← Book details Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 75

Sashe 23

Kirjin Mai Hankali Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A dayan bangaren, an dan yi shiru na ‘yan dakiku kafin wata murya mai cike da tsoro da gaggawa ta karanto mata,

"Hajiya... Nine! Na tsere! Su duka sun shiga hannu! Tawagar fashi an tarwatsa su, kuma wadanda kika saka a sace, sojoji sun kubutar da su!"

Zuciyarta ta harba da karfi, hannunta na tsananta zufa. Ta dan daka tsalle daga kwanciyarta, tana jin wani irin jiri na neman dibarta.

"Me kake nufi? Su waye suka shiga hannu?" Ta tambaya, cikin wata irin murya da ta kasa boye gigicewarta.

"Yan uwana, duka an kama su! Ni kadai ne na tsira, kuma na bar garin gaba daya. Hajiya, na yanke shawarar sanar da ke, don ki san cewa shirin ya rushe. Mutanen da kika saka a sace, sun kubuta!"

Wayar ta kubce daga hannunta, ta fado a kan gadon. Idanunta suka firfito waje, zuciyarta na bugawa kamar za ta tsage KIRJIN ta ta fito. Ji take tamkar iska ta daina ratsawa cikin huhunta.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un...!" Ta furta a hankali, hannunta na kerma.

Ta kama kanta da duka hannayenta, tana jin yadda gumi ke keto mata kamar wadda aka tsoma cikin ruwa. Asirinta yana kokarin tonuwa! Idan har sojoji sun kama su, babu shakka za su tona mata asiri!

Ta dauki wayarta da sauri, tana kokarin sake jin cikakken bayani, amma sai ta fahimci cewa mutumin ya kashe wayarsa. Ta danna lambar a gaggauce, amma ba ta shiga.

Cikin tashin hankali, ta mike daga gadon, zuciyarta na lugude kamar ana dukan ganga a cikinta. Ta fara tafiya a rude a cikin dakin, tana rikita kanta da tunani.

"Me zan yi? Ya Allah, me zan yi?"

Hannu ta daura a kanta, tana jin tamkar duniyar ta ruguzo mata. Idan aka kama ta, menene makomarta? Me Alhaji Amiru zai ce? Ya za a yi idan wannan magana ta fito fili?

Ta durkushe a kan kafafunta, jikinta na kerma tamkar wadda zazzabi ya rufe. Idan wani ya ganta a wannan lokaci, babu shakka zai dauka cewa ta haukace!

Tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da karfi, yana kokarin tarwatsewa. Ashe, yau ce ranar da asirinta zai tonu?

Wayar ta ta Kara dubawa tana Kiran ainihin number mutumin daya hadasu da yan fashin... Ta sanar masa komai tamkar suna ganin juna yadda take labarta masa. Shiru ya ratsa tsakanin su. Duk da cewa ba ta ganin fuskar wanda take magana da shi, amma ta san cewa wannan labari ya razana shi. Hannunta na kerma, zuciyarta na cigaba da bugawa da karfi.

"Me kike nufi, Hajiya?" Muryar namijin ta sauya, akwai tsoro da damuwa a cikinta.

"Na ce sojoji sun kama su! Mutumin da ya kira ni yanzu ya ce tawagar fashi an tarwatsa su! Idan har sojoji sun kama su, ba shakka za su tona asirina! Dole ne mu dauki mataki kafin lokaci ya kure!"

Wani guntun shiru ya sake shiga tsakaninsu, sannan murya mai cike da taka tsantsan ta ce:

"Hajiya Rumanah, kina nufin ba a samu wanda ya kubuta ba?"

"Mutum daya ne ya tsira! Kuma ya ce ya bar garin gaba daya. Amma ka san me hakan ke nufi? Idan sojoji suka matsa wa wadanda aka kama, ba shakka za su fadi komai!"

Ta sake matsa wayar a kunnenta, zuciyarta na ci gaba da harbawa. Idan sojoji suka kama shi, kuma suka matsa masa, zai iya tona sunanta da duk wata alaka da take da wannan shiri.

"Dole mu nemi hanyar dakatar da binciken nan." Muryarta ta fito da karfi fiye da yadda ta zata.

