← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 75

Sashe 3

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar dai a dole likitan ya sallame su. Don gwaggo Hafsatu ta matsa kan ba zata kwana a asibitin nan ba. HANKALIn ta baya jikin ta. Nutsuwar ta da kwanciyar hankalin ta baki daya ya tattara ne awajen su hajia zaytunahh na rashin sanin takamaimai halin da suke ciki..

Hankalin Major General ya ƙara tashi fiye da yadda zai iya bayyanawa. Bai taɓa jin zuciyarsa ta yi nauyi haka ba. Hannunsa ya fara gumi, ya sake duba wayarsa. Bai san sanda ya miƙe tsaye da sauri ba. Ganin lokaci ya sake zartawa.. Amman ba wani labari daga dukkanin wadanda ya saka aikin bincike...

Gwaggo Hafsatu ta dubi dan nata, idanuwanta cike da tsoro.

"Dawuda, ka ce wani abu! Ka ce ba wata matsala!"

Hajiya Hauwa Maijidda ta dan matsa kusa da shi.

"Kayi shiru! Me ke faruwa?"

Muryarsa ta ɗauka da ƙarfi. Bai masan ya furta,

"Wannan abu ba daidai bane! Ba abu ne na hatsari ba. Ba daidai bane gaba ɗaya!"

hajiya Hauwa Maijidda ta ɗaga wayarta da sauri, tana sake ƙoƙarin kiran Hajiya Zaytunah, Nabeeha, da Hammad. Amma duk wayoyin a kashe suke.

"Subhanallah!" Ta furta, jikinta na rawa.

Major General Dawud ya haɗa fuska, ya danna wata lamba a wayarsa. Cikin daƙiƙa biyu kacal aka ɗauka.

"Captain!" Ya kira da kakkausar murya.

"Na’am, ranka ya daɗe!"

"A gaggauce ka bi sawun brid. Gen. Mukhtar, Ka temaka musu ku tsananta binciken nan da gaggawa"

"Ina nan a kan hakan, ranka ya daɗe."

Ya kashe wayar batare da wata magana ba.

Gwaggo Hafsatu tasake fashewa da kuka. Wannan karon muryarta har wani rawa takeyi,

"Dawuda, ka taimake ni! Kar dai wani abu ya same su!"

Zuciyar Major General tana bugawa, amma ya daure kansa. Ya kalli mahaifiyar sa, gwaggo Hafsatu cikin muryar ban tausayi da rarrashi yace,

"Inshaa Allahu zasu kubuta, Za'a ceto su gwaggo, Zaa gansu. Ki bar zubar da hawayen ki dan Allah.."

Major General ya rufe idanuwansa na wasu dakiku, yana shakar iska mai nauyi.

Nan take ya ɗauki waya, ya kira Control Room na sojoji.

"Ina so a fara bincike! A duba ko an samu wani rahoto na motar da ta bar gida tun dazun!"

A ɗaya ɓangaren, wani yaron sa ya kira shi.

"Tracking ɗin motar yana nuna an bar hanya mai tsaro. Motar ta shiga cikin wani yanki da ba a saba wucewa da ita ba!"

Kamar an caka wa Major General ƙwalla da wuka, haka zuciyarsa ta ji.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!"

Ya dafe goshinsa, hannunsa na rawa.

Gwaggo Hafsatu ta kama rigarsa.

"Ka ce ba a sace su ba, Dawuda! Kar dai yan fashi ne!"

Zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Bai iya cewa komai ba. Amma zuciyarsa na jin 'An sace su!'

Ya dan kakaro murmushin kwantar da gwaggon HANKALI yace,

"No akan na'urar aiki ne ta katse. Inshaa Allah komai zai daidaita Gwaggo..ki kwantar da HANKALIn ki"

🎀🎀🎀

Duk da an jima ana tafiya, babu wata gajiyar da Fawaaz ke ji. HANKALIn sa gaba ɗaya yana kan abu ɗaya wato Nabeehan sa...

