Sashe 13
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bala ya numfasa. “Ina da wani shiri, amma dole ne mu kasance cikin shiri.”
Gora ya kalli Bala cikin shakku. “Kana nufin za mu ƙaddamar da hari?”
Bala ya lumshe ido, yana jin nauyin kalmomin da zai faɗa. “Ba mu da wata dama. Ko dai su kama mu su kai mu hannun wadda tasa aka kawo ku, ko kuma mu yi kokarin tsira da kanmu.”
Nabeeha ta ji jikinta yana rawa. Wannan shi ne karo na farko da take jin yadda rayuwa ke iya canzawa cikin ƙanƙanin lokaci.
Kafin su samu damar ci gaba da magana, karar harbi ta tashi!
“Sun gano mu!” Gora ya faɗi da murya mai ƙarfi.
Bala ya yi sauri ya ja Hajiya Zaytunah da Nabeeha zuwa bayan ginin don su kauce wa harbin.
‘Yan fashin sun riga sun kewaye yankin. Muryar shugabansu ta tashi cikin tsawa.
“Kun zata za ku tsere daga gare mu? Ku fito ko kuma mu cinna wuta a wurin nan!”
Bala ya matse hakora. “Dole ne mu yi wani abu yanzu ko kuma su kama mu!”
Gora ya janyo wata tsohuwar sanda da ke kusa, yana duban Bala. “Ko da zan mutu, ba zan bar su su kama su ba!”
Bala ya dubi Gora, sannan ya dube su Hajiya Zaytunah da Nabeeha. Lokaci ya yi da za su yanke hukunci, zai zama ko dai tsira ko shan wahala a hannun Hajiya Rumanah.
“Mu shirya. Komai zai iya faruwa a wannan daren.”
🎀🎀
A daidai lokacin da harbin ya lafa, Bala da Gora suka sami damar janye Hajiya Zaytunah dasu Nabeeha daga wajen. Sun fice daga ginin da suka buya, suka samu wani wuri mai tsaro inda za su huta kadan.
Duk da cewa har yanzu suna cikin fargaba, sun san cewa sun tsira daga hannun ‘yan fashin, amma har yanzu akwai tambayoyi da ke bukatar amsoshi.
Hajiya Zaytunah tana dafe da kirjinta, zuciyarta na bugawa da sauri. Bata fahimci dalilin da yasa aka kama su ba, balle kuma wanda ya kitsa wannan sharrin. Ta kalli Gora, murya na rawa.
“Don Allah, ku gaya min, waye ya sa aka kama mu? Me muka yi da har za a dauki hayar ‘yan fashi don su tsare mu kamar wasu ‘yan ta’adda?”
Gora ya lumshe ido, ya sauke ajiyar zuciya. Ya san cewa dole ne su fada gaskiya, domin babu wani dalili da zai hana hakan. Ya dube ta, fuskar nan tasa cike da alamar tausayi.
“Hajiya…” Ya furta a hankali. “Wata mata ce mai kudi ce ta biya mu don mu kama ku. Ita ce ta sa a kawo ku sansanin ‘yan fashi.”
Hajiya Zaytunah ta kara matse mayafinta, zuciyarta na tsananta bugawa. “Wacece wannan mata? Wacece take da wannan azancin da za ta iya yin haka a kaina?”
Gora ya yi shiru na dan lokaci, yana tunanin ko zai iya fadin hakan. Bala ya jefa masa harara, yana nuni da cewa lokaci ya kure, kuma bai kamata su boye komai ba.
A karshe, Gora ya numfasa, sannan ya ce da karfi,
“Sunanta Hajiya Rumanah.”
Wani irin razana ya bayyana a fuskar Hajiya Zaytunah. Ta ji kamar an jefata a wata duniya da ba ta da alaka da ita. Kafafuwanta sun yi sanyi, zuciyarta ta yi nauyi.
“Me… me kace?” Ta tambaya, kamar bata ji abin da Gora ya fada ba.
Gora ya sake numfasa, yana jin tausayin yadda fuskar Hajiya Zaytunah ta rikice.
