← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 75

Sashe 37

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

INA MA'ABOTA TURARE!
Shin kuna son gida mai ƙamshi da nutsuwa? Kaya masu ɗaukar hankalin kowa? YERWA INCENSE AND MORE ta kawo muku kayayyakin turaruka masu kyau, ingantattu, da tsada mai rahusa!

🌟 Mene ne za ku samu?

Turarukan wuta don gida, kaya, da tsugunno.

Khumrahs masu kamshi irin na Borno, Chadi, da Sudan.

Oil perfumes masu daɗin kamshi mai ɗorewa.

Turaren wanka, mopping, da wanki don dukkan sassan gida.

Man gashi mai gyara da fesa kamshi mai dadi.

Kayayyakin gyaran jiki na musamman don lafiya da ƙamshi mai ɗorewa.

📍 Adireshi:

Kano, amma muna tura kayayyakin mu duk fadin Najeriya da ƙetare.

📞 Tuntuɓe mu:

WhatsApp ko kira: 08095215215 / 09044191709 / 09134848107

Instagram: @yerwaincense_and_more

Facebook: @yerwacollection

Twitter:Hafsaaat00

🌐 Don ƙarin bayani da hotunan kayayyakin mu: Ku ziyarta mu a TikTok:
@besturarenwutainkano
https://www.tiktok.com/@besturarenwutainkano?_t=ZM-8s89xrbgS3x&_r=1

🎉 DON RAGI NA MUSAMMAN: Idan za ku siya, ku faɗi cewa daga ZAFAFA ne!

🌹 Ku more gida da jiki mai kamshi, nutsuwa, da farin ciki. Sai dai kayan turaren YERWA INCENSE AND MORE!

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_

_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:33_

Daren ya yi shiru, sai iska mai laushi da ke kadawa cikin lambun gidan. Wutar fitilun da ke zagaye da falon shakatawa sun haskaka fuskar Captain Fawaaz Dawud, wanda ke tsaye a cikin duhu, yana kallon sama kamar yana nazarin taurari.

A zuciyarsa, yana jin wani irin nauyi da bai taba jin irinsa ba. Nabeeha da iyalanta za su bar garin zuwa wani lokaci.. Wannan yana nufin cewa ba zai sake ganinta ba har sai Allah ya kawo wata dama.

Ya lumshe ido na wani lokaci, kafin ya juyo ya kalli hanyar da take tahowa. A kwance fuskar Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad take, ba tare da wata damuwa ba. Amma idan aka kalli cikin idanuwanta, sai a ga wani irin soyayya da ke boye a zuciyarta, soyayyar da ta kasa furtawa da bakinta.

Bata gama karasowa ba, Fawaaz ya ji wani abu na taso masa daga zuciyarsa. Kafin ya ankara, sai da ya tsugunna a gabanta, yana kokarin saukar da idanuwansa cikin nata. He kneeled down on his knees .. begging for her love 🥹

Nabeeha ta tsaya cak, tana kallonsa da mamaki. Idanunta suka zaro da dan razana.

"Yaa fawaaz?"

Ya kasa magana na wasu dakiku. Hannunsa ya dan taba cinyarsa, yana jin yadda gwiwoyinsa suka daskare akan simintin.

"Nabeeha," ya furta da murya mai sanyi, amma wacce ke cike da nauyi. "Ba zan iya barinki ki tafi ba tare da kin san gaskiyar zuciyata ba."

Zuciyarta ta buga da karfi. "Gaskiya?" Ta furta a hankali.

Fawaaz ya saki wata ajiyar zuciya, yana kokarin danne nauyin da ke kansa. "Yes. I love you, Nabeeha. Ina sonki fiye da yadda kike tunani."

Hawaye ya cika idanuwansa. Duk da miskilancinsa, ya san cewa babu wata dabara da zai iya amfani da ita a wannan lokaci. Wannan ba fagen yin taurare bane, ba lokaci bane da zai boye soyayyarsa a karkashin kamun kai.

