← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 86

Sashe 52

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta na gama abin karin ta bawa Bilal na su Haseenah ya kai mu su, suma ko da su ka kammala suka fito farfajiyar gida, Bilal na yawo da moton shi a tsakar gidan Khadija zaune da waya ta na tunanin ta kira ko karta kira, ta na haka sai kiran shiya shigo wayar ta, yau ma mamaki ta yi ganin kiran shi, hakan ya sa ta d'auka ta aza a kunne, ba sallama bare gaisawa yace "Na kira Hajia akan maganar tafiyar nan, sai ki shirya da wuri ki same su can gida dan sun ce Naseer ne zai kai su."

"H...hello." Ta fad'a da sauri saboda jin zai katse kiran, cike da k'aguwa yace "Ina ji? Lafiya?"

Cikin fad'uwar gaba tace "Lafiya lau, dama ina son yin magana da kai ne."

"Magana akan me kuma?"

Murya k'asan mak'oshi tace "Nura ne dama ya same ni akan maganar aure da ya ke so, amma yace ka ce ba yanzu ba, shine..."

"Shine za ki sani na yarda na mi shi auren ko me?" Ya fad'a cike gatsali, kamar ta kashe wayar sai kuma ta daure tace "A'a ba haka bane, ya fad'a min ne saboda shi a tunanin shi Khadija tafi k'arfin komai a gurin Abban Bilal, ya zo da buk'atar shine gare ni saboda sanin da ya mana ina iya shawartarka akan al'amura har na cikin gida ma kuma ka yi aiki da ita, ya fad'a min ne ba dan tunanin zan saka ka dole ba, sai dan cewa kamar ina da mahimmanci da kima a wajen ka da zan iya nemawa wani alfarma a wajen ka, sannan ni a gani na ba wani abu bane idan an mi shi auren, matashi kamar Nura ya kalli iyayen shi yace ya na son aure, ina ga a mi shi auren shi yafi kwanciyar hankali."

Har k'asan zuciyar shi maganganunta sun ratsashi, amma saiya dake yace "Me Nura ya sani a game da aure da za ayi mi shi? dan ya na da abinyi ba shi ke nuna zai iya rik'e mace ba."

"Amma ai ko neman auren ya tafi daga cikin tambayoyin da za'a masa akwai son sanin abin da yake, hakan kuma nasara ga d'an uwan mu da ya zamana ya na da aikin yi, ko ba komai zai ciyar da ita, zai shayar da ita da tufatar da ita, sannan ina da yak'inin zai kula da ilimin ta ko wane iri ne, sannan zai iya biya mata buk'atar ta."

Saida taji sautin sauke ajiyar zuciyar shi a kunnenta kafin yace "Bansan me ya fad'a mi ki haka ba da ki ka yarda da shi, gashi har kinsa nima na ji banda wata hujjar hana shi auren, ki fad'a ma sa na amince, amma dole ya jira ni na dawo sai ayi duk wacce za ayi, idan kuma ba zai iya jira ba sai ya turaki ki nemo masa auren."

Ya na fad'a ya kashe wayar, ita kam dad'i ne ya sata bushewa da dariya saboda abin da ya fad'a a k'arshe, wayar Nura ta kira ta fad'a ma sa yanda su ka yi da shi, sosai ya yi murna tare da binta da addu'a Allah ya barta da yayan su, suna gama waya ta ji wayar Bilal na k'ara, hannu ya sa a aljihu ya fito da ita ya d'auka, take ta fahimci Abban shi ne ya kira shi, suna nan zaune Hajia ta shigo gidan da sallama saboda ganin su, da farin ciki Khadija ta mik'e ta tarbe ta tana mata sannu da zuwa su na gaisawa, Bilal ma saida su ka tab'a hira irin ta kaka da jika kafin ta kalli Khadija tace "Ina yer uwar ta ki ta na ciki?"

"Eh Hajia su na ciki."

Nufa b'angaren ta yi ta na fad'in "Bara mu gaisa."

"A fito lafiya." Cewar Khadija, ta na shiga su ka gaisa kafin ta tambaye ta sun ci abinci ai? Eh, shine amsa da su ka bata, kallon Aziza ta yi tace "Ke ki zauna gidan to, ke sai ki tashi mu koma asibitin."

