Sashe 18
Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kada ku motsa!" ya daka musu tsawa.
Bala ya yi kokarin daga bindigarsa, amma kafin ya ankara, sai Lieutenant Ibrahim ya karbe bindigar daga hannunsa. Gora kuwa ya yi kokarin tserewa ta bayan bukkar, amma kafin ya iya, Warrant Officer Suleiman ya cafke shi da karfi, ya buga shi kasa.
Fawaaz bai damu da su ba, idanunsa sun sauka kai tsaye kan Nabeeha!
Zuciyarta ta buga da karfi, tana jin kamar numfashinta zai tsaya. A karo na farko, ta ji wani irin kwanciyar hankali da ta dade tana jira.
Fawaaz ya taka kusa da ita, yana kallonta ido cikin ido. Babu wanda ya ce uffan. Ya mika mata hannu a hankali, idanunsa cike da nutsuwa.
"Kin ji tsoro?" ya tambaye ta da murya mai laushi.
Nabeeha ta girgiza kai, amma idanuwanta sun nuna cewa ta ji tsoro fiye da yadda zata iya furtawa.
Ba tare da wata shakka ba, ya kama hannunta ya rike da kyau.
"Don't be...Ssshhh is okayy" ya furta.
A gefe guda, Hajiya Zaytunah ta runtse idanuwa, tana fitar da ajiyar zuciya. Hammad kuwa ya ruga ya rungume Captain Fawaaz da karfi, yana kuka da murna.
Fawaaz ya dan matsa daga gefe, yana tabbatar da cewa komai yana tafiya daidai. Sauran sojojin sun riga sun kama Gora da Bala, sun daure hannayensu da igiya, sannan suka rufe musu baki domin su guji yin hayaniya. A gefe guda, Lieutenant Ibrahim yana duba motar da masu garkuwar suka kawo, yana tabbatar da cewa babu wani abin fashewa ko tarkon da zai iya kawo hatsari.
Nabeeha har yanzu tana tsaye a wurin, zuciyarta na harbawa da karfi. Idanunta sun cika da ruwaye, ba wai saboda tsoro ba, amma saboda yawan damuwar da ta sha. Har yanzu tana jin yadda hannun Fawaaz ke rike da nata , rikon da ya tabbatar mata cewa yanzu tana cikin aminci.
Fawaaz ya dan sunkuya yana shafa kansa, sannan ya ce, "Su daina damunki, Zamu mika su hannun hukuma, za su fuskanci hukuncin da ya dace da su."
Hammad ya dan yi shiru na wasu dakiku, sai daga baya ya jinjina kai. "Mungode, Captain brother!"
Fawaaz bai ce komai ba, sai ya mike tsaye, ya nuna musu hanyar da za su bi zuwa motocin su. Sauran sojojin sun bi sawu, suna rike da Gora da Bala da aka daure su.
A daidai lokacin da suka fara tafiya, sai Fawaaz ya lura da yadda Nabeeha ke tafiya a hankali, kamar wacce ba ta da kwari sosai. Bai yi wata-wata ba, ya dan riko hannunta, yana tafiya tare da ita.
"Kin gaji?" ya tambaya, amma yana kallonta cikin ido.
Ta dan yi murmushi kadan, sannan ta ce, "Kadan dai."
Sai da suka soma tafiya kafin Nabeeha ta iya furta wani abu.
Fawaaz bai ce komai ba. Amma a zuciyarsa, ya san cewa zai iya yin komai don ganin cewa ba ta sake fuskantar irin wannan hatsari ba har abada.
Zuciyar Fawaaz tana daka da sauri fiye da yadda ya saba ji. Hannunsa yana rike da nata, amma har yanzu ba ya jin hakan ya wadatar. Idanunsa na tafiya a fuskarta, yana nazarin ta, yana neman wani alamun ciwo ko wahala.
