← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 75

Sashe 26

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tohm gani nan zuwa."

Bayan dan gajeren lokaci, ta shigo cikin falon. Kallo daya za a yi mata, a fahimci tana cikin tunani.

Ta zauna a kasan kujerar da ke kusa da Gwaggo Hafsatu, tana kallon su da nutsuwa. "Barkan ku da war haka?" Ta karasa tana gayshe su cike da girmamawa.

Major General Dawud ya gyara zamansa, yana kallonta da kulawa. "Hajiya Zaytunah, muna son mu sanar da ke wani abu mai muhimmanci."

Ta kalle su da mamaki. "Ina sauraren ku. Gwaggo"

"Mun tabbatar da cewa muhammd manemin Nabeeha yar mu. Da ne ga yayan mijinki, wato, Alhaji Amiru."

"Ehh" Ta furta, jikinta na daukar wani irin shauki. Tabbas ta tabbata Muhammad jinin hajia rumanah ne.

Numfashinta ya dauke na wasu dakiku. Ta dubi Major General da Gwaggo Hafsatu kamar mai son jin karin bayani.

"Subhan'Allah.... Dama gwaggo Ina san sanar daku nima na daga abunda su gora da bala suka sanar da mu a lokacin da aka kamamu... "

"Eh, babu shakka," Major General ya tabbatar. "Hajiya Rumanah ce mahaifiyarsa. Ita ce matar Alhaji Amiru."

Hajiya Zaytunah ta zaro ido, numfashinta na sarkewa. "Muhammad... ɗan gidan Alhaji Amiru ne. Yayan mahaifin su Nabeeha"

A hankali, wani abu ya soma fitowa daga cikin zuciyarta. Wata ƙwaƙƙwarar fahimta ce take fado mata. Ta dafa goshinta, tana kokarin daidaita numfashinta.

"Gwaggo.... e?" Ta ce da wata murya mai nauyi. "Ina da wani abu mai muhimmanci da zan fada muku."

Major General Dawud da Gwaggo Hafsatu suka kara nutsuwa, suna sauraro.

"Hajiya Rumanah," ta fara bayani, "ita 'yar uwata ce, kuma ita ce matar Alhaji Amiru.. "

Gwaggo Hafsatu ta zaro ido. "Me kike nufi?"

"Itace yar wan mahaifina. Wadda aka haife mu rana daya. Aka aurar damu ma rana daya. Saa tace Kuma kawata ta kut da kut alokacin yarinta. Zumuncin mu ya fara warewa ne alokacin da mahaifinta ya auri mahaifiyata bayan rasuwar mahaifin mu. Sannan manemin ta shine Wanda aka aura mun aure dashi amainakon Amiru sai aka samu sabani aka aura mun uzairu ita Kuma Amiru. Amman sai manya suka ce abar auren a haka tunda dama na Hadi ne bana nagani inaso ba. To yanzu Kuma kaddara tasa dan cikinta yazo yana neman ya ta... atakaice dai kar na cika ku da surutu, Ina nufin cewa ita ce ta bada umarni a dauke mu! Ita ce ta hada baki da wasu, ta turo ‘yan fashin da suka kama ni da yaran nan! Ita ce ta bada duk umarnin azabar da aka yi mana!"

Major General Dawud ya runtse idanu, zuciyarsa na tafasa. "Wannan lamari yana kara zama mai hadari."

Gwaggo Hafsatu ta numfasa. "Zaytunah, kin tabbata da wannan magana?"

"Eh, babu tantama," ta ce, hawaye na taruwa a idanunta. "Gora da Bala sun sanar da ni da bakinsu. Sun gaya min cewa ita ce ta bada duk umarni. Duk abin da aka yi mana, umarninta ne!"

A wannan lokaci, Major General Dawud ya mike tsaye. "Wannan abu ba za a kyale shi ba! Idan har haka ne, to lallai dole ne mu dauki mataki!"

Gwaggo Hafsatu ta gyara zamanta. "Dawuda, wannan magana ba a yi ta da gaggawa ba. Idan har da gaske Hajiya Rumanah ce ta shirya wannan danyen aiki, to akwai babban shiri a bayanta. Bamu san iya sharrinta ba tukunna."

