← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 75

Sashe 50

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_

_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:44_

Hajiya Rumanah, Hajiya Ladi, da Hajiya Karama suna durƙushe a ƙasa, kuka ya cika falon. Sun rasa yadda za su yi. Fuskokin su sun cika da hawaye, amma babu wanda ya nuna tausayi a gare su.

Muhammad ya dubi mahaifiyarsa da takaici. A zuciyarsa yana ƙoƙarin fahimtar yadda zata iya shiga irin wannan mugun nufi, amma babu amsar da ke da daɗi. Mahaifiyarsa ce, amma ta aikata abin da ba zai iya gafartawa ba.

Alhaji Amiru ya girgiza kai cikin takaici. "Ku fice daga gidana kafin na ƙara da hukunci mafi muni!"

Hajiya Karama da Hajiya Ladi sun zabura suna rarrafe suna roƙon afuwa.

"Don Allah, Uzairu! Don girman Allah, ka yi mana rai!"

"Wallahi ba mu da laifi! Hajiya Rumanah ce ta ja mu!"

Ita kuwa Rumanah ta zabura cikin zafin rai.

"Ku daina mini sharri! Ai ku kuka fara! Ku kuka ce za a hana Zaytunah dawowa! Ni fa ba ruwana!"

A take suka hau musayar zargi a tsakaninsu. Kowacce tana ƙoƙarin wanke kanta, amma babu wanda ya yarda. Sun ruguza rayuwar wasu, yau kuma rayuwarsu ce take rushewa.

"Ya Isa!" Alhaji Uzairu ya daka tsawa. "Ba zan saurari wata ƙarya ba! Na ce ku fice daga gidana!"

Babu yadda suka iya. Da kyar suka tattara tarkacensu suna kuka, suka bar gidan kamar waɗanda aka yankewa hukuncin kisa.
....

Muhammad ya tsaya a gefe yana kallon mahaifiyarsa tana barin gidan da tarin nadama. Bai san abin da zai ji ba. Bai san ko zai iya gafarta mata ba. Yana da zafi a zuciyarsa, amma ya san cewa dole ne ya cigaba da rayuwarsa.

"Yaya zaka yi da ita?" Alhaji Amiru ya tambaye shi.

Muhammad ya girgiza kai. "Ba zan iya cewa komai ba. Ita ta jefa kanta cikin wannan bala’in. Ba zan iya yanke hukunci akanta ba, amma gaskiya ta fito. Dole ne ta fuskanci sakamakon muguntarta."

Sai ya juya ya bar falon, zuciyarsa cike da tunani.

..

Bayan fitarsu, falon ya dauki shiru. Alhaji Uzairu ya zauna, yana dafe kansa da tafukan hannunsa. A yanzu, komai ya bayyana. An tona asirin mugunta, amma har yanzu yana jin nauyin zuciya.

"Shekaru da dama..." ya furta a hankali. "Shekaru da dama ina tunanin Zaytunah ce ta rabu da ni, ashe ni aka yaudara?"

Gwaggo Zainabu ta girgiza kai cikin tausayi. "Hakika kun shiga jarabawa, Uzairu. Amma yanzu dai komai ya fito fili. Kuma ina fata ka gane gaskiya."

"Gaskiya ta fito," ya ce cikin wata irin murya mai cike da rauni. "Amma me zan yi da rayuwata yanzu?"

Sai ya lumshe ido, zuciyarsa cike da nadama.

..

A yanzu, Alhaji Uzairu ya san cewa dole ne ya nemi Zaytunah. Amma ina za a ganta? Shin za ta yafe masa bayan duk abin da ya faru? Ya san cewa komai ba zai dawo da sauƙi ba.

Alhaji Amiru ya dube shi, ya ce: "Abin da ya rage gare ka shi ne ka nemi ‘ya’yanka. Ka nemi Zaytunah, ka nemi gafara."

Uzairu ya ɗaga kai ya kalle shi, yana jin kamar duniya ta sauya. Bai san da wane ido zai kalli ‘ya’yansa ba. Duk da haka, ya san dole ne ya nemi su.

A can nesa, wata rana, wata sabuwar rayuwa za ta fara. Amma yanzu, ya rage ga Uzairu da yadda zai fuskanci abin da ya shuka...

Muhammad ya girgiza kai lokacin daya Kalli wajen ta faifon bidiyon da yake gani yaja dogon tsaki yana mai sake furzar da iska mai nauyi daga bakinsa.. ya cigaba da kalla.. yana saurara,

Kwana biyu bayan abin da ya faru, Alhaji Uzairu ya kasa samun sukuni. Yana jin tamkar rayuwarsa ta faɗa cikin duhu. Zaytunah ce macen da ya fi so, amma saboda sharrin matansa ya zarge ta, ya bar ta..

Bayan duk wannan shekarun, yanzu ya san gaskiya. Amma ya rasa yadda zai fara. Ya zauna a cikin falonsa, yana duban hoton da ya rage masa daga aurensu—hoton da ke nuna Zaytunah tana murmushi da Nabeeha ƙarama a bayanta.

Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. "Dole ne in nemi Zaytunah," ya furta a fili. "Ko da kuwa ba za ta yafe mini ba, dole ne in roƙe ta gafara."

Da farko, Alhaji Uzairu ya ziyarci Alhaji Amiru. Sun zauna cikin falonsa mai girma, Uzairu yana fuskantar ɗan’uwansa da tsantsar nadama a idanunsa.

"Na tafka kuskure, Yaya Amiru," ya furta da wata irin murya mai rauni. "Na tafka babban kuskure da ba zan iya gafarta wa kaina ba. Amma dole ne in nemi Zaytunah. Ko da kuwa ba za ta yafe mini ba, zan roƙe ta gafara."