Tunda suka fara tafiya daga base, tunaninsa ya kasa barin fuskar Nabeeha, Yanayin tsarin halittar jikin ta, sanyayyar muryarta, Kai komai nata ma, Yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa da soyayyarta, yana jin yadda zuciyarsa ke harbawa da son ya ganta a zahiri, ya fuskance ta, ya faɗa mata abin da ke ransa.

Ya gama yanke hukunci, yau ba zai kwanta ba tare da ya fuskance ta ba. Duk da miskilancinsa da kamun kansa, ya yanke shawarar faɗa mata gaskiyar zuciyarsa. 😂

Sai ga direban nasa yana sanar da shi,

"Yallaɓai, yanzu zamu hau babban titi har cikin gari"

Yana shirin bayar da umarni, sai wayarsa ta fara ringing. Mahaifinsa ne. Wato, Major General Dawud.

Nan take bugun zuciyarsa ya sauya. Ya duba fuskar wayar, yana jin kamar numfashinsa na ɗaukewa, Mahaifinsa ba mutum ne mai yawan kiran sa ba, sai dai idan da wani lamari mai muhimmanci.

Ya ɗaga wayar da sauri.

"Morning sir! Barka da war haka Baba!"

Muryar mahaifinsa ta fito da ƙarfi da girmamawa, amma kuma da wani yanayi na tashin hankali da bai saba jin sa da shi ba.

"Fawaaz! Ba lokaci, muna da matsala! An sace su Hajiya Zaytunah, Nabeeha da Hammad!"

Zuciyarsa ta tsaya cak. Duk duniya tamkar ta tsaya cak a kunnensa.

"M... menene?"

"An sace su akan hanyar zuwa asibiti! Gwaggo an kwantar da ita as of then , su kuma an sace su! Duk wayoyinsu a kashe! Babu wanda ya san inda suke!"

A wani lokaci dabam, Fawaaz zai iya sarrafa kansa, amma yanzu zuciyarsa ta gama harbawa da tashin hankali! Ya ji wani sanyi yana ratsashi daga ƙasa har sama. Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi.

"Nabeeha..." ya furta a hankali, yana jin yadda wani abu mai tsananin zafi ke ciwo a KIRJIN sa.

Tunanin cewa Nabeeha tana hannun wasu mutane ya kusa gigita shi. Ita da ke ransa da zuciyarsa, ita da yake shirin faɗa wa gaskiyar zuciyarsa, ita ce aka sace?

"Kana jina kuwa, Fawaaz?!" Mahaifinsa ya ɗaka masa tsawa.

Ya rufe idanunsa, yana kokarin daidaita numfashinsa. Ya sanya hannunsa yana dafe kansa.

"Sorry sir. Yes sir! I'm all ears..Ina sauraron ka... gashinan zan dawo gidan yanzu! Babu wanda zai kwana ba tare da an san inda suke ba inshaa Allah !"

Major General Dawud ya sauke ajiyar zuciya.

"Godiya nake, Fawaaz. Mun baza jami’an bincike, amma kana da ilimi da kwarewa wajen gano abubuwa. Sauran jami’ai na kan aikinsu, amma ina bukatar ka waiwayo gidah yanzu don taimakawa wajen gano su."

Fawaaz ya sunkuyar da kansa, yana jin yadda zuciyarsa ke ƙuna da damuwa.

"Inshaa Allah baba...." Major general ya katse wayar..

Cikin muryar sa mai cike da damuwa yace da direban,

"Kara gudu ! Please... I beg you!"

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
              _🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:4_

Gaba daya tunda Captain Fawaaz Dawud ya karɓi kiran mahaifinsa, Major General Dawud, hankalinsa ya yi matuƙar tashi, amma a zahiri ba a iya karanta komai a fuskarsa. Yana daga cikin mota tare da direbansa lokacin da kiran ya shigo. Duk da cewa tunaninsa yana kan Nabeeh.. masoyiyar da bai furtawa kalaman yana kaunarta ba a zahiri. Sai gashi labari mafi muni ya riskesa alokacin daya gama tsarawa zuciyarsa da labbansa yanayin yarda zai furta mata komai na kaunar da yake mata. Mummunan labarin an sace su ya doki kofofin kunnuwan sa..