Major General ya gyada kai. "Hakane, Gwaggo. Amma fa ba za mu zura ido muna kallon zalunci yana cigaba ba."

A can bangaren Hajiya Zaytunah, zuciyarta cike take da bakin ciki. Ta rufe idonta, ta furta cikin tsanani,

"Ya Allah, ka tona asirin duk wanda yake cikin wannan mummunan shiri! Allah ka nuna mana gaskiya, ka tona asirin azzalumai!"

A wannan dare, wata sabuwar makoma ta fara bayyana. Lamarin ya kara zama mai hatsari, domin yanzu an fara bankado manyan sirruka.

_____

A BANGAREN HAJIYA RUMANAH

A ranar, bayan ta samu wannan kiran da ya firgitata, Hajiya Rumanah ta kasa samun sukuni. Ta sha kwanciya tana tashi, zuciyarta tana tsananta bugawa. Kamar wadda aka tsunduma cikin matsanancin firgici, ta kirawo abokan muguntar su Hajiya Karama, da kuma kishiyar ta Hajiya Ladi.

Lokacin da suka iso gidanta, suka same ta zaune a kan kujera, tana jijjiga kanta da damuwa.

"Rumanah, lafiya kuwa?" Hajiya Karama ta tambaya, tana dubanta da kulawa.

Hajiya Rumanah ta dube su, idonta cike da tashin hankali. "Muna cikin matsala."

Hajiya Ladi ta hade girar sama da kasa. "Mene ne kuma? Ke me ya same ki haka?"

Hajiya Rumanah ta numfasa, sannan ta furta da raunin murya: "Asirina yana gab da tonuwa. Sojoji sun ceci su zaytunah da muka bada umarnin a sace. Sannan sun kama kusan dukkansu, sai guda daya da ya tsere. Kuma kun san me ya faru?"

Suka girgiza kai.

"Wannan daya da ya tsere, sai ya kira ni, ya sanar da ni cewa shirinmu ya gaza, kuma yanzu an kama abokan aikinsa."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Hajiya Karama ta furta.

Hajiya Karama ta zuba tagumi. Ta Kara da cewar "Yanzu me kike tunani? Dole ne mu san matakin da za a dauka kafin abubuwa su kara dagulewa."

Hajiya Rumanah ta dafe goshinta. "Yanzu haka Major General Dawud yana bincike. Idan har ya gano cewa ni ce nake bayan lamarin, to zan shiga matsala."

Hajiya Ladi ta numfasa, tana girgiza kai. "Ke dai kin jefa kanki cikin babbar matsala. Idan hakan ta fito fili, ba zaki iya shiryawa ba."

"Don Allah, ku taimaka min!" Hajiya Rumanah ta ce da muryar kuka. "Dole ne mu sami mafita kafin lamarin ya fi kamari! Kada ku manta harda ku acikin komai"

Hajiya Karama ta kalli Hajiya Ladi. "Wannan abu yana bukatar dabaru. Idan har muna so mu ceci Rumanah, to dole ne mu yi tunani mai zurfi."

Hajiya Ladi ta sake daidaita zaman mayafinta. "Da alama dole ne ki fara tunanin yadda za ki karyata wannan zargi tun kafin su fara bincike sosai."

Hajiya Rumanah ta dafe kirjinta, zuciyarta na dokawa da tsananin tashin hankali.

____
A wannan dare, bayan dawowa daga ofishinsa, Major General Dawud ya sake komawa sashen mahaifiyarsa. Gwaggo Hafsatu tana zaune akan kujera, tana juyawa cikin Azkar.

Ya zauna a gefenta, sannan ya furta cikin kwanciyar hankali. "Gwaggo, zamu iya samun babbar matsala nan gaba."

Ta dago ta kalle shi. "Me ya faru?"

"Duk alama Hajiya Rumanah tana kokarin boye hannunta a wannan lamari. Amma ina da tabbacin cewa akwai karin sirruka da ba mu sani ba tukuna."

Gwaggo Hafsatu ta numfasa. "Allah ya tona asirin wanda yake da laifi."

