← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 75

Sashe 1

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE... AKAN NERA DARI BIYAR KACHAL.TUNTUBENI TA 09134848107 DON MALLAKAR NA KU...

*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO:_*

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

_Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai..... Assalamu Alaikum Wa Rahamatullahi Wa Barakatuh!!_

_Barkan mu da dawowa daga hutun Ibadah!! Allah yasa munyi ibada karbabbiya, Allah yasa muna daga cikin yantuttun bayin sa. Allah kuma ya biya mana dukkanin bukatun mu. ya kuma yafe mana kurakuren mu. Aameen. Fatan anyi sallah lafiya? Toh Allah ya karba mana Amin... Zafafa na miko gaisuwa da dinbin fatan alkhairi agare ku😍🎀_

_PAGE 1:_

°•°•°•°•

**Tamkar* a mafarki, tana jin kamar zuciyarta ta fada cikin wani irin nauyi da ba ta taba jin irinsa ba. Kalaman Fawaaz sun kasance kamar wani sako daga duniyar da ba ta taba tsammani ba, amma a lokaci guda, suna da karfi fiye da yadda take iya dannewa.

Hannunta yana rawa, ta sauke ajiyar zuciya, amma kafin ta samu damar kara tunani, karar kararrawar motar yan fashin dake gefe ya katse ta. Ta dago kai da sauri, zuciyarta tana dukan uku-uku, tana kallon yadda daya daga cikin 'yan fashin ya matsa kusa da su da wata matsananciyar fusata a fuskarsa.

"Nace maki kiyi shiru, ko kuwa kina bukatar a koya maki darasi?" Ya fadi cikin tsawa, yana daga hannunsa da wata sanda kamar zai buga musu.

Nabeeha ta razana, ta rufe idonta a firgice, amma kafin ma ta iya tunanin yin wani abu, Hajiya Zaytunah ta tare ta da jikinta, tana cewa da murya mai sanyi,

"Don Allah, ku yi hakuri. Ta dan razane ne, amma ba zata sake ba."

Nabeeha tana jin kamar ana karanta mata labari ne daga wani littafi na soyayya. Amma wannan ba labari bane, Fawaaz ne, mutum mai rai da numfashi, wanda bai taba nuna wani irin motsi na soyayya a kanta ba, sai yau.

Tana jin bugun zuciyarta yana karuwa, amma a lokaci guda tana cikin wani hali mai wahala. Wani bangare na zuciyarta yana son amsa sakon nan take, yana son fadin abin da ke zuciyarta,. Amma wani bangare kuma yana ji kamar ba wannan ne lokacin da ya dace ba. Yanzu haka suna hannun 'yan fashi, cikin yanayi na tsoro da fargaba, kuma har yanzu ba su san yadda za su kubuta ba.

A hankali ta dauke idonta daga kan hannunta da aka daure da igiya, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Idanunta suka sauka kan Hajiya Zaytunah wacce ke kokarin kwantar musu da hankali.. Ta dan kakaro murmushi tana kokarin danne hawayen dake kokarin zuba daga idanun tah...

A zuciyarta, Nabeeha tana jinjina irin tashin hankalin da suke ciki. Amma zuciyarta ba za ta iya musun yadda sakon Fawaaz ya shigeta ba. Tun farkon haduwarsu, ya kasance mutum mai nisa, miskili wanda bai fiye magana da ita ba sai idan ya zama dole. Musanman da shi din magana ta fatar baki ma bata dame shi ba. Ki cikin yan uwansa da suke ciki daya baka Jin bakinsa..Amma yau… yau ne rana ta farko da ya furta wani abu mai kama da soyayya a gare ta.

Hannunta na rawa, sai ta sake duban hannun ta..Tamkar wayar ce agabanta. Idanunta da kwakwalwar ta suna tariyo mata sakonnin fawaaz,

“Ki min alkawari cewa za ki tsaya min, Nabeeha. Ko bayan wannan wahala, kar ki guje ni.”

Sai ta runtse idonta, ta jin cunkoso a KIRJIN ta. Me zai hana ta amsa? Idan har akwai lokacin da zata fara tunanin Fawaaz da gaske, ba a cikin irin wannan hali ba. Amma zuciyarta ta riga ta furta amsa tun kafin kwakwalwarta ta tantance.

Kafin ta iya cigaba da dulmiya a duniyar fawaaz data lula, Razananniyar karar sautin muryar wani daga cikin yan fashin ya kurma kururuwa yana cewa,

"Lokacin lallasa yazo.."

Yan fashin sukayi kansu, Suka sake tamke daurin hannayensu da kafafuwansu, sai suka fara azabtar da su ta hanyoyi daban-daban.

Hajiya Zaytunah, wacce take da jiki da nauyi, an rike ta da karfi yayin da take kokarin kare 'ya'yanta Nabeeha da Hammad. Wani daga cikin 'yan fashin ya watsa mata mari mai karfi da ya gigita ta. Idanunta sun yi jajir saboda zafin dukan da ta sha. Kafin ta farfado daga girgizar marin, wani daga cikinsu ya fizgo gashinta da karfi, yana jan kanta zuwa gefe.

Nabeeha kuwa, duk da kokarin karfafa zuciyarta, ta kasa jurewa azabar da take sha. Wani dan fashi ya dunkule hannunsa ya kwada mata naushi a gefen cikinta, wanda ya sa ta zube a kasa da radadin ciwo. Ta narke, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Hawayen da ta kasa shanye wa sun zubo kan kumatunta.

Ya yinda wani daga cikin 'yan fashin ya rike hannun Hammad, wanda bai cika girma sosai ba, ya yi kokarin daga shi sama yana mai tsoratar da shi. Hammad ya yi kururuwa da murya mai tsanani, yana rokon su su sake shi. Amma maimakon su tausaya masa, sai suka dinga dukansa da sanduna a cinyoyi da hannayensa.