“An sace su Hajiya Zaytunah akan hanyar su ta zuwa asibiti duba gwaggo,” Ya tuno mahaifinsa ya sanar da shi da kakkausar murya...

Fawaaz ya ɗauki sakanni kaɗan yana nazari, ba tare da wata hayaniya ko wata alama ta firgici ba.

Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Gabansa na tsananta bugawa, Ahankali ya zura hannu ya zare katin kuɗi mai nauyi daga aljihunsa, ya miƙawa direban nasa, sannan ya ce,

“gashi ba yawa, ka tafi gida ka huta, Na gode.”

Direban ya ji mamakin yadda Fawaaz bai nuna wata damuwa ko firgici ba. Lalle wannan shi ne Captain Fawaaz Dawud Mafia. Soja mai cikakken ikon sarrafa kansa... Direban ya sauka ahankali yana yana sake yiwa captain fawaaz godia. Idanuwansa sun cika da ruwan hawayen kyautar kudi masu yawa da fawaaz din ya masa,

"Nagode ranka ya dade. Allah ya saka maka da alkhairi. Ya yi riko da hannuwan ka. Allah kuma ya shiga cikin lamuran ku Kai da zuriyar ka. Ya kawo karshen dukkanin matsaloli"

"Aameen, Ni ne da godiya" captain fawaaz, Bai jira komai ba, ya shiga cikin motarsa ya ja da gudun wuce kima, har sai da tayoyin suka yi ƙara akan titin. Hannunsa yana kan sitiyari, idonsa yana kan hanyar da ke gabansa, amma zuciyarsa tana can waje guda kawai.,

Nabeeha.

Sai yanzu ya fahimci cewa damuwar da yake ciki ba saboda kowane mutum ba ne sai ita. Duk da kasancewarsa mutum mai natsuwa da miskilanci, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi saboda ita.

Amma ba lokacin tunani ba ne. Yanzu aiki ya rage masa.

Yana tafe yana amfani da na’urorin binciken sojoji na zamani, yana tuntuɓar abokan aikinsa ta SIRRI. A matsayin soja, ya san hanyoyin gano mafakar masu aikata laifi, kuma ya san yadda ake bibiyar mutum ta hanyoyin zamani.

Yana tuki da gudu fiye da kima, yana kauce wa motocin da ke kan titin, yana kwana cikin gaggawa. Da wani irin zafi yake tuƙi, tamkar idan har ba zai isa ba nan take, zai iya karya ƙa'idojin duniya gaba ɗaya don kawai ya isa.

Wani lokaci ne da bai taba jin kansa a haka ba cikin tsananin gaggawa da tsoro mai yawa.

"Waye ya sace su? Me suke nufi? Me yasa?!"

A yanzu, babu wani abu a duniyarsa da ya fi muhimmanci fiye da gano inda Nabeeha take.

A zuciyarsa, yana jin wani sabon irin fushi da ba kasafai yake jin sa ba. Idan har wani ne ya kuskura ya cutar da ita... to wannan zai kasance babban kuskuren rayuwarsa.

Fawaaz ya cigaba da tuƙi da gudun tsiya, tamkar zai tarwatse da zuciya. Bai damu da harbin hanyoyi ko ƙa'idojin hanya ba, burinsa guda ɗaya ne isa gida cikin gaggawa!

A lokacin da ya kusa isa, ya hango daya daga cikin masu gadin gidan yana buɗe babbar ƙofar shiga. Wani saurin fakin ya yi, motar na kusan sulalewa ta tsaya cak! Bai ko kashe injin ba, ya fice da matuƙar sauri.

Da sauri da gudu gudu yana shigewa cikin gida da hanzari. Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.

Yana shiga cikin babban falo, ya hango mahaifinsa, Major General Dawud, tsaye cikin damuwa, yana waya da wasu mutane. A gefe kuma Gwaggo Hafsatu zaune, hannayenta a dage a sama, kamar tana addu’a. Damuwa ta bayyana a fuskarta,

"Baba! Sir! " Fawaaz ya furta, zuciyarsa na harbawa.

Major General Dawud ya waiwaya da sauri, idanunsa sun nuna yawan tunani da damuwa.
Chapter 3 · 0% Book details