Idonta ya lumshe na wani lokaci, sannan ta bude su a hankali, tana jin yadda dumin hannunsa ke ratsata. A duk tsawon rayuwarta, bata taba ganin Fawaaz a irin wannan yanayin ba. Idonsa na bayyana damuwa da tsananin kauna, amma duk da haka yana kokarin boye hakan a karkashin miskilancinsa.
Ya dan tsugunna kadan gabanta, yana kallonta sosai. “Nabeeha…” ya kira sunanta da wata murya da bata saba ji ba, murya mai cike da soyayya da fargabar rasa ta.
Ta dago idonta ta kalle shi.
“Yaya Fawaaz…”
Ya dan rufe idonsa na dan lokaci, yana kokarin daidaita numfashinsa, saboda yadda sanyayyar muryarta Mai kama da ana busa sarewa ta doki kofofin kunnuwansa. sannan ya bude su da karfi, kamar wanda ya yanke shawarar cewa ba zai kara boye abin da yake ji ba.
“Ban taba jin tsoro irin na yau ba.”Ya fada a hankali, amma tare da zurfi..''Ban taba tunanin za a dauke ki ba, ban taba jin fargabar rasa wani kamar yadda na ji akan ki ba.”
Nabeeha ta kalle shi da sauri, zuciyarta na bugawa da karfi. Tana iya jin gaskiyar da ke cikin muryarsa. Bata taba jin Fawaaz yana magana da irin wannan zafin rai ba.
Ya dan sosa keyarsa yana jin yadda zuciyarsa ke tashi da wani irin yanayi da bai saba ba.
“Kin san me yasa na san daidai inda kike?” Ya tambaya, yana kallon cikin idanunta.
Ta girgiza kai a hankali.
Ya dan sauke ajiyar zuciya, sannan ya saki murmushi kadan,
“Saboda na riga na turawa zuciyarki saƙo.” ya fada cikin zuciyarsa.
Sai Kuma yace,
"Tracking device" a fili..
Idanunta suka cika da mamaki. “Saƙon dama turo fa?”ta furta a kasan zuciyar ta
"Ohh" tace a fili..
Ya gyada kai. “Eh. Na san da cewa idan har da gaske akwai soyayya a zuciyarki, to da zarar kin karanta sakon nan, sai zuciyata ta ja ni zuwa inda kike.”ya furta a kasan makoshi ..
"You're loved..."
Hawaye suka cika idon Nabeeha. Bai taɓa furta mata soyayya a fili ba, amma wannan maganar ta fi duk wata soyayya da take zato.
Fawaaz ya zare safar hannunsa a hankali, ya cusa mata acikin hannunta. Saboda yadda sanyi ke kadata. Ya zare coat din jikinsa ya dora mata akan kafadarta yana dubanta cikeda kulawa yace,
“Nabeeha…” ya furta sunanta da wata irin murya mai daɗi. “Kin ji wani rauni a jikinki? Sun miki wani abu?”
Ta girgiza kai cikin sanyin jiki. “A’a… Ni lafiya lau nake.”
Amma Fawaaz bai yarda da hakan ba. Ya matsa kusa da ita, yana dubanta sosai, yana nazarin yadda jikinta yake.
“Babu inda kike jin ciwo?” Ya sake tambaya, yana kiran sunanta cikin kwantar da murya.
Nabeeha ta dan lumshe idonta, sannan ta ce, “Kai ne kake bani ciwo, Fawaaz.” ta furta batare da ta sani ba..
Ya dan zaro ido kadan, zuciyarsa na harbawa. “Me kike nufi?”
Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta bude idanunta ta kalle shi.
"Babu.”
Fawaaz ya dan yi shiru, yana jin kalmomin nata na ratsa zuciyarsa. A koyaushe yana miskilanci, yana boye abubuwan da yake ji. Amma yau, ba zai iya musanta gaskiya ba.
Ya dan yi murmushi a hankali, sannan ya ce, “Kin san wani abu?”
