← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 75

Sashe 57

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fawaaz ya bita da kallo, murmushi na sauka saman fuskarsa. Ya ja numfashi, sannan ya tada motarsa, yana tafiya da zuciyarsa da ya riga ya miƙa a hannun wata ‘yar baiwa.

Idanunta suka faɗa a cikin nasa. Bata ce komai ba. Sai kawai ta juya a hankali, tana tafiya zuwa cikin gida, zuciyarta na ɗauke da wani sabon yanayi da bata san yadda zata fassara shi ba.

Nabeeha ta shiga cikin gidan a HANKALI, zuciyarta cike da nauyin tunani. Tana jin kamar ƙafafunta ba su taɓa jin irin wannan nauyin ba. Abinda Fawaaz ya faɗa mata na yawo a cikin zuciyarta, yana ratsa jijiyoyinta kamar wani irin sako da ba ta shirya karɓa ba.

A harabar gidan, ta hango Hammad yana zaune akan kujerar filawa, yana duba wayarsa. Ya ɗago yana kallonta, sannan ya hura iska a hankali. “Kin fita da dare.” Muryarsa cike da ma’anoni da dama.

Ta tsaya, ta kalle shi. Bata ce komai ba.

Hammad ya cigaba da kallonta. “dear sis?”

Ta jinjina kai kawai, sannan ta juya cikin gida. Hammad ya bita da kallo, yana nazarin yadda take tafiya cikin shiru da tunani.

---

A ɗayan ɓangaren kuwa, Fawaaz na tafiya da mota cikin natsuwa, amma zuciyarsa tana tafarfasa da wani irin yanayi. Yana tunanin yadda Nabeeha ta kalle shi da idanunta masu cike da tambayoyi. Yana jin yadda shiru ya cika tsakaninsu, shiru mai yawa fiye da kalmomi.

Ya saki numfashi a hankali, yana murmushi kaɗan. “Sai ki ji da kyau, Nabeeha,” ya furta a hankali. “Bana wasa da alkawari.”

Bai kai ko ina ba, sai ga kira daga mahaifiyarsa, Hajiya Hawwa. Ya danna answering, yana ɗaga wayar zuwa kunnensa.

“Fawaaz, kana ina?”

“Gida zan koma, Mami.”

“Akwai magana. Muna son muyi taro da kai gobe da safe.”

Fawaaz ya ɗan runtsa ido. “Taro?”

“Eh. Akwai wasu batutuwa da suka shafi rayuwarka da zamanka a nan.”

Fawaaz ya yi shiru na ƴan sakanni. “To Mami, zan zo.”

Ya kashe wayar a hankali, yana jin wani iri. Mahaifiyarsa tana da wani abu a zuciyarta, kuma yana ji a jikinsa cewa wannan magana tana da nasaba da abubuwan da ke faruwa.

Ya sauke numfashi, yana sake tuƙa motarsa cikin dare, zuciyarsa na tafiya da tunani mai nauyi.

---

Washe gari, tun da safe, Fawaaz ya shiga falon babansa, Major General Dawud. Akwai mahaifiyarsa Hajiya Hawwa a zaune, da kuma mahaifiyarsa ta ɓangaren uba, Hajiya Zaytunah.

Hajiya Hawwa ta dubi Fawaaz, tana daidaita zaman hijabinta. “Muna son magana da kai.”

Ya kalle ta cikin mutuntawa. “Ina jin ki, Mami.”

Hajiya Hawwa ta gyara zama. “Kana jin dadin zaman ka a nan gidan?”

Fawaaz ya ɗan kalli mahaifinsa, wanda ke zaune cikin natsuwa, sannan ya mayar da kallonsa kan mahaifiyarsa. “Eh.”

Hajiya Hawwa ta ɗanyi jim. “Ba ka ganin lokaci yayi da zaka ƙara tunanin abubuwa masu muhimmanci a rayuwa? Irin su aure.”

Fawaaz ya ɗan jinjina kai. “Mami…”

Ta ɗaga hannu. “Fawaaz, ni ba ƙanwarka ka bace. Ni mahaifiyarka ce. Na san irin dabi’unka. Kuma na san cewa kana da abin da kake buƙata a zuciyarka.”

Fawaaz ya numfasa a hankali. “Mami…”

“Ka shirya, za mu tattauna da kai.”

A lokacin, zuciyarsa ta fara jin wani irin nauyi. Ya san cewa batun aure ya fara matsowa kusa da shi, kuma yana da tabbacin cewa mahaifiyarsa tana da ra’ayin da ba zai dace da nasa ba.

---

A ɗayan ɓangaren kuma, Nabeeha na cikin ɗakinta, tana kallon kanta a madubi. Har yanzu bata iya daina tunanin maganganun Fawaaz ba. Kalaman sa suna yawo a cikin kunnuwanta, suna sakata jin wani abu da ba ta taɓa jin sa ba a rayuwarta.

"Zuciyata ta riga ta yanke shawarar inda take so ta tsaya. Kuma wannan wuri… shine ke, Nabeeha."

Ta lumshe ido, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. Wani yanki a cikin zuciyarta yana gaya mata cewa wannan ba soyayyar wasa ba ce. Wannan abu ne mai zurfi, mai nisa, wanda ba zata iya watsi da shi ba.

Amma fa tana da tsoro. Tsoron cewa idan ta biye wa zuciyarta, wata rana hakan zai jefa ta cikin hali da ba ta shirya ba.

Ta sake bude idonta, tana kallon kanta a madubi. Sai dai abin mamaki, ba tsoro kadai take gani a fuskar ta ba. Akwai wani abu na daban.

Wani abu da bata taɓa tsammanin zata gani ba.

