← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 75

Sashe 62

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sirrin da ya fara bayyana....

Tafiyar da suke yi a motar na da shiru, shiru mai cike da magana. Kowane daga cikinsu yana nazarin wanda ke gefensa. Duk da cewa babu abin da ya bambanta halayyar Fawaaz a zahiri, amma Nabeeha tana iya fahimtar cewa akwai wani abu da ya canza a tsakaninsu.

Fawaaz bai sake cewa uffan ba, amma hannunsa da ke kan sitiyari yana dan motsi kamar yana tunanin wani abu mai muhimmanci.

Nabeeha ta gyara zamanta. Ta sauke ajiyar zuciya. “Ya Fawaaz.”

Ya juyo a HANKALI, yana kallonta, idanunsa na bayyanar da zurfin tunani.

"Na’am."

“Wata rana… za ka iya bude AKWATIN SIRRIN ka?” Ta fada a HANKALI, kamar tana tsoron jin amsar da zai bata.

Fawaaz ya dan lumshe ido, sannan ya bude su da natsuwa. Bai amsa da sauri ba, sai da ya dauki lokaci yana kallonta, kamar yana kokarin sanin irin amsar da take bukata.

A karshe, sai ya murmusa kadan. "Idan kin shirya jin gaskiyar da ke cikinsa."

Nabeeha ta ji zuciyarta ta buga da sauri. Gaskiya? Shin menene gaskiyar da Fawaaz yake ɓoyewa a zuciyarsa?

Da suka iso gidan Humyrah, Fawaaz bai bar Nabeeha ta fito ita kadai ba. Sai da ya fita ya zagaya ya bude mata kofa.

"Kada ki dade," ya fada a hankali. "Ina nan a waje."

Nabeeha ta dan zaro ido. “Kana nufin za ka jirani yau ma?”

Fawaaz bai amsa ba, sai ya jingina da motarsa, yana kallonta da wani irin kallo mai nauyi.

"Ki fito da wuri."

Ta dan saki murmushi. “Ba zan jima ba.”

Tana shiga cikin gidan, sai ta tarar da Humyrah tsaye tana jiranta da fara'arta.

“Lallai kuwa! Daga ina kike da soja?” Humyrah ta fada tana dariya.

Nabeeha ta dan hade rai. “Me kike nufi?”

Humyrah ta matso kusa da ita tana tsokanarta. "Ai duk duniya babu wanda yake tsananta tsaro akanki kamar yayanmu Fawaaz."

Ta dan kalle ta da murmushi mai ma'ana, sannan ta gyada kai.

"Nima tun shekaru da yawa na fahimci cewa yana kaunarki, sai dai kawai miskilancinsa bai bari ya fada miki ba."

Nabeeha ta yi shiru, zuciyarta tana bugawa.

“Yana kaunata?”

Humyrah ta yi dariya. "Idan har baki gane ba, to ke ce matsalar!"

Fawaaz yana tsaye a gefen motarsa, yana jiran fitowar Nabeeha. Idanunsa suna kan kofar gidan, amma a zuciyarsa, yana tunanin abubuwa da dama.

"Shin, Nabeeha za ta fahimci cewa zuciyata ta dade tana ajiyarta a cikin Akwatin Sirrinta?"

Ya sauke ajiyar zuciya. Idan har akwai ranar da zai bude wannan akwati, to watakila, yau yana gab da hakan.

Ko da Nabeeha ta fito daga gidan, ta tsaya tana kallonsa na wani lokaci.

Shi ma yana kallonta, fuskar sa da natsuwa.

Sai ta taka a hankali, ta tsaya a gabansa.

“Yaa Fawaaz… Ni ma.”

Bai bukaci ta kammala maganarta ba. Domin ya rigada ya gane abin da take nufi.

Ya lumshe ido yana murmushi. A wannan lokaci, babu bukatar karin kalmomi.

Soyayya ta riga ta tabbatar kanta.

....

Falon gidan Gwaggo Zainabu cike yake da manyan mutane, kuma hirar da ake yi tana tafiya cikin annashuwa. Ana zaune cikin natsuwa, kowanne fuska cike da farin ciki da kwanciyar hankali.