"Kiyi hakuri," ya ci gaba da magana, muryarsa na rawa. "Na jima da fahimtar cewa ke ce kadai mace da zuciyata take bukata, amma na ki furta hakan."🤭

Ya runtse idanuwansa kamar mai jin radadi. "Na ki bari ki san yadda kike da muhimmanci a rayuwata. Amma a yau, ba zan bari ki tafi ba tare da kin san cewa ina matukar son ki ba."

Nabeeha ta saki numfashi, zuciyarta na kokarin daukar nauyin kalmomin da ta ji. Ba ta taba tunanin cewa Fawaaz, mutumin da ke da kamun kai da miskilanci, zai iya furta irin wadannan kalmomi ba.

"Yaa fawaaz… ka tabbata da abinda kake fada?" Ta tambaya cikin rawar murya.

Ya bude idanuwansa a hankali, yana kallonta da soyayya mai cike da tsafta.

"Yes, Nabeeha. I am sure. I have never been more sure about anything in my life."

Ta dauke kai a hankali, hawaye na taruwa a gefen idanuwanta. "Amma me yasa yanzu, Yaa Fawaaz? Me yasa sai a daren da zan tafi?"

Yayi murmushi, murmushin da ya fi kama da radadi fiye da jin dadi. "Saboda na ki amincewa da zuciyata tun farko. Saboda na dade ina kokarin danne soyayyarki a raina, amma sai gashi yanzu tana neman tarwatsa zuciyata."

Ya kara matsowa kusa da ita, yana kallonta da wani irin yanayi da ya sanya ta kasa dauke idonta daga nasa.

"Nabeeha," ya sake furta sunanta, yana shafar hancinsa da hannunsa. "Ba na so ki tafi ba tare da kin san cewa babu wanda yake son ki kamar yadda nake son ki ba. Ko da kuwa ba zan taba samun ki ba, na fi so ki tafi da sanin gaskiyar zuciyata."

Hawaye ya gangaro daga gefen idanuwansa.

"I love you, Nabeeha."

Ta dan rusuna, zuciyarta cike da shauki da soyayya. Bata san lokacin da hawaye ya wanke fuskarta ba.

"Na jima ina jin hakan, Ya Fawaaz. Amma ba na son yin kuskure. Ka yi min alkawari cewa ba ka da wata mace da kake so kamar yadda kake so na."

Ya daga hannayensa sama kamar yana yin rantsuwa. "I swear by Allah, ke kadai nake so, Nabeeha."

Ta shafi fuskarta da tafin hannunta, tana kokarin boye jin dadinta. "Na amince da kai, Yaa Fawaaz."

Wani irin sanyi ya sauka a zuciyarsa. Ya lumshe idanuwansa na wani lokaci, kafin ya bude su a hankali.

"Thank you, Nabeeha. Thank you for trusting me."

Suka tsaya suna kallon juna, kowannensu yana jin irin soyayyar da ba su taba bayyanawa da fadar magana ba. Daren nan ya dauke su a cikin shaukin da ba za su taba mantawa da shi ba.

Iskar dare ta ci gaba da kadawa cikin lambun gidan, tana tayar da sassanyar ƙamshin furannin da ke kewaye da su. Fawaaz har yanzu yana tsugunne a gaban Nabeeha, yana kallonta da idanuwansa masu cike da so da buƙatar ta fahimce shi.

She was standing still, her heart pounding wildly in her chest. Never had she imagined that Captain Fawaaz Dawud, the ever-mysterious, ever-distant man, would kneel before her and pour out his heart like this.🥹

Hannayensa sun yi sanyi a gefensa, yana kallonta da idanuwansa masu tsananin zurfi. "Nabeeha," he whispered, his voice laced with raw emotion. "I can’t let you go without telling you what’s in my heart."

A cikin zuciyarta, tana jin kamar zata daina numfashi.