Alhaji Amiru ya jinjina kai. "Hakika kayi babban kuskure, Uzairu. Amma ba kai kaɗai ba, ni ma ina da laifi. Lokacin da Zaytunah ta ɓace, na yi tunanin cewa kawai ta tafi ne, ba tare da neman zurfafa bincike ba. Bai kamata na bar lamarin haka ba."

"Kana tunanin za ta karɓe ni?" Uzairu ya tambaya, idonsa cike da damuwa.

"Ba zan iya cewa komai ba," Amiru ya amsa. "Amma abu ɗaya da na sani shi ne, dole ka nemi ta. Idan ka samu gafararta, hakan zai fi maka kwanciyar hankali fiye da komai."

GANAWA DA MAJOR GENERAL DAWUD

Bayan tattaunawa da Alhaji Amiru, Uzairu ya yanke shawarar cewa dole ne ya je wajen Major General Dawud, don kuwa shi ne mutumin da zai iya taimaka masa ya san inda Zaytunah take.

Ya isa gidan Major General Dawud cikin matsanancin damuwa. Bayan an sanar da shi zuwan Alhaji Uzairu, Major General Dawud ya amince da ganinsa.

A cikin babban falon da ya kasance mai cike da ƙamshi da ɗaukar hankali, Uzairu ya zauna yana jiran fitowar Major General Dawud. Cikin ‘yan mintuna, Dawud ya fito sanye da farin riga da wando na shan iska, yana daure fuska kamar yadda ya saba.

"Ina wuni, Major General," Uzairu ya furta cikin ladabi.

"Lafiya lau," Dawud ya amsa, yana kallonsa da idanu masu cike da tambaya. "Meye ya kawo ka?"

Uzairu ya yi ajiyar zuciya, ya sunkuyar da kansa. "Na zo ne domin neman gafara. Ba daga gare ka ba, amma daga gare ta. Dole ne in ganta, in roƙe ta gafara. Ko da ba za ta yafe mini ba, in nemi ‘ya’yana."

Major General Dawud bai ce komai ba na wani lokaci. Sai daga baya ya numfasa, ya gyara zamansa.

"Zaytunah ta shafe shekaru da dama cikin damuwa. Baka san irin wahalar da ta sha ba. Kawai kana so ka je ka roƙe ta gafara, sai komai ya wuce?"

Uzairu ya girgiza kai. "Ba haka nake nufi ba. Ina jin nauyin abin da ya faru. Ina son in nemi su, in roƙe su gafara, kuma in mayar da ‘ya’yana gare ni."

Major General Dawud ya yi shiru, yana nazari. Bayan wasu mintuna, ya ɗaga kai ya ce:

"Idan har da gaske kake, to dole ka jira. Na fahimci cewa kai ma baka san cewa ana cutar da Zaytunah ba. Amma hakan ba yana nufin cewa komai zai dawo kamar da ba. Zan fara tattaunawa da ita. Idan ta amince da ganinka, sai in sanar da kai."

Uzairu ya ɗaga kai, zuciyarsa tana cike da begen samun dama. "Nagode. Ko da kuwa ba za ta yafe mini ba, zan gode idan na ganta."

A cikin kwanakin da suka biyo baya, Major General Dawud ya tattauna da Hajiya Zaytunah game da bukatar Alhaji Uzairu na ganinta. A farko, ta yi shiru na dogon lokaci, tana nazarin abinda ya dace.

"Bayan shekaru da dama, yanzu ne yake tunanin ganina?" Ta furta a hankali.

Dawud ya kalle ta da kulawa. "Na san cewa ba abu ne mai sauƙi ba. Amma ina ganin yana cikin nadama. Yana son ‘ya’yansa, kuma yana son ya nemi gafararki."

Zaytunah ta jinjina kai, zuciyarta cike da tunani.

Bayan dogon tunani, ta ɗaga kai. "To, zan gan shi. Amma ba don in karɓe shi ba. Zan ji abin da zai ce."

Ranar da aka shirya ganawar, Alhaji Uzairu ya kasance cikin rawar jiki. Yana fargabar yadda za a karɓe shi, amma ya san cewa dole ne ya fuskanci sakamakon abin da ya aikata.

A lokacin da ya shiga falon da aka tanada don ganawar, zuciyarsa ta kusan bugawa da sauri. Ganin Zaytunah a zaune a gefen kujera, tana kallonsa da idanu masu cike da kamewa, ya ji tamkar an caka masa wuka a zuciya.

Ya durƙusa a gabanta, idonsa cike da hawaye.

"Zaytunah, na tafka babban kuskure. Na tafka laifi da ba zan iya gafarta wa kaina ba. Na yarda da ƙarya, na bar ku cikin wahala, Banyi kokari ba wajen fahimtar gaskiya. Na zo gare ki ba don in roƙi ki ki dawo ba, amma don in roƙi ki gafarta mini. Domin zuciyata ba za ta samu sukuni ba idan baki yafe mini ba."

Zaytunah ta dubi shi, idonta cike da nauyin tunani. Tana iya ganin nadama a fuskarsa. Tana iya jin ƙaryar da aka yi masa, amma hakan ba yana nufin cewa komai zai dawo da sauƙi ba.

Ta sauke ajiyar zuciya. "Uzairu, zan iya yafe maka, amma ba zan iya mantawa da abin da ya faru ba. Rayuwata ta lalace saboda laifin da baka sani ba. Amma ba zan hana ka ganin ‘ya’yanka ba."

Uzairu ya ji kamar zuciyarsa ta tsinke da farin ciki. "Nagode! Wallahi nagode! Ko da ba za ki dawo gare ni ba, hakan ya isa mini."
Chapter 50 · 0% Book details