A gefe guda, manyan mazajen suna tattauna al’amura. Alhaji Uzairu, Alhaji Amiru, Major General Dawud, Muhammad, da Fawaaz, tare da Chief Judge Abdulfatah da wasu dattawa biyu suna zaune, suna tattaunawa kan rayuwa da zaman duniya.

A dayan gefen kuwa, Gwaggo Hafsatu da Gwaggo Zainabu suna zaune cikin jin daɗi, suna sauraron hirar da ke gudana. Sai kuma Hajiya Zaytunah, wacce ke zaune cikin farin ciki, tana kallon sabuwar rayuwar da aka shimfiɗa mata.

Gidan da aka gyara mata ba ƙaramin kyawu yake da shi ba. Komai sabo ne, kayan cikin gidan na ƙasashen waje, tamkar wata sabuwar amarya. Abin da aka yi mata ya wuce tunaninta, ya nuna karramawa da daraja.

An ci, an sha, an yi nishadi. An yi hira mai cike da barkwanci da dariya. Sai dai daga bisani, hira ta sauya salo.

Dattawan suka fara maganar rayuwa da al’amuran iyali, har suka shigo batun matasa da aure.

Chief Judge Abdulfatah ya kalli Major General Dawud da murmushi. “Yallabai, har yanzu wannan ƙaton yaron naka yana da aure a gaba?” Ya nuna Fawaaz da sigar zolaya.

Dariya ta biyo baya. Major General Dawud ya yi murmushi. “Shi ya sani. Idan ya shirya, to muna nan.”

Alhaji Uzairu ya jinjina kai yana murmushi. “Mu ma muna da tamu ‘yar gidan. Idan tana da miji a gaba, to muna jiransa ya bayyana.”

Ana cikin haka, Alhaji Amiru ya dubi sauran dattawan da ke zaune, yana mai dariya. “Ni dai ina ganin, tun da duk bangarorin suna da amincewa da juna, me zai hana a daura auren nan take, a nan cikin wannan falon?”

Wani shiru ya biyo baya, kowa yana nazari. Sai kuma gaba ɗaya suka amince!

Daurin Auren Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad da Captain Fawaaz Dawud

A lokacin da aka tsara don daurin aure, yan uwan duk sun hallara a babban parlorn...Captain Fawaaz Dawud, ya kasance cikin kayan mutunci, tare da iyayensa da abokan arziki. Amarya, Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad, tana gida batasan wainar da ake toyawa ba ..

bayan sun gama tanadar komai an sayo su huhun goro da alawa, limamin masallacin gidan ne ya jagoranci daurin aure. An fara ne da ambaton sunayen ma’auratan da waliyyansu.

Amarya: Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad

Waliyyin amarya: Alhaji Amiru (wanda ya tsaya a matsayin waliyyi)

Ango: Captain Fawaaz Dawud

Waliyyin ango: Major General Dawud..

Limamin ya nemi waliyyin amarya, Alhaji Amiru, ya amince da bayar da auren Nabeeha ga Fawaaz. Sai Alhaji Amiru ya ce:

"Na aurar da Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad ga Captain Fawaaz Dawud bisa sadakin da aka yarda da shi."

Sai limamin ya tambayi ango, Captain Fawaaz Dawud, ko ya karɓa. Fawaaz, cikin kamun kai da nutsuwa, ya ce:

"Na karɓa."

Daga nan sai limamin ya yi addu’a, tare da albarka ga ma’auratan. Jama’a suka yi farin ciki da yin kabbarar "Allahu Akbar!" don nuna gamsuwa da amincewa da auren.

Bayan an kammala daurin aure, an yi wa ma’auratan addu’o’i.

A wannan rana, Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad ta kasance a gida cikin halin rashin sani. Ba ta da masaniya cewa an riga an daura aurenta da Captain Fawaaz Dawud. Tun da safe, an hana ta fita, kuma duk wanda ta tambaya sai dai a bata amsar da ba ta fahimta sosai ba.

Da yamma, bayan daurin aure, Fawaaz ya isa gidan da aka kai amarya. Ya shiga cikin gidan cikin natsuwa, kamar yadda ya saba—ba shi da hayaniya ko nuna wata alama ta farin ciki sosai. Duk da haka, a yau akwai wani salo a tare da shi—salo na wanda ya gama nasarar da bai taba zato ba.

