← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 75

Sashe 51

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan rana, duk da cewa ba a mayar da komai kamar da ba, an yi mataki na farko zuwa ga zaman lafiya. An share gaban baya, an bar gaba a hannu Allah. Kuma a yanzu, duk wanda ya aikata laifi, yana fuskantar sakamakonsa.

Kamar yadda kowa ya ce… akwai sauran rina a kaba.

Bayan ganawar su, zuciyar Zaytunah ta cika da ruɗani. A tsawon shekarun da suka gabata, ta koya yadda za ta rayu ba tare da Uzairu ba. Ta saba da kasancewa uwa guda ga Nabeeha da Hammad. Amma yanzu, ga shi ya dawo, yana roƙon gafara.

A daren ranar, tana zaune a ɗakin ta, idonta yana kallo amma ba ta ganin komai. Tunaninta ya tafi can baya, lokacin da take matar Uzairu, da irin son da yake mata kafin a raba su. Tana tunanin yadda rayuwarta ta canza bayan fitarta daga gidansa.

Major General Dawud ya shigo, ya zauna kusa da ita. "Zaytunah," ya kira sunanta a hankali.

Ta ɗaga kai, tana kallonsa da idanun da suka bayyana gajiyarta.

"Ba zan ce ki yafe masa ba," ya ce da natsuwa. "Ba zan ce ki manta da abin da ya faru ba. Amma ina so ki yi tunani akan kanki. Shin har abada za ki riƙe wannan zafin a zuciyarki?"

Zaytunah ta numfasa. "Ban sani ba," ta furta a hankali. "Ban san ko zan iya ba."

"To ki bari lokaci ya nuna," ya ce mata. "Amma kada ki ƙi yarda da zuciyarki. Idan har za ki samu sauƙin zuciya da yafiya, to ki yi. Idan kuma ba za ki iya ba, babu wanda zai matsa miki."

Zaytunah ta jinjina kai, tana nazari.

Bayan ganawarsa da Zaytunah, Uzairu ya koma gidansa, amma ba ya jin daɗin zama a can. Gidan ya yi shiru, ba matansa, ba ‘ya’yansa. Komai ya sauya.

Ranar da ta biyo baya, ya zauna cikin falonsa, yana kallon sararin sama daga tagar da ke gefen ɗakin. Rayuwarsa ta canza gaba ɗaya. Duk abin da ya gina ya rushe.

Bai san da wane ido zai kalli Nabeeha da Hammad ba. Bai san ko za su karɓe shi ba.

Alhaji Amiru ya zo masa ziyarar dare, suka zauna tare a babban falo.

"Ya kake ji?" Amiru ya tambaye shi.

Uzairu ya yi dariyar takaici. "Ina jin tamkar mutum da aka cire masa zuciya."

Amiru ya ɗan saki ajiyar zuciya. "Uzairu, an ce komai yana da dalili. Wataƙila haka Allah ya tsara. Amma yanzu da ka san gaskiya, mene ne matakin da za ka ɗauka?"

Uzairu ya lumshe ido. "Zan jira. Zan jira har sai lokacin da suka shirya. Ina fatan wata rana ‘ya’yana za su yarda da ni."

Amiru ya jinjina kai. "Hakan shine mafi alheri."

A bangaren Nabeeha da Hammad, su ma sun samu labarin komai. Sun san cewa mahaifinsu yana neman gafara. Sun san cewa shi kansa bai san gaskiya ba.

Sai dai, hakan ba yana nufin cewa komai zai dawo da sauƙi ba.

Hammad ne ya fara magana lokacin da suke zaune a ɗaki. "Nabeeha, ya kika ji da jin cewa mahaifinmu yana neman gafara?"

Nabeeha ta taɓe baki. "Ban san abin da zan ji ba. Abin yana da wahala. A shekaru da dama, ban taɓa tunanin zan sake ganin shi ba. Yanzu kuma gashi, yana son ya dawo cikin rayuwarmu."

Hammad ya nisa. "Ni ma haka nake ji. Amma gaskiya, ina son in san shi."

Nabeeha ta kalle shi. "Kana nufin za ka gan shi?"

Hammad ya gyada kai. "Eh. Ko da kuwa ba zan yarda da shi ba, ina son in san mahaifina."

Nabeeha ta yi shiru, tana nazari. Shin ita ma za ta iya? Shin za ta iya fuskantar mahaifinta bayan shekaru da dama?

Sai ta numfasa, sannan ta ce a hankali, "Zan yi tunani akai."

A cikin kwanakin da suka biyo baya, duk wanda abin ya shafa yana cikin tunani. Ko da yake an gano gaskiya, hakan bai canza komai ba cikin dare. Rayuwa tana buƙatar lokaci don ta daidaita.

A wata rana, Zaytunah tana cikin shiryawa a ɗakin ta, sai ta tsaya ta dubi kanta a madubi. Ta taɓa fuskarta a hankali.

Ko da yake ta sha wahala, ta tsira. Ko da yake ta rasa komai, ta sake samun sabuwar rayuwa. Kuma yanzu, tana da ‘ya’yanta, tana da mutanen da suke ƙaunarta.

Shin zata iya yafiya? Shin zata iya rungumar canji?

Ba ta da amsar wannan tambayar tukuna, amma ta san cewa lokaci ne kawai fada.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:45_

Bayan kwana biyu, Zaytunah ta kasa samun sukuni. A duk lokacin da ta rufe idanuwanta, sai tunanin Uzairu ya dawo mata. Kalaman sa sun tsaya a ranta, yadda ya durƙusa yana roƙonta gafara, yadda ya bayyana nadamarsa, yadda ya ce ko da ba za ta yafe masa ba, yana so ya ga ‘ya’yansa.

