← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 75

Sashe 10

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wane lokaci kake nufi? Ko dai mu aiwatar da shi ko kuma mu kashe ta gaba daya.”

Gora, wanda ya riga ya nuna rashin yarda tun da farko, ya sake matsowa.

“Wannan ba abu ne da zan iya aikatawa ba,” ya furta da karfi.

Shugaban ya kalle shi da fuska mai nuna rashin hakuri.

“Kai ne zaka zaba, ko dai ka aikata, ko kuma kai ma ka fuskanci hukuncin Hajiya Rumanah.”

Gora ya kara hararar shugaban, zuciyarsa cike da bacin rai. Ya jima yana rayuwa da laifi, amma bai taba zuwa inda aka ce ya wulakanta mace ba. Bai taba yi ba, kuma ba zai fara da wannan ba.

Ya sauke numfashi, sannan ya ce,

“Idan wannan shine abin da kuka shirya, to ni ba zan kasance da ku ba.”

Shugaban ya yi dariyar takaici, yana girgiza kai.

“Dama nasan kana da wata zuciya mai laushi. Ba ka dace da wannan aiki ba.”

Daga cikin sauran ‘yan fashin, wasu suka fara hada ido da juna, kamar suna tunanin cewa Gora yana da gaskiya. A wannan lokaci, an samu rarrabuwar kawuna.

A gefe guda kuma, Bala ya kalli dakin da aka kulle su Hajiya Zaytunah da Nabeeha. Yana jin zuciyarsa tana bugawa da wani irin yanayi da bai taba ji ba.

“Idan muka aikata hakan, me zai rage mana?” Bala ya fada a hankali. “Mu ‘yan fashi ne, amma ba azzalumai ba.”

Shugaban ya yi fuska, yana kallon Bala da Gora da mamaki. Bai zata cewa matsalar zata yi girma haka ba.

“Ina jin dai kun manta cewa mun karbi kudi a wannan aiki,” ya fada cikin bacin rai. “Kuma duk wanda ya ki aikatawa, to shi da kansa zai fuskanci hukunci.”

A wannan lokaci, Bala ya dauki mataki na rashin zato ya zaro bindigarsa!

Gaba daya ‘yan fashin suka ja da baya, sai wasu suka zaro makamai suma. Rikici ya fara tasowa, kamar tafasasshen ruwa.

Bala ya kalli shugabansu ido cikin ido, sannan ya ce da kakkausar murya:l,

“Ba zan bari ka wulakanta su ba. Idan haka ne, to sai dai ka kashe ni.”

Hakan ya tada hankalin sauran ‘yan fashin. Gora ma ya janye daga gefe, yana goyon bayan Bala. Sauran suka fara yin tunani.

Shugaban ya gane cewa idan har zai cigaba da tilasta su, to zai iya rasa hannun wasu daga cikin nasa.

Ya hura hanci, sannan ya girgiza kai.

“To, tunda haka ne, sai dai mu mayar da ita ga Hajiya Rumanah ta yi da ita yadda take so.”

Ya juya yana fita daga wajen, yana huci da takaici. Sauran ‘yan fashin suka bi shi, amma akwai wadanda suka yanke shawarar cewa wannan shine lokacin da za su daina wannan aiki.

Bala ya dubi Gora, sannan ya ce cikin sassanyar murya:

“Mun ceci rayuwar su, amma ba mu san makomarsu ba.”

Bayan shugabansu ya bar wajen da fuskar rashin jin daɗi, Bala da Gora suka kalli juna, kowanne yana nazarin abinda ke zuciyar ɗan uwansa. Sun san cewa sun yi kuskuren yin adawa da shugabansu, kuma hakan na iya jawo musu matsala. Amma sun yanke hukunci rayuwar Hajiya Zaytunah da Nabeeha ta fi komai muhimmanci.

Daga can gefe, wasu daga cikin ‘yan fashin suka ja baya, ba sa so su tsoma kansu cikin lamarin. Wasu kuwa sun riga sun yanke shawarar cewa wannan aiki ba zai ci gaba ba.