Major General Dawud ya gyada kai. "Babu shakka, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan."

A wannan dare, zuciyoyi sun kagara. Wasu suna firgita da tsoron abinda zai biyo baya, wasu kuma suna shirin tonon silili.

Shin Hajiya Rumanah za ta iya kare kanta?

Ko kuwa gaskiya za ta bayyana?

Lokaci ne kawai zai tabbatar!

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(AKWATIN SIRRIN SA)_
🧳➿💞

*PG :22*

*AREWABOOKS VVIP:👇*

https://www.arewabooks.com/book?id=670bd07e35879b101764c0eb

__

Dare ya ja, amma Nabeeha ba ta jin barci. Barci ya kauracewa manyan idanunta da suke dauke da gashin idanu Zara Zara tubarkAllah ..Iskar sanyi tana kadawa daga kofar tagar da aka bude kadan, tana motsa labulen siliki da ke lullube da gilashin. Tana kwance a gadonta, tana kallon rufin dakin, amma zuciyarta na can... a wani wuri daban.

Zuciyarta cike take da tunanin captain Fawaaz....

A zahiri, yana da kamewa. Mutum ne mai miskilanci da ba ya nuna damuwarsa ko ra’ayinsa kai tsaye. Babu wanda ke iya gane abin da ke ransa – ko da shi ne yake shirin bayyana shi.

Amma duk da haka… yana aika mata sakonnin soyayya!

Tun farko, ta yi zaton ba da gaske ba ne. Ta ce, watakila wani ne ya yi amfani da wayarsa. Ko kuma wasa ne kawai. Amma sakonni na ci gaba da zuwa, kowanne cike da kalmomin da ke bayyana yadda zuciyarsa ke a kulle.

"Nabeeha, ki yarda da zuciyata… ko da ba zan iya furtawa a baki ba."

"Idan har akwai wanda zuciyata ke muradi, to ke ce…"

"Soyayya ba wai da baki kawai ake furtawa ba. Amma idan har kina bukatar jin hakan daga bakina, to wata rana zan samu karfin gwiwa."

Ta rufe idanunta da karfi. Me yasa yake hakan? Me yasa yake aikata abin da ba zai iya bayyana wa duniya ba? Idan har yana sonta, me yasa yake yin nesa da ita? Me yasa ya kasa furtawa kai tsaye?

Zuciyarta na dauke da amsar da ba ta iya fahimta..

Ana cikin haka, sai aka turo kofar dakin da sauri.

"Nabeeha!"

Nabeeha ta zabura kadan, tana kallon kofar. "Lafiya?"

"Yi hakuri, ‘yar uwa!" Humayrah ta ce, fuskarta dauke da murmushi.

"Muhammad ne ke son yin magana da ke."

Nabeeha ta yamutsa fuska kadan. "Muhammad?"

"Eh mana, kin san ba ki da waya, sai ya kira ta tawa.. dalla malama karbi"

Nabeeha ta dan yi shiru. Ba ta da wani tunani a kai. A yanzu, zuciyarta na wajen wani daban – Fawaaz. Ta dan yi kasa da idanu tana dankarawa humyrah hararar wasa,

"Gashi nan, ki karba," Humayrah ta ce, tana mika mata wayar.

A hankali ta karba, ta kara a kunne.

"Assalamu alaikum."

A daya bangaren, muryar Muhammad ta amsa cikin nutsuwa.

"Wa alaikumus salam, Nabeeha. Ya kike?"

"Ina wuni ? Alhamdulillah!Lafiya lau."

Sai shiru ya biyo baya na wasu sakanni. Muhammad yana kokarin samun kalmomin da zai fara da su. Ita kuwa Nabeeha, hankalinta ba kan wayar yake ba – tana can tana sake tunanin Fawaaz da sakonnin da ya turo mata.

Muhammad ya numfasa. "Nabeeha... I love and miss you soo much"

Ta dan runtse idanu. Ta san abin da zai fada.

"Nabeeha, ina kaunarki."

Zuciyarta ta buga, amma ba don maganar Muhammad ba – sai don tunanin yadda Fawaaz ya kasa furtawa haka.
Chapter 26 · 0% Book details