Ta girgiza kai, tana jiran jin me zai fada.
Ya dan matsa kusa da ita sosai, har numfashinsa yana haduwa da nata.
“A duk tsawon lokacin da nake boye abin da ke raina, sai da aka zo kusa da dauke ki ne na fahimci cewa… Babu sauran boyewa.”
Ta lumshe ido, tana jin nauyin kalmomin nasa a zuciyarta.
“Da gaske kake,Yaa Fawaaz?” ta tambaya cikin wata murya mai taushi.
Ya murmusa, yana dubanta da wani irin so da babu wanda ya taba gani a idanunsa.
“Ba zan taba barinki ba, Nabeeha.” Ya furta da karfi. “Koda zai zame min zunubi, 🤭koda zai haifar min da matsala, koda duniya za ta juya min baya, ba zan taba barinki ba.”
A lokacin, wani hawayen farin ciki ya sulale daga idon Nabeeha. Tana kallon Fawaaz, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin shauki da bata taba ji ba.
Bata taba sanin cewa shi ma yana jin haka ba. Bata taba sanin cewa kaunar da take masa na da girman haka ba.
A hankali, ta daga hannunta, ta matse yatsunta tana jin yadda dumin tafin hannunta ke bata kwanciyar hankali.
“Nagode, Yaa Fawaaz.”
Ya dan lumshe ido, yana jin yadda wadannan kalmomi suka bugi zuciyarsa fiye da komai. Bai taba jin farin ciki irin wannan ba.
A yanzu, ba shi da shakka. Nabeeha ita ce ransa. Ita ce zuciyarsa. Ita ce rayuwarsa.kuma daga yau, ba zai taba barinta ba.
_1-KALBIM:MAMUH GEE_
_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_
_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_
_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_
_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_
_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_
_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_
_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_
*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*
*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩❤️👨🌺_
*_The Vault Of His Secrets_*
_®️NANA HAFSATU (MX)_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
*_BOOK TWO_*
_PAGE: 15_
Fawaaz ya kura wa Nabeeha ido, kamar zai tsotse ta da kallon kauna. Duk da sojojin nasa na tsaye a gefe suna jiran umarninsa, duk da akwai sauran aikinsa na tabbatar da tsaro, babu komai a duniyarsa a wannan lokacin face ita.
Zuciyarsa na bugawa da sauri, ya shafi kumatunsa hankali, yana jin yadda dumin fatarsa ke ratsa tafin hannunsa.
“You don’t know how much I was scared, Nabeeha,” ya furta da wata murya mai cike da zurfin shauki.
Idanunta suka dan kakkalo kwalla. “I knew you would come for me,” ta furta a hankali, murya na rawa.
Ya dan lumshe ido, sannan ya bude su da sauri. “Even if the whole world stood against me, I would have still come for you.”
Ta runtse ido, tana jin yadda nauyin kalmomin nasa ke shigarta, suna watsa mata dumin da ba ta taba ji ba. Ya matse hannunsa , yana jin yadda zuciyarsa ke harbawa da soyayya.
“I thought I had lost you…” ya karasa cikin wata murya mai nauyi, kamar wanda yake kokarin hadiye damuwa.
Ta girgiza kai a hankali. “No, Yaa Fawaaz. I was waiting for you.”
Ya saki ajiyar zuciya, yana jin wani irin sanyi yana lullube shi. Bai taba jin irin wannan soyayya ba. Bai taba jin cewa yana bukatar wani a rayuwarsa haka ba. Amma yau, a gabanta, yana jin komai a gare shi ita ce.
A hankali, sai ya lumshe ido na dan wani lokaci, yana kokarin danne fushin da yake ji akan mutanen da suka dauketa..
Ya bude idonsa, sai ya dan matsa gefe, ya gyara tsayuwarsa. A hankali ya waiwayo ya kalli Hajiya Zaytunah, wadda take tsaye tana kallonsa da wani irin yanayi na mamaki.