Bala ya lumshe ido, yana jin zuciyarsa tana dukan uku-uku. Ya san cewa idan aka mayar da Hajiya Zaytunah da Nabeeha ga Hajiya Rumanah, to babu shakka za su fuskanci matsananciyar azaba. Dole ne su yi wani abu da wuri.

“Gora,” ya ce da ƙasa da murya. “Dole mu ceci su kafin a kai su wajen Hajiya Rumanah.”

Gora ya gyada kai, yana jin wani irin karfin gwiwa na ratsawa cikin zuciyarsa.

“Amma yaya za mu yi hakan?” Gora ya tambaya. “Shugabanmu yana da ido a ko’ina. Idan muka yi kuskure, mu da kanmu za mu rasa rayukanmu.”

Bala ya dube shi, yana murmushi mai cike da rashin tsoro.

“Idan muka tsaya muna tunani sosai, lokaci zai kure mana. Mu aiwatar da shirinmu kafin su kai su wajen waccan muguwar mata.”

Bala ya sake duba dakin da aka daure Hajiya Zaytunah dasubNabeeha. Idanunta sun cika da hawaye, sai dai yanzu ta fahimci cewa akwai wani abu da ke faruwa tsakanin ‘yan fashin. A ganinta, kamar dai ba dukkansu ne suka amince da azabar da aka bukaci a yi mata da ‘yayanta ba.

Bala ya juya ya dube Gora.

“Zan nemo wata mota, sai mu fita da su cikin dare.”

Gora ya sauke numfashi. “Kana nufin mu fitar da su ba tare da wani ya gane ba?”

Bala ya gyada kai. “Haka nake nufi. Idan muka yi hakan cikin sauri, kafin shugabanmu ya dawo daga shirin aikawa da Hajiya Rumanah sakon cewa an kama su, to za mu iya fitar da su lafiya.”

Gora ya sake duban sauran ‘yan fashin da ke gefe. “Me kuke tunani?”

Daya daga cikin su ya numfasa. “Ni dai na san cewa idan suka koma wajen waccan mata, za su fi shan wahala fiye da yadda aka yi musu a nan.”

Wani daga cikinsu ya ce: “Ina tare da ku. Idan dai zamu cece su, dole ne mu yi hakan yanzu.”

Da dare sosai, Bala da Gora suka shiga cikin dakin. A hankali, suka warware igiyoyin da ke daure Hajiya Zaytunah da Nabeeha da Hammad.

“Ku yi shiru,” Bala ya ce da su, yana duban kofa don tabbatar da cewa babu wanda ya lura da su. “Za mu fitar da ku daga nan, amma dole ne ku bi umarninmu.”

Hajiya Zaytunah ta kasa magana, zuciyarta cike da tsoro da fargaba. Ita dai ba ta fahimci dalilin da yasa wasu daga cikin ‘yan fashin suka canja ra’ayi ba, amma duk da haka, ta san cewa wannan shi ne damar da zasu iya samu don su tsira.

Nabeeha ta kalli Bala da Gora, tana jin wani irin fargaba. Amma lokacin da ta kalli idon Gora, ta ga baƙon abu a ciki, ba irin mugunta ba ne da ta saba gani daga sauran ‘yan fashin, sai dai

Bala ya riko mayafin hannun Nabeeha , Hammad da Hajiya Zaytunah yana matsawa cikin duhun dare. A hankali suke tafiya a gefen shinge mai katanga da ke kewaye da sansanin ‘yan fashin. Gora kuma ya tsaya yana saurarawa, yana jiran lokacin da zai tayar da hankali don jawo hankalin sauran ‘yan fashin zuwa wani wuri daban.

Hajiya Zaytunah tana jin jikinta yana rawa, ba don sanyi ba, sai don tsananin fargaba. Idan har suka yi kuskure, to ba shakka za a kama su kuma wannan wata babbar matsala ce da ba za ta iya fatan tsira daga gare ta ba.

