← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 86

Sashe 40

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon shi Khadija ta yi ta na wani shegen murmushi mai kama da na mugunta tace "Ka yi hak'uri Abban Bilal, ban raina ka ba, kuma ka isa ka sani komai na yi maka, amma banda hidimar matar ka, gaskiya matsayi na bai taka wannan matakin ba, ka yi hak'uri idan na b'ata maka rai."

Ta na fad'a ta rufe kwanukan ta juya ta bar wajen, komai bai ce ba sai bayan Haseenah da ya bi da abincin ya lallab'a ta har ta ci, saida su ka gama kad'ai ya samu ya fita, saida ya shiga wajen Khadija ya same ta falo zaune, tsaye ya yi a kan ta ya ciro kud'i aljihun shi ya mik'o mata yace "Ba na da tabbacin za ki yi abin da na saka ki, amma dan Allah ki taimaka ki mana abinci mai yawa saboda ba zan dawo ci ba, zan aiko a d'auka saboda akwai bak'in da su ka zo mana."

Karb'a ta yi da hannu biyu tace "Zanyi farin ciki a lokacin da nake aikin nan, saboda hidimar ka ce."

Juyawa ya yi zai fita ta bishi da "Adawo lafiya."

"Allah ya sa." Ya fad'a a tsaurare.

Tun k'arfe d'aya Khadija ta kammala komai kamar ba ta yi ba, sai bayan sallah azahar Usman ya aiko aka d'auki manyan kwanukan tare da lemun da aka had'a na zallar abarba, ba jimawa ta kira shi tace su na so su koma ganin jikin Baba, cike da k'aguwa yace "Kuje, amma ki tabbatar tare ku ka tafi da Haseenah, dan ba na son raba kan nan da ku ke, sannan kar ki manta su na gida an sallame su."

Kafin ta yi magana ya datse kiran, dama a shirye take ita kam, Uwani ta kalla tace "Uwani ki je ki fad'awa Haseenah ta shirya yanzu za mu tafi ganin jikin Baba."

"To." Cewar Uwani ta nufi hanyar fita, jim kad'an ta dawo tace "Na fad'a mata tace ta na zuwa."

Kallo suke su na hira har sama da awa d'aya Haseenah ba ta fito ba, Khadija ta k'agu sosai dan haka ta kalli Uwani tace "Uwani dan Allah koma ki sake fad'a mata ta gaggauta, har uku ta na shirin yi mana a gida ba mu fita ba, ni kuma a wannan lokacin madafa ya kamata ace zan shiga."

Fita Uwani ta sake yi, amma ko da ta dawo sai cewa ta yi "Umman Bilal wallahi da na shiga na same ta kwance akan kujera da d'aurin k'irji, da na fad'a mata sai tace wai da zata shiga wanka, amma kula ba ta jin dad'in jikin ta kawai ki tafi za ta je daga baya."

Saida Khadija ta lumshe ido saboda haushi, mik'ewa ta yi ta kalli Bilal tace "Ka koma d'aki ka sako kayan makarantar ka daga nan saina aje ka, dan banga anfanin dawowar ba tunda mun riga da mun makara."

"To Mummy." Ya fad'a ya na nufa d'akin shi, bayan yan mintuna ya dawo da kayan makarantar shi da jakar shi a hannu, Khadija kuma bawa Uwani makullai tace "Ki rufe ko ina sai ki same ni a mota."

Karb'a ta yi ta kulle ko ina ta fita waje ta same su a k'ofar gida su na jiran ta, shiga ta yi su ka wuce suna tafe su na hira har suka isa, Uwani ce ta fito da kwanukan ita kuma ta na rik'e da jakar ta, haka suka shiga bayan sun gaisa suka zauna aka d'an tab'a hira, ana fara kiran sallah Khadija ta tashi su ka yi alwala su ka yi sallah, suna gamawa kuma suka musu sallama suka tafi saboda kar Bilal ya makara, haka suka aje shi sannan suka wuce gida kai tsaye, da shigar su ta hangi motar Usman, ba ta yi mamaki ba dan tasan wasu lokuta ya kan dawo ya yi wanka, su na shiga falon su suka ja birki ita da Uwani saboda ganin Usman zaune kai da gani kasan babu arziki ko mutunci cikin zaman, gabanta na fad'uwa ta k'arasa kusa da shi tace "Abban Bilal ashe ka dawo? Sannu da zuwa."

Uwani ya ma jan kallo yace "Kira min Haseenah."

Wucewa ta yi ba tace komai ba dan dama tun farko ya na mata kwarjini, Haseenah ta kira suka fito kusan a tare, tsaye duka su ka yi sai Uwani da ta fita farfajiyar gidan, tsaye ya mik'e yace "Nace ku tafi tare, amma me ya sa ki ka tafi ki ka barta?"

K'aramar ajiyar zuciya ta sauke ta kalli Haseenah tace "Na fad'a mata ai, da farko mun jira ta sai tace ba ta jin dad'i mu tafi kawai."

Kallon Haseenah ya yi yace "Ke ya ki ka fad'a min?"

Ko kallon Khadija ba ta yi ba ta kalle shi tace "Bansan za su tafi ba, fitar su kawai na gani daga gida, idan da ta fad'a min ai zan bisu tunda lafiya ta k'alau."

Kallon Khadija ya yi yace "Na d'auka zan iya fad'a mi ki kiji ashe ba haka bane, yanzu ina so naji raina ni ne ki ka yi ko me?"