A cikin wannan halin, Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa. Ta durkushe tana rokon su,

“Don Allah, ku yi hakuri! Ku bar yaran nan haka, ku duke ni a madadin su!”

Amma 'yan fashin sai suka fashe da dariya, daya daga cikinsu yana cewa

"Ai ba mu dauko ku don sauki ba! Za ku dandana bakin ciki kafin mu raba ku da iska"

Duk azabar da suke sha, babu wanda ya kawo musu dauki. Duhu ya lullube su, tsoro ya cika zukatansu, kuma babu alamun kubuta a gaban su…

A yayin da azabar ta kara tsananta, Nabeeha ta kasa motsi, jikinta yana karkarwa saboda radadi da tsananin tsoro. Idanunta sun cika da kwalla, amma ta runtse su da karfi, tana fatan mafarki ne kawai, ko kuma wata rana mai kyau za ta farka ta ga komai ya wuce.

Hajiya Zaytunah ta kokarta ta tashi, amma wani dan fashi mai dogon gemu da idanu masu kaushi ya yi birgima da ita gefe, yana dariyar mugunta. Ya kama mata hannu, yana matsawa da karfi, har sai da ta saki wata kara mai tsanani.

“Ai yau ne ranar ku! Babu wanda zai cece ku!” ya fada da wata murya mai cike da izgilanci.

Hammad ya ci gaba da kiran mahaifiyarsa, yana kuka da karfi. Amma maimakon jin tausayinsa, daya daga cikin ‘yan fashin ya rike shi da karfi ya wurgar da shi gefe, har sai da ya bugi bango, Hammad ya saki wata kara, jikinsa yana rawar sanyi.

Daya daga cikin ‘yan fashin, wanda yake kamar su ne shugabansu, ya matso kusa da Hajiya Zaytunah yana kallonta da mugunta yace,

"Meyasa ake son aga bayan ku? Ku din su wanene? Kuna da babban daraja a wajen wadanda suka turo mu!” ya fada, yana gyara bindigar da ke rataye a kafadarsa.

Hajiya Zaytunah ta kasa magana. Hankalinta yana kan yaranta da ke kuka da radadi. Sai dai kafin ta iya cewa wani abu, sai daya daga cikinsu ya zaro waya ya fara daukar bidiyo.

“Muna so ki amsa mana tambayoyi!” ya fada yana zungurin Nabeeha da gefen takobinsa.

Sai da Nabeeha ta saki kara, jikinta yana karkarwa. Sannan daya daga cikinsu ya matso kusa da ita yana fadin,

"Da alama ke ce kadara a cikin ku! Domin an ja mana kunne akan ki sosai, Wannan ne zai sa mu ci gaba da azabtar da ku har sai mun ji daga gare su"

"Dan Allah kuyi hakuri. Wallahi mu ba kowa bane." Nabeeha ta fada cikin muryar ban roko da lallashi

"Bude muryar ki sosai kiyi magana..."

"Wallahi mu ba kowa bane. Dan Allah kuyi hakuri ku sake mu" Ta karasa fada tana fashewa da matsanancin Kuka..

Tsoro ya sake lullube su. Wane irin hali ne sukatsinci kansu? Shin akwai mai ceton su?...

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09032345899_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____

MX🎀
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:2_

Azaba da tsoro sun cika sararin da suke ciki. Numfashin Nabeeha yana fita da kyar, jikinta yana karkarwa yayin da yan fashin ke ci gaba da azabtar da su. Hajiya Zaytunah ta kasa jurewa ganin yadda suke dukan 'yarta da danta. Ta yi kokarin tashi amma wani daga cikin yan fashin ya hankada ta da karfi, ta fadi a kasa.

"Ke dai ba kya jin magana, ko?" Shugaban yan fashin ya fada da murya mai cike da tsawa.

"Ki gaya mana gaskiya! Wacece ke? Kuma menene SIRRIN da wasu ke kokarin karewa game da ke?"

Hajiya Zaytunah ta dan kalli Nabeeha da Hammad da ke kuka da radadi. Ta san cewa ba zata iya bayyana komai ba, amma azabar da ake yi musu na neman ya tilasta ta yin magana. Sai dai kafin ta iya cewa komai, daya daga cikin yan fashin ya janyo gashinta da karfi.

"Idan baki gaya mana ba, kiyi tunanin abin da zai faru da 'ya'yanki!" Ya fadi yana daga wuka.

Hammad ya kara fashewa da kuka.

"Don Allah ku kyale mu! Ba mu da laifi!"

Nabeeha kuwa ta kasa cewa komai. Kawai idanunta ne suka cika da kwalla, tana kallon mahaifiyarta cikin tausayi. Baki daya tausayin mahaifiyar tasu take bata. Taga rayuwar tsanani a baya. Yanzun da rayuwa take kokarin sauyawa musu sun fara Jin dadi kuma ga abunda ya biyo baya...

A wannan lokacin, wata yarinya daga cikin yan fashin ta matso kusa da su, tana kallon su da alama kamar tana jin tausayinsu. Amma kafin ta iya cewa wani abu, shugabansu ya daka mata tsawa.

"Ke kuma me kike Shirin yi? Idan baki da zuciyar cigaba da aiki, sai ki bar nan yanzu!"

"Sorry sir.... " Yarinyar fashin ta fada tana juyawa baya ta koma...

Zuciyar Hajiya Zaytunah ta buga da karfi. Shin akwai wanda zai taimaka musu daga cikin su? Shin akwai wata hanyar tsira?
Chapter 1 · 0% Book details