Nabeeha kuwa ta kasa gane yanda ake tafiyar da lamarin, zuciyarta cike da addu’a da fatan samun mafita. Duk tsawon rayuwarta ba ta taba jin tsoro irin wanda take ji a wannan lokaci ba.

“Ku ci gaba da tafiya a hankali,” Bala ya rada musu a kunne. “Muna kusa da inda na ajiye wata mota da za ta fitar da mu daga nan.”

A cikin wannan lokaci, Gora ya matsa zuwa wani wuri da yake kusa da wani babban gangare. Ya dauki wata babbar duwatsu, ya jefar da ita a wani bangare na sansanin da ke kusa da inda wasu daga cikin ‘yan fashin suke gadin shinge.

A take, hayaniya ta tashi!

“Wane ne a can?” Wani daga cikin masu gadi ya daka tsawa, yana juyawa da bindiga a hannunsa.

“Wata kila wani abu ya fado,” wani ya ce.

“Sai dai mu duba don tabbatarwa,” wani daga cikinsu ya kara da cewa.

Suna tafiya don duba wajen, hakan ya samar da dama ga Bala da su Hajiya Zaytunah su ci gaba da tafiyarsu ba tare da an gano su ba.

Bala ya kai su zuwa wata tsohuwar mota da ke kusa da wata hanya da ke gefen daji. Ya bude kofar motar cikin hanzari, yana duban Hajiya Zaytunah da Nabeeha.

“ku shiga cikin mota,” ya umarce su.

Ba tare da bata lokaci ba, suka shige motar, zuciyarsu na bugawa da sauri. Bala ya kunna motar, sai dai a lokacin da ya fara juyawa don fita daga wurin, wani mummunan abu ya faru.

Daya daga cikin ‘yan fashin ya lura da motsin motar, sai ya daka wata tsawa da karfi.

“Waye ke cikin waccan mota?!”

A take, karar harbi ta biyo baya!

“Sun gano mu!” Nabeeha ta furta cikin tsananin firgici.

Bala ya cije lebe, yana danna motar da karfi don ya fice daga wurin. Motar ta yi kara, sai ya ja birki da karfi, yana kokarin kaucewa harsashin da ke shigowa.

Wani daga cikin ‘yan fashin ya ruga zuwa inda suke, yana kokarin harbawa, amma kafin ya samu damar yin hakan, Gora ya bayyana daga gefe, yana rike da bindiga!

“Ka ajiye makamin nan ko kuma na harbe ka!” Gora ya daka masa tsawa.

Mutumin ya tsaya cak, yana kallon Gora da mamaki. Bai taba tunanin cewa daya daga cikin ‘yan uwansa zai yi masa haka ba.

Kafin ya samu damar yin wani abu, Gora ya kwada masa kwallo da hannu, ya fadi a kasa sumamme!

Bala ya kalli Gora, yana jin zuciyarsa tana bugawa da sauri.

“Shiga mota!” Bala ya ce da Gora.

Ba tare da bata lokaci ba, Gora ya bude kofar motar, ya shiga cikin hanzari. Bala ya danne motar da karfi, suka fice daga sansanin da gudu.

‘Yan fashin da suka lura da abin da ke faruwa sun ruga da gudu suna kokarin bin su da harsasai, amma Bala ya ci gaba da tafiya da sauri, yana kaucewa harsashin da ake harbawa.

Bayan tafiya da gudu har na tsawon mintuna, Bala ya shiga wata hanya da ke cikin daji, ya rinka bi da hankali don kada su bar wata alama da za a iya binsu da ita.

Nabeeha ta kalli Hajiya Zaytunah, tana jin hawayen da suka cika mata idanu.

“Mun tsira, Ammi?” Ta tambaya cikin rawar murya.

Hajiya Zaytunah ta rungume ta da karfi, tana jin wani irin sanyi a zuciyarta. Daya hannunta Kuma takamo na hammad tana damtsewa
Chapter 10 · 0% Book details