Da mamaki ta kalli Haseenah ta kalle shi tace "Amma fa wann..."

"Amma me, ki na so ki nuna ba na da mahimmanci ne ko me? Zan fad'i yanda na ke so ayi a cikin gida amma ke kiyi gaban kan ki, wannan ai iskanci ne da d'aukar mutane yan iska, to ban makullin motar."

Da mamaki kawai ta ke kallon shi kafin tace "Makullin mota kuma?"

Zaro ido ya yi yace "Eh, ko taki ce? Ai ba yan uwan ki bane suka siya mi ki bare ki ji dad'in magana, ni ne na siya da kud'i saboda tunanin kin cancanta."

Hannu tasa a jaka ta fito da makullin ta mik'a mi shi, hannu ya zuro zai karb'a ta rik'e tace "Zan baka, amma ina so ka k'ara bincike akan lamarin nan, sanin kan ka ne wannan yarinyar ba ta kai na tsaya na mata k'arya ba, Uwani ita ce na aika ta mata magana, kuma Bilal ya na wajen."

Haseenah ce ta katse da cewa "Uwani? Ita ce tace mi ki ba zanje ba? K'arya take wallahi, wannan yarinyar fa munafuka ce wallahi."

A fysace Khadija ta kalle ta tace "Kar ki sake kiran Uwani munafuka dan ba ita ba ce, Uwani ba yau mu ke tare da ita ba, nafi sanin ta fiye da ke kamar yanda shi kan shi ya fi sanin ta fiya da ke."

Cike da rashin kunya tace "Idan an kira ta munafukar me za ki yi? Me ya sa ki ke son had'a yar aikin gidan nan da mu ne? Da alama wata rana ma cewa za ki yi matar shi ce ita ma."

"Kai." Ya daka musu tsawa, cikin b'acin rai yace "Akan wata banzar yar aiki ne za ku tsaya kuna musayar yawu? Ba na so, kowace ta wuce d'akin ta."

"Banza? Uwani ce banza?" Cewar Khadija ta na kallon shi, "Eh na fad'a, ko nima rashin kunyar za ki min?"

Rumgume hannaye Haseenah ta yi tace "To ai ba ka wuce ta maka ba tunda ka tab'a yar gold d'in ta, wallahi yarinyar can munafuka ce ta gidan gaba, ranar ma ai duk ita ta haddasa masifar da matar ka ta kusan k'ona ni da raina."

"Oho, hakane kenan?" K'ofar fita ya nufa ya na fad'in "To bara ki gani, yau zata bar gidan nan kuma na ga wanda ya isa ya hana tunda gida na ne."

Tun daga k'ofa ya fara kiran sunan Uwani, da sauri ta matso dan ba nisa ta yi sosai ba, Khadija ma bayan shi ta biyo ta na fad'in "Dan girman Allah Abban Bilal kar ka yi haka, ka k'yale yarinyar nan, in Allah ya yarda babu abin da zai sake faruwa da za ka ji sunan Uwani a ciki."

Ko sauraren ta baiyi ba saida ya tsaya gaban Uwani ya kalle ta yace "Ke, na fahimci zaman ki a gidan nan ba zai yiwu ba saboda matsalar da ake samu, dan haka karb'i nan." Ya fad'a ya na fito da kud'i aljihun shi masu yawan gaske da baisan ko nawa ne ba ya mik'a mata yace "Ki je na kore ki, ba na son sake ganin ki a gidan nan, kinji ko?"

Ruwa ne ya cika idon Uwani ta na kallon Khadija, ganin ta k'i amsar kud'in ya sa ya janyo hannun ta ya damk'a mata ya na fad'in "Karb'i na ce ko."

Juyawa ya yi ya koma ciki sai Khadija ta dafa ta tace "Ki yi hak'uri Uwani, wannan ita ce jarabawa ta a game da k'ara auren Usman, kije Uwani, ban ji dad'in korar ki da ya yi ba, amma dai hakan ya sa hankali na ya kwanta, dan a yanda ya ke jin kansa yanzu zai iya wulak'anta ni a gaban koma waye, wanda ni kuma ba zan so hakan ba."

Kuka sosai Uwani keyi da k'yar Khadija ta rarrashe ta ta juya ta tafi, falo ta koma ta same shi tsaye da alama ita yake jira, makullin motar ya nuna mata yace "Daga yau motar nan ta zama ta duka yan gida, zan samo mu ku dreba da zai dinga kai ku duk in da za ku je, sannan daga yau ban yarda wata ta fita ta bar d'aya ba in dai har fita ce ta dangi na data shafe ni, wannan hukunci na ne."

Zai bud'a k'ofar falon shi dake falon ta ya wuce ta tare gaban shi ta na kallon k'wayar idon shi tace "Abban Bilal wane laifi na yi ma ka? Ka fad'a min dan Allah na baka hak'uri, wallahi tallahi ba zan juri wannan sabon yanayin ba, ka sani kai ma ba zan iya ba ko kad'an."

Lumshe ido ya yi saboda ganin fitowar hawayen ta, amma saboda tasirin sihiri sai kawai ya basar yace "Ba zan d'auki hukuncin da ya dace ba dole sai kin min wani laifi? Ba komai to."

Shigewa ya yi ya barta tsaye, da k'yar ta samu ta shiga d'aki ta cire kayan jikin ta ta wuce madafa, yau girki kala d'aya ta yi saboda yanayin da take ciki.
Chapter 40 · 0% Book details