Akwai wata dakiya a cikin falon lokacin da ya zauna akan kujera, yana kallon Nabeeha da ta tsaya a gefe, cikin shigar biki, amma har yanzu tana cikin rashin tabbas. A zuciyarta tana zargin wani abu, amma ba ta da cikakken bayani.

Ya janye numfashinsa a hankali, yana dubanta da idanuwansa masu zurfi. A dai-dai lokacin, Nabeeha ta kasa jure shiru.

"Yaa Fawaaz, me ke faruwa?" Ta tambaya, muryarta na nuna rashin tabbas.

Fawaaz ya kalli gefen gefe, sannan ya dawo da idanunsa gareta. Cikin nutsuwa, ya furta,

"Kin amince da kaddara, ko?"

Nabeeha ta rike hannayenta, tana nazarin fuskarsa. "Eh, amma—"

Sai ya katseta da cewa: "Toh yanzu, ni ne kaddararki. An daura mana aure."

Zuciyarta ta buga! Ta zaro ido, tana kokarin tabbatar da abin da ta ji. "Me?"

Ya dube ta ba tare da sakewa ba. "Kin ji abinda na fada. Kin zama matata, Dr. Nabeeha Uzairu Muhammad Dawud... Mrs, captain Fawaaz. ."

Jikinta ya yi sanyi. Hannunta ya fara rawa a hankali, zuciyarta na dokawa da karfi. Wane irin abu ne wannan? Yaya hakan ya faru ba tare da saninta ba?

Amma Fawaaz bai bar mata damar juyawa ba. Ya mike tsaye, yana kallonta kai tsaye.

"Duk tambayar da kike da ita, sai mun koma gida."

Shiru ya ratsa tsakaninsu. Lokaci daya, ta fahimci cewa rayuwarta ta canza gaba daya.

Ya karasa kusada ita ya sakar mata sunba a gefen kumatunta. Ya sanya rigarsa yana goge mata hawayen da ke zuba daga idanun ta. Ya shiga rada mata,

"Kuka....ki dena zubar mun da tsadaddun hawayen ki please. Ki adana su sai nan gaba. Ranar daren mu na masoya. Ina kaunar ki Nabeeha. Kuma inshaa Allah da yardar Allah ba zaki taba Dana sanin aure na ba.. I love you long time. Love you big."

Ta masa dena kukan sai ma sake Jan sautin kukan da takeyi tana rerashi a HANKALI.

Fawaaz, da yake ba mutum bane mai yawan surutu ko bayani, sai ya zauna a gaban Nabeeha, yana kallonta da idanunsa masu zurfi. Cikin nutsuwa, ya furta da murya mai nauyi da zurfi,

"Nabeeha, from this moment on, you are mine. My wife. My responsibility. My peace. I know this is unexpected for you, but for me, it’s something I have long accepted. Fate has written your name next to mine, and I will honor that..I will protect you, care for you, and stand by you. Not because I have to, but because I want to. Because you are mine now, and I am yours."💜

Ya tsaya, yana kallonta cikin ido, yana jiran ta fahimci nauyin kalamansa. Daga nan ya kara da cewa,

"You are no longer just Nabeeha Uzairu Muhammad. You are now Nabeeha Uzairu Muhammad Dawud. My wife."

Kawai sai ta fashe da Kuka. Mutumin ku ya wawuro abarsa ya riketa gam. Tamkar zaa kwace masa ita.. ya sanya hannunsa yana shafa gadon bayanta..

"Shhhhhh my love. Kukan ya Isa haka nan. Please mana, kinji babyluv?" Haka dai yayita rokonta yana bata hakuri..

Alhamdulillahi Nabeeha ta samu gata iya gata daga danginta Kashi biyu. Dangin mahaifanta su Alhaji uzairu. Dama danginta na biyu na su major general dawud..

Anmata kaya na lefe da saka rana Wanda aka hada a rana daya . Akwatina kuwa bayyana adadin yawansu da kayan cikin su ma bata lokaci ne. Babu ce kawai babu aciki.
Chapter 62 · 0% Book details