"Hajiya, ai kin san wannan abu ba mai sauki bane. Idan har su sojoji sun riga sun kama su, to kuwa abu ya fi karfinmu."

"Baka gane bane?! Idan aka bincike su, kuma suka fadi sunana fa? Ka san me hakan ke nufi? Na gama, na mutu! Kuma ba ni kadai ba, hatta kai ma wannan abu zai shafe ka!"

Tayi tsit na ‘yan dakiku, tana kokarin daidaita tunaninta.

"Yanzu haka Alhaji Amiru bai san komai ba," ta furta a hankali, kamar tana magana da kanta. "Idan kuwa ya gano...!"

Sai ta dafe kanta, zuciyarta na lugude. Tun daga wannan rana, komai zai iya sauyawa. Ta san halin Mai gidan nata Alhaji Amiru, mutum ne mai tsananin taka tsantsan da mutunci, kuma yana da karfin iko. Idan ya gano cewa ita ce ta shirya sace mutanen da aka cece, me zai faru?

A lokaci guda, ta ji wani irin faduwar gaba. Idan ta gaza hana wannan bincike cigaba, to kuwa za ta iya rasa komai!

"Dole ne mu dauki mataki yanzu!" Ta kara nanatawa, da muryar da ta nuna ba za ta amince da wani shiru ba.

"Me kike so muyi, Hajiya?" Muryar namijin ta dawo da taka tsantsan.

Ta dan yi shiru na ‘yan dakiku, sannan ta furta cikin murya mai cike da karfin hali,

"Dole ne mu dauki matakin da zai hana wannan bincike kaiwa garemu. Kuma dole ne a gaggauta!"

Jikinta yana kerma, zuciyarta na bugawa, amma yanzu ta san cewa ba ta da wani zabi. Asirinta yana kokarin tonuwa, kuma dole ne ta dauki matakin da zai hana hakan faruwa.

Tirqashi!!!

_1-KALBIM:MAMUH GEE_

_2-KIRJIN MAI HANKALI (AKWATIN SIRRIN SA):MSS XOXO_

_3-ADUNIYATAH :HUGUMAH_

_4-AJIYA A DUHU: BILYN ABDULL_
°°
_1-BOOK DAYA:DARI BIYAR_

_2-BOOKS BIYU:DUBU DAYA_

_3-BOOKS UKU: DUBU DAYA DA DARI BIYAR_

_4-BOOKS HUDU :DUBU BIYU_

_5_YAN NIJAR: 1000CF: 89825722 NOUSAIBA LAWALI MARADI_
_ku tura receipt zuwa ga 09033181070_

*IDAN KATI NE A TURO TA WANNAN NUMBER:*

*09032345899.. SHEDAR KATIN MA NAN ZAA TURA. KATIN MTN!!MTN!!*
____
*
*KIRJIN MAI HANKALI*
_(Akwatin sirrin sa)_
_🧳👩‍❤️‍👨🌺_

*_The Vault Of His Secrets_*

_®️NANA HAFSATU (MX)_

_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_

*_BOOK TWO_*

_PAGE:19_

Jin shiru daga dayan bangaren ya tabbatar mata da cewa maganarta ta yi tasiri. Dole su dauki mataki, kuma dole su gaggauta kafin lokaci ya kure.

"Hajiya, ina jin tsoron cewa..."

"Kada ka ce min haka! Idan muka tsaya muna tsoro, to fa kowa zai sha da kansa!" Ta katse shi da wata irin kasala a muryarta.

Ta tashi daga inda take zaune, ta soma yawo a dakin, kafafunta suna bugawa da sauri a kan falon dakin kamar wadda take kokarin watsa duk wata damuwa da ke zuciyarta.

"Mun riga mun shiga, babu hanyar janyewa. Idan mun yi sake, sai dai mu shirya da kanmu zuwa gidan yari!"

A dayan bangaren, namijin ya sauke ajiyar zuciya. Sai can ya ce,

"To me kike ganin za a yi?"

"Binciken dole ne ya tsaya! Kamar yadda muka saba, dole ne mu hada hannu da wanda zai iya murkushe wannan magana kafin ta fita waje."

"Amma Hajiya, wannan binciken ba karamin abu bane. Idan har su sojoji ne suka sa hannu, ai kinsan ba lallai ne a iya hana su ba."