“wasu mata ne, Amman babbar ciki Hajiya Rumanah ce ta biya mu don mu kamo ku. Itace Kuma duk ta tsara dukkanin nau'ikan azabobin da akai mu ku."
Hajiya Zaytunah ta ja da baya, hannunta yana rawa. “Hajiya Rumanah?” Ta sake maimaitawa da murya kasa-kasa.
Wata zufa ta fara keto mata a goshinta. Kamar yadda take tsaye haka ne zuciyarta ta dauki nauyi, numfashinta ya soma hauhawa. Matar yayan mijin… ‘yar uwarta ta jini… . Yar wan mahaifin ta. Da aka haife su rana daya, akai auren su rana daya, Suka Kuma auri mazaje yan gidah daya. Ita ce ta jefa su cikin wannan azaba?
“Ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba!”
Hajia Zaytunah ta fada tana girgiza Kai cikin tabbatarwa..
Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah cikin mamaki. Ita ma bata fahimta ba. “Wacece Hajiya Rumanah, Ammi?”
Hajiya Zaytunah ta ji zuciyarta kamar zata fashe. Ta runtse ido, tana jin yadda wannan gaskiya take cin ranta. Tana jin tamkar ba ainihin duniyarta take ba...Sam bata samu damar amsa tambayar Nabeeha ba.
Ta kara kallon Gora, zuciyarta cike da shakku da rashin yarda.
"Don Allah, ku fada min, me ya sa ta aikata haka? Me yasa ta dauki hayar ‘yan fashi don su kama ni? Me nayi mata?” hajia zaytunah ta tanbaye su don baki daya kwakwalwar ta da tunanin ta sun ki amincewa da Hajia rumanah ce tayi haka.
Bala ne ya amsa wannan karon. “Ba mu da cikakken bayani, amma daga abin da muka ji daga bakin shugaban ‘yan fashin, Hajiya Rumanah tana so ta wulakanta ku, a yi muku wani abu da ba zai taba mantuwa ba...a Kuma kashe ku a sanda ta umarta. "
Idanun Hajiya Zaytunah suka ciko da hawaye. “Na amince da ita… Na dauke ta tamkar uwar mu daya ubanmu daya. mijinta yayan mijina ne, Mahaifin ta yayan mahaifi nane. Rana daya aka haife mu. Tare muka tashi tun yarinta. Karewarta rana daya aka daura auren mu. Kai komai namu iri daya ne. … yaya za ta iya min haka?”
Nabeeha ta matso kusa da ita, ta rike hannunta. “Ammi…” Ta kira sunanta da murya mai rauni.
Hajiya Zaytunah ta girgiza kai, tana jin zuciyarta tana karyewa.
“Hakan ba zai yuwu ba… Rumanah ba za ta iya min haka ba…”
Amma zuciyarta ta sani, Idan har Gora da Bala sun fadi haka, to akwai gaskiya. Kuma hakan yana nufin akwai wani abu da take bukatar sani.
Bayan ‘yan dakiku, Hajiya Zaytunah ta dago kanta. Idanunta sun canza, sun yi ja. Ba hawaye take ba yanzu, Ba tsoro take ji ba, sai fushi da ƙudurin gano dalilin da yasa Hajiya Rumanah ta aikata wannan danyen aiki.
“Dole ne in san gaskiya.”
Ta juyo ta kalli Bala da Gora. “Ina son jin komai. Ina son sanin dalilin da ya sa ta aikata hakan.”
Bala ya lumshe ido, sannan ya furta: “Za ki ji komai, Hajiya. Amma dole ne mu fice daga nan da farko.”
Hajiya Zaytunah ta gyada kai, tana jin zuciyarta cike da zafi. Duk da cewa har yanzu ba ta gama fahimtar dalilin da yasa ‘yar uwarta za ta aikata hakan ba, ta san abu daya, ba za ta kyale wannan lamari haka kawai ba.
Da wannan kuduri a zuciyarta, Hajiya Zaytunah ta tsaya da ƙarfi. Babu gudu, babu ja da baya.
“lokaci yayi da AKWATI zai bude, SIRRI ka zasu bayyana. Fargaaba zata cika KIRJI, HANKALIn mutane da dama zai hauhawa.."
