← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 86

Sashe 9

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mik'ewa ta yi ta juya ta kalle shi tace "Ya ma fita a rai na wallahi, kawai ka bar shi."

Za ta nufi k'ofar da za ta sada ta da d'akin ta ya yi saurin tare gaban ta ya kamo hannun ta ya nufi wajen teburin da ita ya na fad'in "Idan ba za ki ci tuwon ba ai ga sarauniya ta dafa mana wani abun, kuma zaiyi wuya ki ce ba za ki so shi ba, dan na yarda da girkin mata ta."

Khadija da ke kallon hannun shi dake cikin na Haseenah wani nauyayyen abu ta had'e a mak'oshin ta, yayin da ita kan ta Haseenah taji kamar ta fasa ihu, haka ta zuba abincin ta zauna ita ma, sakin baki Haseenah ta yi ganin Bilal ya haye k'afafun Usman ya sa hannu a farantin da ke gaban Usman d'in, haka ma Khadija ita ma ta saka na ta hannun a ciki, kallon ta Usman ya yi da dariya yace "Ki saka hannun ki mana, haka mu ke cin abinci anan."

A hankali ta zura hannu duk sai ta ji kan ta kamar bak'uwa a gidan, kamar ba gidan mijin ta ba haka ta ji kan ta, dan haka ma bata wani ci mai yawa ba sai kallon shiriritar su ta ke, haka aka gama kuma ya tashi ya tafi kai Bilal makarantar islamiyya, tun da ta shiga d'aki ta d'auki wayar ta, yanar gizo ta shiga manhajar WhatsApp, sak'onni ta samu masu yawa daga mutane da k'awaye, ta yi sa'ar samun k'awar ta Zeinab ta na kai ita, bayan sun gaisa ta tambaye ta ya amarci ne ta ke fad'a mata wai da matsala, duk abin da ya faru ta kwashe ta fad'a mata, shawarar da ta ba ta ita ce ta saki jikin ta ita ma yar gida ce aure ta ke, sannan ta canza wannan tsarin na cin abinci, dan ba zai yiwu ace ko ranar girkin ta sai dai aci tare duka ba, da irin haka su ka jima su na hira kafin Usman ya dawo ta taya shi ya shirya zai fita, jikka biyar (jaka biyar) ya bata kud'in girki duk da babu abin da za ta nema ta rasa a madafa, amma sanin akwai abin da za ta iya nema ya bata su, sallama ya mata kafin ya wuce d'akin Khadija, ya d'an d'auki lokaci kafin ya fito ya fita.

*11:00* daidai na rana Haseenah ta fito dan fara girkin rana, kamar yanda Usman ya fad'a mata cewa duk abin da ta ke buk'ata ko za ta yi ta nemi taimakon Khadija ko ta tambaye ta, kai tsaye falon Khadija ta shiga, ganin ta zaune ya sa ta yi sallama ciki ciki kamar an sata dole, da fara'a Khadija ta amsa ta na fad'in "Amarya kin fito?"

Wani shegen murmushi ta yi tace "Um."

D'orawa ta yi da "Dama zan fara girki ne, kuma yace na tambaye ki idan ina neman wani abu."

Cikin sakin fuska Khadija tace "Ayyah, kar ki damu kan ki, ga Uwani sai ku je tare ta taimaka mi ki."

Da sauri tace "A'a, ba na buk'ata, nagode, kawai ki fad'a min in da zan samu kayan, dan yace akwai duk abun buk'ata."

Cike da iko ta kalle ta tace "Hakane, kije to su na madafar."

A gadarance tace "Madafar a ina?"

Murmushin gefen labb'a ta yi ta mik'e tace "Muje na nuna mi ki."

Bin bayan Khadija ta yi har madafar, k'atuwar frigi (fridge) ta bud'a ta nuna mata tace " Za ki iya samun duk naman da ki ke so."

Haka ta nuna mata komai ta fice, ita kuma d'akin ta ta koma ta dauk'o wasu daga cikin kayan miyar da aka had'o ta da su, cire hijabi ta yi ta dauk'o naman zabbi dan wankewa ta fara aikin, ta yi k'ok'ari sosai wajen yin abin da ba ta saba yi ba, sai da ta ga miyar ta ta kusa kammala kad'ai ta d'ora ruwan silalar macca, d'akin Khadija ta je ta tambaye ta adadin wacce za ta dafa? Cike da sakin fuska tace " Eh to, za ki iya saka leda biyu, idan kinsan ba za ki yi bak'i ba."

Biyu ta saka kamar yanda ta fad'a mata, sai dai kuma a maimakon ya zo gida cin abinci sai ya kirata wai ta fidda mi shi abinci mai yawa zai aiko a d'aukar ma sa, gashi Aziza ta zo tare da k'awar ta, ga kuma wasu daga cikin dangi su na zuwa, ga kuma k'annan ta su uku sun zo, ga kuma mutanen gida.

