← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 75

Sashe 53

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fawaaz ya gyara zaman rigarsa, ya ɗaura hannu kan cinyarsa, yana kallon ta da wani irin kallo mai cike da ƙarfi.

"Nabeeha, na ce ba za ki shiga da su ba. Idan kin isa wajen, ki jira a yi shigar su, sannan sai ki shiga daga baya."

Nabeeha ta yi shiru tana nazari. Ta san cewa Fawaaz mutum ne mai kishi, amma bata yi tsammanin zai hana ta shiga dinner tare da tawagar kawayenta ba.

"To me zai hana?" Ta tambaya, tana son jin dalilinsa.

Fawaaz ya numfasa a hankali, sannan ya ce,

"Saboda ba zan so wata guda daga cikin su ya shiga kusa da ke ba. Idan kin shiga da su, wani daga cikinsu zai iya kallon ki da idon da ba na gaskiya ba."

Nabeeha ta zaro ido cikin mamaki. "Yaa fawaaz! Me kake nufi? Ai waɗannan abokan angwaye ne!"

Fawaaz ya ɗaga gira. "Ban ce kowa ne zai yi hakan ba. Amma ba zan bari wani ya sami dama ya kalle ki da idon da bai dace ba."

Nabeeha ta cije baki, amma daga ƙarshe ta fahimci cewa babu fa’ida a cikin jayayya da Fawaaz. Idan ya ce abu, to ya gama yanke hukunci.

"To shikenan." Ta amsa, koda ba ta ji daɗin hakan ba.

Da suka isa wajen dinner, kawayenta suka shiga tare da abokan ango, amma ita sai da ta tsaya a ƙofar hall din tana jiran su gama shiga kafin ta shige ita kaɗai.

Yayinda ta shiga, Fawaaz na zaune a wata kujera, yana kallonta da wani irin kallo mai cike da izza da ikon mallaka.

Ta zauna kusa da shi ba tare da ta ce komai ba. Amma zuciyarta ta yi dariya. "Wannan kishi na Fawaaz dai..."

Ranar da za a kai su humyrah gidajen aurensu, an shirya siyan baki na musamman. Kamar yadda aka saba, abokan ango ne za su siya bakin kawayen amarya.

A lokacin da ake shirin wannan al’ada, Nabeeha tana zaune cikin ɗakin shiryawa, tana jiran lokacin da za a kira su su fito. Kawayenta sun hallara, suna dariya da raha, suna jiran lokacin da za a fara siyan baki.

Amma kafin su tafi, sai Fawaaz ya shigo cikin ɗakin da wani irin yanayi na girmamawa da iko. Kallo ɗaya za ka masa ka san cewa akwai wani abu da yake so ya faɗa.

Nabeeha ta kalle shi tana murmushi. "Ya fawaaz, me kake yi a nan? Ai yanzu za a fara siyan baki."

Ya kalleta da ido mai zurfi. "Ba za ki zauna a wajen siyan bakin ba."

Daga inda take zaune, ta ɗago tana kallonsa da mamaki. "Me kake nufi?"

"Ba zan bari wani ya tsaya yana ‘yan kace-nace da ke ba. Wannan abu ba ya min daɗi."

Nabeeha ta zaro ido. "Kai dai kana da matsanancin kishi! Ai hakan ya zama al’ada. Kuma dukkannin amaren suna yin hakan."

Fawaaz ya ɗan matsa kusa da ita, ya zauna gefenta, yana kallonta da ido mai cike da tsaro.

"Ke ba kowace kawar amarya ba ce. Ke mallaki na ce. You're mine and mine only"

Nabeeha ta yi shiru tana nazarin yadda zai kaya. Ta san Fawaaz ba mutum bane mai sauƙin shawara idan ya yanke hukunci.

"To amma..." Ta fara magana, amma ya katse ta.

"Ba wani ‘amma.’ Ki zauna a nan har sai an kammala komai."

Daga waje, an fara siyan bakin. An fara raha da zolaya tsakanin abokan ango da kawayen amarya. Sai dai Nabeeha, babbar amarar da ya kamata ta kasance a wajen, tana zaune cikin ɗakin shiryawa, tana murmushin takaici.

Kawayenta suna ta nemanta, amma ana cewa ta yi shiru tana dariya kawai. Duk da haka, babu wadda ta fahimci cewa Fawaaz ne ya hana ta fitowa.

Bayan an kammala komai, sai Fawaaz ya mike, . "Za mu tafi?"

Ta kalle shi, tana girgiza kai cikin murmushi. "Kai fa akwai matsala."

Ya ɗan kalleta a hankali. "Matsala kamar yaya?"

Ta girgiza kai. "Matsalar kishi. Kishi kamar na soyayyen jan nama."

Fawaaz ya ɗaga gira, yana kallonta da kallo mai ma’ana. "Kishi na wajibi ne. Idan ban miki kishi ba, wane zai miki?"

Ta cije leɓe, sannan ta ce cikin raha. "Ai haka ne. Amma ka rage mana kaɗan."

Ya girgiza kai yana dariya. "Ragewa ba zai yiwu ba."

Da haka suka fita, suka nufi motar da za ta kai su, Nabeeha na jin cewa rayuwa da Fawaaz ba za ta kasance mai sauƙi ba, amma za ta kasance cike da so da kulawa.

Fawaaz ya kalleta kafin su shiga mota. "Na gaya miki cewa zan kula da ke, ko?"

Ta gyada kai. "Eh."