Haka dai suka dauki matakin barin wurin, yayin da zuciyar Hajiya Zaytunah ke tafasa da zafi, tana jira ta hadu da Hajiya Rumanah domin jin dalilin wannan mugunyar makarkashiya…
A cikin dare, motarsu na tafiya da sauri yayin da Bala ke kokarin kauce wa duk wata barazana. Gora yana zaune a baya tare da Hajiya Zaytunah da Nabeeha, amma duk zuciyarsu cike take da damuwa.
Hajiya Zaytunah ta kasa hakura. Ta sake duban Bala da Gora, zuciyarta na tafasa da fushi.
"Don Allah, ku gaya min komai. Ku daina ɓoye min gaskiya!"
Bala ya yi shiru, yana tunanin yadda zai bayyana abin da ya sani. Amma kafin ya iya magana, Gora ya riga shi.
"Hajiya, ba mu san ainihin dalilin da ya sa ta aikata hakan ba, amma shugabanmu ya ce Hajiya Rumanah ta fi son mu cutar da ku sosai kafin wai akai gashin kan ki da aka aske gareta, Ta bada umarni cewa a azabtar da ku a wulakanta ku, A tozarta ku. A Kuma raba wannan budurwar yar ta ki da mutuncin ta... Tamafi jaddada sunan yarinyar nan ta ki. Tace a tabbatar an rabata da martabarta.."
Jikin Hajiya Zaytunah ya yi sanyi. Ta jinjina kai, tana jin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyarta.
"Ta yaya za ta iya yin haka? Me nayi mata?"
Bala ya gyada kai. "Wataƙila ta gaji da kasancewarki a duniya. Wataƙila tana jin tsoron wani abu a kanki."
Nabeeha, wadda ke shiru tun tuni, ta juyo tana kallon Ammin ta. "Me hakan ke nufi, Ammi? Me yasa za ta yi hakan?"
Hajiya Zaytunah ta numfasa, hawaye na taruwa a idanunta. "Nabeeha, Hajiya Rumanah matar yayan mahaifin kuce kamar yadda na fada, sannan yayata ce. Yar wan mahaifi na ce..gidan mu daya. Mun daɗe tare da ita, mun rayu a gida daya. Ban taɓa tunanin cewa wata rana za ta nemi hallakani ba."
Nabeeha ta ji jikin ta na rawa.
"Matar yayan baba na ce?!"
"Eh," Hajiya Zaytunah ta tabbatar da hakan. "Ta kasance kamar ‘yar uwa a gare ni, amma yanzu ta juyawa rayuwata baya."
Bala ya kalli Gora, sannan ya sake fuskantar Hajiya Zaytunah.
"Hajiya, akwai abu daya da ya kamata ki sani. A lokacin da aka ba mu aikin, an ce mana cewa dole ne mu tabbata cewa babu wanda zai sake jin labarinki ko ‘yar ki da danki. Kuma mun fahimci cewa tana matukar tsoron wani abu."
Hajiya Zaytunah ta jinjina kai, zuciyarta na tambayar kanta me hakan ke nufi. Me Rumanah ke tsoro har ta kai ga neman rayuwarta?
Bala ya ci gaba da magana, yana bayyana abinda ya ji daga bakin shugaban ‘yan fashin.
"Wani abu ne da ke tsakanin ki da ita. Wani abu da ya shafi rayuwar mijinta ko yayanta ne ko danta na dai manta"
Hajiya Zaytunah ta runtse ido. Ta san cewa akwai abubuwa da yawa da suka faru a baya, amma ko daya daga cikinsu bai yi mata kama da dalilin da zai sa Hajiya Rumanah ta nemi hallakawa ba.
"Dole ne in samu amsar tambayoyi na," ta furta a hankali, amma da ƙuduri mai karfi. "Ba zan bar wannan lamari haka ba."
Duk da cewa sun tsira daga wannan haɗari, hakan bai nufin cewa sun gama da barazana ba. Har yanzu akwai Hajiya Rumanah a can, mai cike da makirci da sharrinta. Kuma har yanzu ba su san menene ainihin dalilinta na yin haka ba.