*Za mu ga idan ki na da wayo ai.*🤪
08/01/2020 à 17:09 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

_SAMIRA HAROUNA_

*Littatafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._

*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

```Fatan alkairi masoya```

_Bismillahir rahamanir rahim_

*8*

Jin ba za ta iya d'ora wata tukunyar ba ya sa ta aiki Bilal d'an unguwar ya siyo mata bredi mai yawa, maccar da ta dafa sai ta juye wa mijin ta, bredi kuma ta had'a Khadija da shi tace ta rarraba, da mamaki Khadija tace "Amma Haseenah da ba ta isa ba aida wata ki ka d'ora, tun da akwai sauran lokaci bare ace a matse ake."

Shiru ta yi ta ba tanka ta ba, haka ta raba miyar wa sauran mutanen da ke wurin, ficewa ta yi daga madafar in da Aziza ta bita da harara, tab'e baki ta yi tace "Kiji wani iyayi kuma, ko ina ruwan ta da abin da ki ka ga damar yi, sai ka ce ke ba gidan mijin ki ba."

Cikin sanyin jiki Haseenah tace "Ke, wannan ai ba komai bane, gaskiya ta fad'a."

"Tab'." Cewar Aziza tare da kallon k'awar ta, farantin abincin su ta d'auka ta d'auki bredin tace "Muje d'aki sai mu ci ko."

Tashi su ka yi su ka bi bayan ta, abinci su ke ci su na hira, Haseenah dai na sauraren su sai dai ta yi dariya, har su ka gama su ka d'ora daga inda su ka tsaya, ko da yamma ta yi su ka kama mata aikin dare ta yi, da su ka gama za su tafi kyaututtuka ta ba su, turaruka da sauran kayan kwalliya da kud'i wai su shiga adaudaita, da k'yar su ka karb'i kud'in da ta dage sosai, su na tafiya ta koma d'aki ta yi wanka ta shirya dan tarbar mijin ta, ta na gamawa ta d'auki d'aya kwanukan abincin ta sallama har falon Khadija, amsawa ta yi Bilal na zaune kusa da ita ya na karatu, da murmushi ta amsa ta na fad'in "Amarya ke da kan ki?"

Sunkuyawa ta yi ta aje kwanukan ta d'ago ta kalle ta tace "Ga abincin ku nan."

Juyawa ta yi za ta fita Khadija tace "A'a, ban gane abincin mu ba, ni da wa? Ko kin manta ba'a raba abinci a gidan nan? Ai Abban Bilal bai yarda da haka ba, duka iyalinshi su na cin abinci tare ne."

Juyowa ta yi cike da gadara da ido tsakar kai tace "Eh, na sani, amma waccen ai tsohon yayi ne, yanzu kuma na shigo gidan, dole za'a samu canje-canje da dama, daga yanzu in dai girki na ne gaskiya miji na zai ci abinci a nawa b'angaren ne ba na shi ba."

Juyawa ta yi har ta fara takawa Khadija ta gyara zama tace "Haseenah, nasan kinsan abinda ki ke shirin aikatawa kamar k'ok'arin rusa farin cikin gidan nan ne, dan haka kar ki ce za ki biyo min ta wannan hanyar, da ba zan d'auka ba, kin ganni nan? Wallahi ba na d'aukar raini ko rashin kunya, zaifi mi ki tun wuri ki fara taka tsantsan, abinci kuma ki d'auki kayan ki ba zan ci ba, ba kuma zan bawa yaro na ba, dan bansan me ki ka saka mana a ciki ba."

Wata dariya Haseenah ta yi tace "Ikon Allah na kwance ya fad'i, wato ke yanzu tunanin ki kenan? Nima zan yi abin da ke ki ke yi ne, hum! To ki farka, ni ba boka ba malam zan mallaki miji na, ke kuma da ki ke barbad'e a abinci sai ki yi ta yi, da sannu k'aryar ki za ta k'are a gidan nan."

Tsaye ta mik'e da mamaki a fuskar ta tace " Au! Kema tunanin ki kenan? Hhhhhhhh, lallai yarinya, in kuwa har wannan shine tunanin ki, to ki zanca tun wuri, dan wata rana zuciyar ki za ta iya raya mi ki kema ki bi boka da malam dan samun zuciyar babban mutum, kinga kuwa har abada ba za ki san sirri na ba."

Matsowa ta yi kusan ta dafa kafad'ar ta tace "Haseenah, ina kishin miji na, amma duk da haka bai sa na ji a raina cewa zan iya cutar da ke ba, ki kwantar da hankalin ki sannan ki nutsu, sannu a hankali sai kema ki ciri tuta a wajen mijin ki, ni zan taimaka mi ki kamar yer uwa ta."

Matsawa ta yi nesa da ita yace "Me? Taimako? Ki na kishiya ta za ki taimake ni dan na samu soyayyar mijin mu? Allah ya kiyaye, to me ki ka d'auke ni? Ban cika mace ba ko me? To ba na buk'ata, nasan hayoyin da zan shawo kan miji na, ba sai wani ya taimaka min ba."

Murmushi Khadija ta yi wanda har ya fito da haurun makkar ta guda biyu, Haseenah kam juyawa ta yi ta koma na ta falon ta zauna, ta na kallo Haseenah ta shigo da kwanon ta aje mata a kan teburin ta ta fice, tab'e baki ta yi tace "Ina daidai ke wallahi, sai dai duk abin da zai faru ya faru."
Chapter 9 · 0% Book details