"To ki sani, in har ina son ki, ba zan bari wani ya zo kusa da ke da wata manufa ba."

Nabeeha ta yi murmushi. Ta san cewa Fawaaz ba zai taɓa canzawa ba. Kuma wata zuciyarta na jin daɗin hakan.

🎀🎀🎀

Yayin da suke zaune a babban zauren gidan Major General Dawud, an hallara gaba daya, har da Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru. Zancen da Muhammad ya fada yana ci gaba da mamaye tunanin kowa. Sai dai kafin su yanke hukunci na karshe, sai Fawaaz ya durkusa cikin mutuntawa bayan sun gaisa.

Dukkan idanu suka sauka a kansa.

"Ina neman alfarmar a bani auren Nabeeha."

Kowa ya kalli juna da mamaki. Gwaggo Hafsat ta dan runtse ido kamar mai nazari. Major General Dawud ya jinjina kai, yana kallon dansa da basira.

Alhaji Uzairu da Alhaji Amiru suka kalli juna, sannan suka dubi Major General Dawud don jin ra'ayinsa.

Wannan batu ya dauki hankalin kowa, don haka dole ne su dauki lokaci kafin su yanke shawara. Amma abu daya ya bayyana wannan rana rana ce mai cike da yanke manyan shawarwari!

ADVERT👇

YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE
YERWA INCENSE AND MORE

(THE SCENTS WITH DIFFERENT ESSENCE FOR YOU AND YOUR HOME)
(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:47_

Wurin ya dauki shiru bayan Fawaaz ya bayyana bukatarsa. Kowa ya dauki lokaci yana nazarin kalamansa. Idan aka duba halinsa na miskilanci da kamun kai, ba kowa zai yi tunanin cewa zai fito fili ya nemi auren Nabeeha ba.

Major General Dawud ya kalli dansa cike da zurfin tunani. Wannan mataki da Fawaaz ya dauka ba karamin abu ba ne. A gefe guda, Gwaggo Hafsat ta kalli Zaytunah, wadda ta dafa habarta cikin nazari. Haka ma Alhaji Amiru da Alhaji Uzairu, duk suna jiran jin ra'ayin iyayen Nabeeha.

Zaytunah ta numfasa, sannan ta dubi Fawaaz. "Kana da tabbacin wannan shawarar da ka dauka?"

Fawaaz ya dago idonsa, yana kallon mahaifiyar Nabeeha da mutuntaka. "Eh, aunty. Ba zan yi magana da ku ba sai da na tabbatar da cewa zuciyata ta yanke hukunci. Idan Allah ya bani dama, zan kula da ita da dukkan mutuntawa da soyayya."

Gwaggo Hafsat ta kalli Major General Dawud. "Dawuda, yaronka ya fito da bukatarsa. Mene ne ra'ayinka?"

Major General Dawud ya gyara zamansa, yana duban danta kai tsaye. "Na san halin Fawaaz. Ba mutum bane da yake daukar mataki cikin gaggawa. Idan har ya yanke shawara, to yana nufin ya rigaya ya yi nazari mai zurfi."

Sai dai, har yanzu akwai matsala guda, yadda za a sanar da Nabeeha da kuma yanke shawarar amincewa da hakan ko akasin haka.

Zaytunah ta dubi Gwaggo Hafsat, sannan ta ce, "A ganina, ya dace a ji ra'ayin Nabeeha kafin a dauki wani mataki. Wannan abu ne da ya shafi rayuwarta gaba daya."

Gwaggo Hafsat ta jinjina kai. "Hakan ne dai. Bai kamata mu tilasta mata ba."

---

Bayan an gama wannan zama, sai aka yi shawarar cewa za a kira Nabeeha don jin ra'ayinta. Ana so a tabbatar da cewa ba za a yi mata dole ba, kuma za a yi abu ne cikin natsuwa.

A gefe guda, Muhammad da kansa yana nazarin abubuwa a zuciyarsa. Shin zai iya jurewa ganin Nabeeha da wani? Duk da cewa ya yanke shawarar hakura da ita, amma zuciyarsa ba ta da sauki.

A gefe guda kuma, Fawaaz yana da natsuwa, amma yana jiran jin amsar Nabeeha. Shi kansa ya san cewa ba lallai ta amince ba, amma yana fatan Allah ya zaba masa mafi alheri.

Zaytunah da kanta ta tafi sashen Nabeeha don sanar da ita wannan batu.

"Nabeeha, akwai maganar da muke bukatar jin ra'ayinki a kanta."

Nabeeha ta dago da mamaki. "Mene ne Ammi?"

Zaytunah ta dan yi shiru na wasu sakanni, sannan ta dubi ‘yarta ido da ido. "Fawaaz ya fito da bukatar auranki."

Nabeeha ta zaro ido! "Ni? Da Fawaaz?"

Numfashinta ya dan tsaya na wani lokaci. Hankalinta ya tashi. Wannan abu ne da ba ta yi tsammani ba...

Nabeeha ta zaro ido tana kallon Zaytunah tamkar ba ta jin daidai. Kamar dai bata fahimci abin da Ammi ta faɗa ba. "Ni? Da Fawaaz?" Ta maimaita tamkar tana son tabbatarwa idan da gaske take.

Zaytunah ta numfasa, sannan ta gyara zama. "Eh, Fawaaz da kansa ya zo ya nemi auranki. Amma muna son jin ra'ayinki kafin a dauki mataki."
Chapter 53 · 0% Book details