"Yaa Fawaaz..." Ta kira sunansa da murya mai sanyi, idanuwanta cike da jin ƙauna da tsoro. "Why now? Why tell me this on the night I’m leaving?"

Yayi shiru na wasu dakiku, kafin ya saki wata ajiyar zuciya mai nauyi.

"Because I have been a fool," he admitted. "Because for too long, I let my pride and my fears stop me from saying what my heart has always known—I love you, Nabeeha. I love you more than I ever thought possible."

Hawayen da take ƙoƙarin hana su zuba sun gangaro a kumatunta.

"Fawaaz, you don’t know what you’re asking of me."

Ya girgiza kai a hankali, yana kallonta da kulawa. "I know exactly what I’m asking. I am asking you to believe me. To know that I have never felt this way about anyone before. And I don’t think I ever will."

Zuciyarta ta buga da ƙarfi. Tana jin cewa idan har zata amince da kowa a duniya, to Fawaaz ne.

"But what if fate separates us? Idan kaddarar mu bata haduwa bace ba fa?" Ta tambaya da murya mai sanyi.

Fawaaz ya ɗan saki wani murmushi mai cike da zafi. "Then I will fight for us. I will find you. I will prove to you that what we have is real. Ina matukar kaunar ki"

Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ɗaga hannunta ta kama nasa. Wannan shi ne karo na farko da ta taɓa yin hakan, kuma jin sa a tafin hannunta ya sanyaya zuciyarta fiye da duk wani abu da ta taɓa ji.

"I won’t make promises, Yaa Fawaaz," she whispered. "But if we are meant to be, I believe fate will bring us together again."

He closed his eyes for a moment, as if letting her words sink deep into his soul. Then, slowly, he nodded.

"That’s enough for me, Nabeeha. That’s all I need to hear."

She smiled through her tears. "Take care of yourself, Yaa Fawaaz."

A hankali, ta janye hannunta daga nasa, sannan ta juya. She walked away without looking back—because she knew that if she did, her heart would never let her go.

Fawaaz remained on his knees, watching her disappear into the night. His heart ached with longing, but deep down, he knew one thing—what they shared was not something time or distance could ever break.🥹🤭

Fawaaz ya ci gaba da kallon Nabeeha har sai da ta bace cikin duhun dare. Wani irin sanyi da daci suka gauraya a zuciyarsa, yana jin kamar ba zai iya motsawa ba.

Ajiyar zuciya ya sauke, ya runtse idanuwansa na ɗan lokaci, yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi. "Ko da kuwa za ki tafi, Nabeeha," ya furta a hankali, "na riga na ajiye soyayyarki a zuciyata."

A can gefe, Nabeeha ta tsaya a bakin kofa, tana kallon sama. Ta lumshe ido, tana jin kalmomin Fawaaz na ci gaba da karade zuciyarta.

"I love you, Nabeeha."

Wani irin shauƙi ya ziyarci zuciyarta. Bai kamata ta yi tunanin cewa wannan rabuwa ce ta har abada ba, saboda zuciyarta ta riga ta gamsu da cewa Fawaaz yana sonta da gaske. Amma har yanzu, akwai abubuwa da yawa da ba ta fahimta ba.

Ta dan runtse ido, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa. "Idan kaddara ta so, Fawaaz," ta furta a hankali, "to wata rana, za mu sake haduwa."

A can bayan ta, Fawaaz yana tsaye yana kallonta daga nesa, ba tare da ta sani ba. Bai san lokacin da ya runtse ido ba, yana jin wani nauyi yana danne zuciyarsa.

"I will wait for that day, Nabeeha," ya furta da wata murya mai sanyi. "No matter how long it takes."

Daren yana da shiru, amma zuciyoyinsu na cike da kalmomin da ba su fada ba. Wannan ba dare ne na rabuwa ba, dare ne na alkawari, na fata, da kuma soyayyar da lokaci ba zai iya rushewa ba.

ADVERT👇
Chapter 37 · 0% Book details