya tafi gaba ɗaya. Idanunta suka tsaya a cikin nasa, tana jin zuciyarta tana tafarfasa da wani irin yanayi da bata taɓa fuskanta ba.

Sai dai, kafin ta samu damar cewa komai, sai ya matso kusa da ita kadan, yana kallonta cikin nutsuwa.

“Ki yi min alƙawari, Nabeeha.”

Muryarta ta sarke. “Alƙawari?”

Ya gyada kai a hankali. “Idan har zuciyarki ta taba tunani akaina… ki bar ni in sani.”

Wani abu mai ƙarfi ya tsaya a ƙirjinta.

Zuciyarta na bugu da sauri, amma bata iya cewa komai ba.

Shi kuwa ya saki murmushi mai cike da kwanciyar hankali. “Ba yau ba… ba sai yanzu ba. Amma…”

Ya tsaya na ‘yan dakiku, sannan cikin muryar da ta sauka kamar iska mai taushi, ya ce,

“Zan jira.”

---

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:52_

Ta buɗe idanunta a hankali, suka haɗa ido da shi. Sai dai ta kasa cewa komai.

Shi kuwa Fawaaz, murmushinsa bai gushe ba. A hankali ya ɗaga hannunsa, ya ɗan taɓa gefen motar da yake jingina da ita, yana kallonta da zurfi.

"Ba sai kin ce komai ba, Nabeeha."

Ta ɗauke idonta, amma zuciyarta ta kasa yin shiru. Sai bugawa take kamar ana danna gangar zuciya.

Muryarsa ta sauka cikin sanyi, kamar iska mai sanyaya rai. "Amma ki sani... idan wata rana zuciyarki ta taɓa furta wani abu game da ni, ko da kuwa a cikin ruwan sanyi ne, zan ji shi."

Wani abu ya tsaya a KIRJIN ta.

Ya sake murmushi mai taushi. "Zan saurara… zan ji, har ma in amsa."
Chapter 58 · 0% Book details