'soyayya'

Soyayya tana da wata hanya ta ɓoyewa a cikin zuciya ba tare da izinin mai ita ba. Idan ta shige, sai dai ka ji tana zagaye da jininka, tana fitar da numfashinka, tana bugawa da kowace irin motsin da zuciyarka ke yi.

A haka Nabeeha ta tsinci kanta.

Tana jin numfashinta yana yin nauyi a duk sanda ta tuno yadda Fawaaz ya kalleta da idanunsa masu cike da kauna. Kalaman sa sun bi jijiyoyinta, sun sauka a inda ba za ta iya goge su ba.

"Bana iya kwana yau idan ban ji muryarki ba."

Ta runtse idonta, zuciyarta na tsalle a KIRJIN ta. Yaya zai ce haka? Yaya zata iya fahimtar cewa Fawaaz, mai kamewa da miskilanci, yana da soyayya irin haka a cikin zuciyarsa?

Ta sauke numfashi. Ita kanta, ba ta da tabbacin menene yake faruwa da ita.

Sai dai abu guda ne take da tabbaci a kai— tunanin sa ya gama mamaye zuciyarta.

---

A bangaren Fawaaz kuwa, yana zaune a cikin motarsa, ba tare da ya kunna ta ba. Hannunsa yana kan sitiyari, yana tunani mai zurfi. Bai taɓa jin irin soyayyar da yake ji yanzu ba.

"Kin taɓa ganin mutum da yake da tsananin soyayya, amma yana jin tsoron furtawa?"

Ya saki murmushi a hankali. Shi kansa bai san yaushe soyayyar Nabeeha ta fara cika ransa ba. Sai dai abu guda ne yake sani—zuciyarsa ta riga ta faɗa, kuma babu komai da zai iya janye hakan.

A hankali, ya zaro wayarsa. Ya duba chat ɗin da suka yi da ita, amma babu saƙon da ya fito daga gare ta. Hakan ya sa ya danna rubutu,

"Ina fatan kin isa gida lafiya?"

Bayan sakanni, ya ga typing a jikin screen ɗin. Zuciyarsa ta buga.

Sai dai kafin sakon ya iso, sai ya ga typing ɗin ya tsaya. Shiru ya wanzu. Bai samu komai ba.

Ya sake duba wayarsa. Babu reply.

Ya saki ajiyar zuciya. Wata murmushi ya bayyana saman fuskarsa.

"My mystery girl.... Lokacin ki ne."

---

A ɗayan ɓangaren kuwa, Nabeeha tana riƙe da wayarta a hannunta. Sakon Fawaaz ya shigo amma ta kasa rubuta komai. Numfashinta ya sauka da nauyi. Dan murmushi tayi, tana maimaita yadda yace taje gidah lafiya? Bayan gidan su daya. Kai kache kowanne unguwar sa daban...

Sai da ta ɗauki lokaci tana tunani, sannan ta matso hannu. A hankali, ta danna rubutu:

"Na isa lafiya. Kaima ka isa lafiya?"

Ta aika.

Bayan ‘yan sakanni, sai sakonsa ya dawo.

"Ina lafiya, idan har ke ma kina lafiya."

Ta ɗan runtse ido, tana jin yadda kalmomin suka shige mata kai. Wani murmushi ya bayyana saman fuskarta ba tare da ta sani ba.

Soyayya… Tana da nauyi. Tana da sanyi. Kuma tana da kwarjini da ba za a iya kaucewa ba.

Tana jin hakan a yau fiye da kullum.

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:51_

Haka zuciyar Nabeeha take ji yayin da take kwance a kan gadonta, idanu a lumshe, tana tuno kowane kalma da Fawaaz ya furta.

"Kin taɓa ganin mutum da yake da tsananin soyayya, amma yana jin tsoron furtawa?"

Kalmomin nan sun mamaye tunaninta, sun cika kunnenta. Bata iya mantawa da yadda idanunsa suka cika da gaskiya lokacin da yake magana. Bata taɓa sanin cewa zuciyarta zata buga da irin wannan nauyin soyayya ba.

Numfashinta ya yi nauyi, zuciyarta na ci gaba da bugawa.

Wayarta tayi ƙara.

Ta buɗe idanu a hankali, zuciyarta ta tsinke. Ta kai hannu ta ɗauka, sai ta hango sunansa a saman screen.

Yaa Fawaaz.

Ta tsaya, tana kallon sunan na wasu ‘yan dakiku. Me zai ce? Me yasa yake kiran ta yanzu? A yanda ta san shi, ba mutum bane mai yawan magana, balle shi da kansa ya kira da daren nan.

Tayi ajiyar zuciya, sannan ta ɗaga wayar a hankali, murya a ƙasa. “Assalamu alaikum.”

Muryarsa ta fito cikin taushi. “Wa alaikumus salam.”

Shiru ya wanzu na wasu dakiku. Daga jin numfashinta a cikin wayar, Fawaaz ya san cewa zuciyarta na bugawa da sauri. Ya san tana jin wani abu, kamar yadda shima yake ji.

A hankali, ya ɗanyi gyaran murya. “Ban so na dame ki da waya ba…”

Ta lumshe idanu, zuciyarta na sake bugawa. “Ba komai.”

Ya sauke numfashi. “Amma akwai abu guda da bana so na kwana da shi a zuciyata.”

Ta jinjina kai a hankali, duk da cewa baya ganinta. “Mene ne?”

Yayi shiru na wani lokaci. Sai daga baya ya ce, “Duk sanda na rufe idanuwa na, sai naga fuskarki.”

Hannunta ya ɗan yi sanyi, zuciyarta ta yi wata irin harbi.
Chapter 57 · 0% Book details