Hakanan, ta tuna da Major General Dawud da maganganunsa masu hikima. A kowanne lokaci yana ƙarfafa ta da cewa yin gafara ba yana nufin cewa dole ne a koma da baya ba, amma yana nufin a wanke zuciya daga ɗacin rai.

Ta kai hannu ta shafi fuskarta a HANKALI. Wani ɓangare na zuciyarta yana cewa ya kamata ta ƙyale shi ya ci gaba da rayuwarsa ba tare da ita ba, amma wani ɓangare kuma yana cewa ya kamata ta yi tunani akai.

Da yamma, ta tafi ɗakin Gwaggo Hafsat don samun shawara. Tana jin daɗin tuntuɓarta a irin waɗannan lokutan.

Ta same ta zaune bisa kujera tana lazimi, ta jira sai da ta gama sannan ta durƙusa a gabanta.

"Gwaggo, ina da magana."

Gwaggo Hafsat ta dubeta da kulawa. "Ina saurarenki, ‘yata."

Zaytunah ta numfasa sannan ta ce, "Alhaji Uzairu yana son gafara, yana son ganin ‘ya’yansa. Kuma na san cewa yana cikin nadama. Amma ban san ko zan iya yafewa ba."

Gwaggo Hafsat ta jinjina kai, tana nazari. "Zaytunah, na fahimci halin da kike ciki. Ba sauƙi a yafe wa wanda ya zalunce ki. Amma kuma idan kika riƙe fushin nan a zuciyarki, waye zai fi cutuwa?

Zaytunah ta yi shiru, tana nazari.

"Idan kika ba shi dama ya gan su, ba yana nufin cewa kin karɓe shi ba," Gwaggo ta ci gaba. "Kawai yana nufin cewa kina bin tafarkin da Allah ya fi so. Idan har yana cikin nadama, Allah zai hukunta shi bisa gaskiya."

Zaytunah ta lumshe idanuwanta. Tana buƙatar tunani mai zurfi.

..

A ɗaya ɓangaren kuma, Nabeeha tana zaune a ɗakinta tana nazarin abin da ke faruwa. Tun daga ranar da ta ji labarin gaskiya, take jin zuciyarta tana tafasa. Ba wai tana jin ƙiyayya ga mahaifinta ba, amma tana jin tsoron sake karɓarsa cikin rayuwarsu.

Bayan dogon tunani, ta yanke shawarar cewa dole ne ta yi magana da wani. Ta samu Fawaaz yana zaune a cikin falon gidan yana kallon wani bayani a wayarsa.

"Yaa fawaaz," ta kira shi a hankali.

Ya ɗago, yana kallonta da yanayin da bai nuna komai ba. "Eh?"

Ta matsa kusa, ta zauna akan kujerar kusa da shi. "Ina cikin ruɗani. Ban san yadda zan ji game da mahaifina ba."

Fawaaz ya ɗora wayarsa gefe, yana mai sauraron ta sosai.

"Kin san cewa ke ce za ki zaɓi yadda kike so ki ji?" Ya tambaya.

Nabeeha ta kalle shi cikin rashin fahimta. "Me kake nufi?"

"Ba dole bane ki karɓe shi cikin dare ba," Fawaaz ya amsa. "Idan kina jin fushi, hakan halal ne. Idan kuma kina jin tausayi, hakan ma halal ne. Amma duk yadda kika zaɓa, ki tabbatar cewa hakan ba zai zama nauyi a zuciyarki ba."

Nabeeha ta yi shiru tana nazari. A gaskiya, maganarsa tana da ma’ana.

"Duk yadda kike ji, dole ne ya fuskanta," ya ƙara da cewa. "Amma idan za ki gafarta, ki yi domin kanki, ba domin shi ba."

Ta numfasa, ta gyada kai. "Zan yi tunani akai."

Bayan kwanaki uku, an shirya wata ganawa. Wannan karon, Zaytunah, Nabeeha, Hammad, da Alhaji Uzairu za su hadu.

A lokacin da suka iso cikin wani falo mai cike da nutsuwa, zuciyar kowa tana bugawa da sauri.

Alhaji Uzairu ya tsaya yana kallonsu da tsantsar nadama a fuskarsa. Nabeeha da Hammad suna zaune kusa da juna, yayin da Zaytunah ke gefe.

Ya numfasa, ya durƙusa a gabansu.

"Na sani cewa ba zan iya gyara baya ba," ya ce da murya mai rauni. "Amma ina roƙon ku, ku bani dama. Nabeeha, Hammad… ku bani dama in san ku."

Hammad ya yi shiru, yana kallon mahaifinsa. "Kana nufin kana so ka zama ɓangare na rayuwarmu?"

Uzairu ya ɗaga kai. "Eh, amma ba zan matsa ba. Idan ba ku shirya ba, zan jira."

Nabeeha ta dubi mahaifiyarsu. Ta san cewa ita ce ke da yanke shawara.

Zaytunah ta numfasa, ta kalli Alhaji Uzairu da ido. "Ka riga ka yi barna da yawa," ta ce a hankali. "Ba za a iya gyara baya ba. Amma ba zan hana ka ganin ‘ya’yanka ba."

Uzairu ya ji wani nauyi ya sauka daga zuciyarsa.
Chapter 51 · 0% Book details