"Ba su ne matsalata a yanzu ba" Ta katse shi, tana kokarin hadiye tashin hankalinta. "Babban abin da ke gabana shi ne, ina fargabar cewa mai gidah na zai iya jin wani abu! Idan ya fara bincike, to kuwa babu shakka zai gane komai!"

Da zarar ta ambaci sunan Alhaji Amiru, sai shiru ya sake biyo bayan su. Kamar kowane lokaci, wannan sunan yana da nauyi, domin duk wanda ya san shi, ya san cewa ba mutum ne da za a iya yaudara da sauki ba. Idan ya gano cewa matarsa tana da hannu a cikin wannan danyen aiki, babu shakka zai dauki mataki. Kuma ita ta san cewa matakin ba zai zama mai kyau ba!

"Hajiya," murya mai cike da taka tsantsan ta sake bayyana, "ko kin tabbata babu wani da ya riga ya sanar da shi wani abu?"

Wani irin sanyi ya ratsa ta. Ta ji wani irin jiri yana neman daukarta. Idan har akwai wanda ya riga ya sanar da shi, to lamarin ya fi ta karfin tunani.

Ta hadiye yawu da kyar, ta ce,

"Ba zan iya cewa da tabbaci ba, amma zan tabbatar kafin gari ya waye. Ka tafi ka kula da abin da na fada maka. Idan wani daga cikin wadanda aka kama ya fara magana, dole mu samu labari kafin sauran mutane!"

"Hajiya, na fahimta. Amma fa wannan lamari yana bukatar shiri sosai."

"Ni zan shirya abin da ya kamata a bangarena. Kai kuma ka kula da naku."

Ta kashe wayar a fusace, sannan ta jefa ta a kan gado. Ta zura ido a cikin dakin, zuciyarta tana tafarfasa.

Kawai lokaci ne yake tsakanin ta da faduwar asiri! Idan ba ta yi gaggawa ba, rayuwarta za ta shiga ruftawa kamar gida mai tushe mai rauni.

Ta dubi agogon da ke gefen gadonta karfe uku da rabi na dare. Tana jin zuciyarta na tafarfasa da damuwa.

" dole ne na fara binciken sa!"

Wannan tunanin ya tsaya a zuciyarta kamar dutsen da aka kafa. Idan har yana da wani bayani da zai kai shi ga gano abin da take boyewa, to dole ne ta dakatar da shi, kafin lokaci ya kure!

Hajiya Rumanah ta kasa zama. Hankalinta ya gama tashi, zuciyarta na tafarfasa da tsoro da fargaba. Ta san cewa idan ta yi sake, komai zai fita hannunta.

Ba tare da bata lokaci ba, ta dauki wayarta, ta fara laluben lambar Hajiya Karama. Hannunta yana kerma yayin da ta danna kiran. Wayar ta fara ringin, zuciyarta na bugawa da karfi.

Bugu na uku, aka dauka.

"Hajiya Rumanah?!" Muryar Hajiya Karama ta fito da alamun bacci a cikinta. "Lafiya kuwa kike kirana a wannan dare?"

"Karama!" Hajiya Rumanah ta furta da wata irin murya da ba ta saba da ita ba,muryar mace mai cike da damuwa da fargaba. "Mun shiga matsala! Babbar matsala!"

"Subhanallah! Me ya faru?" Hajiya Karama ta tambaya, yanzu hankalinta ya fara dawowa hayyacinsa.

"Dan daban nan da muka tura... ya kira ni yanzu!" Ta sha jinin jikinta, sannan ta cigaba. "Karama, sojoji sun tarwatsa su! Duk an kama su, shi kadai ne ya tsira!"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Hajiya Karama ta furta, zuciyarta na harbawa. "Me kike nufi da an kama su?! Kin tabbata?!"

"Na tabbata, Karama! Kuma kin san me hakan ke nufi?! Idan suka fara magana, to fa...!"

Shiru ya ratsa tsakaninsu. Kowannensu ya fahimci girman abin da ke tafe. Idan har ‘yan fashin suka fadi hakikanin wanda ya dauke su aiki, to babu makawa SIRRIN su zai tonu!
Chapter 23 · 0% Book details