Dama a shirye take, hijabi kawai ta saka suka fito tare da Hajia da ke rik'e da katin likita a hannu, "Hajia har kun fito? Gida za ku tafi ne?"

"A'a." Ta fad'a kai tsaye, ganin Haseenah tare da ita ya bata mamaki, musamman da taga ta na gaba ta na binta, "Hajia lafiya kuwa? Ko ba ta da lafiya ne?"

Sai kawai Hajia ta ji haushin wannan tambayar, bud'ar bakinta cewa ta yi "A'a lafiyar ta k'alau, akwai in da za mu ne."

Da ido kawai ta bisu ta na mamakin kamuwar Hajia ita ma da wannan cuta ta 'ya'yan ta, ido kawai ta zuba mu su har suka dawo lokacin ta na madafa ta na girki, lokacin ne kuma 'yan uwan Haseenah da ma 'yan uwan Usman d'in suka fara zuwa ganin ta, ita dai ta na kammala girki ta fitar mu su ta bayar aka kai, sai dai ta yi niyyar ko ciwon ajali ne Haseenah keyi ba za ta je ta duba ta cikin mutane, tunda ta lura b'oyewa ake ba asa ta sani saboda tunanin wani abu.

Da yamma Haseenah ta karb'i girki, amma 'yan uwan ta ne suka shigar madafar suka yi yanda su ke so, sai dare su ka bar gidan Khadija ta shiga dan samun abin da za su ci, yanda ta ga madafar abin ya bata mamaki da dariya, saida ta gyara ta sosai kafin ta samu abin da za su ci, ko da su ka kammala suka kwanta abin su.

*Hummmmmmmmmm.*

Tunda asuba Khadija ta shirya tare da Bilal suka yi karin kumallo, sai da ta kira Usman tace ta na si ta aje Bilal a gida, amma sai yace "Me ye haka Khadija? Gidan nan fa akwai mutane, ya ki ke so ki nunawa yaron banbanci a zahirance."

"Shikenan ka yi hak'uri." Ta na fad'a ta kashe wayar ita ma, zuwa k'arfe *07:15* suka fito, saida su ka shiga d'akin Haseenah da sallama suna falo ita da Aziza ita ma ta na shiri, "Antashi lafiya?"

"K'alau." Cewar Haseenah, Aziza ce tace "Ina kwana."

"Lau." Cewar Khadija, kallon su ta yi tace "Dama zan tafi Tessaoua ne wajen biki, na kulle d'aki na, ga kayan Bilal idan an dawo da shi sai ya canza wannan, sai na dawo."

Hannun shi ta kama su ka fita, Aziza kam cewa ta yi "Ka ji matar nan sai ka ce akwai bawanta anan d'in."

"Ke kuwa miye a ciki? Bilal ai d'an mu duka, Allah dai ya kaita lafiya."

Saida ta gama shiri suka karya tace"Idan na tafi zan tsaya gida na wuni, na san dai saida dare ko na dawo gida."

Da haka su ka yi sallama ita ma ta tafi makaranta, Khadija ma ko da suka isa Ashir ne ya kai su makarantar duka, su kuma zuwa tara Naseer ya d'auke su suka tunkari *Tessaoua*.

*Me kuma zai faru yanzun?*
16/02/2020 à 13:20 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._

*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

```Fatan alkairi masoya```

_Bismillahir rahamanir rahim_

*27*

Sha biyu Ashir ya d'auko su Bilal, suna hanya Khadija ta kira shi su ka gaisa, gida aka aje shi kafin suka wuce, k'ofa mai gadi ya bud'e masa ya na fad'in "K'aramin Alhaji har an taso?"

"Eh, ya aiki?" Ya fad'a da fara'a, shi ma da fara'a ya mayar masa da "Alhamdulillah."

Ciki ya shiga kai tsaye kuma b'angaren Haseenah ya wuce tunda yau ita ce maman shi, sallama ya dinga rabkawa amma ya ji shiru, saida ya bud'a k'ofar falon ya shiga kad'ai ya ga takalma alamar bak'i amma kuma ba kowa a falon, kujera ya samu ya zauna ya ciro wayar shi ya na dannawa da chocolat a hannu ya na sha, minti talatin ya d'auka a falon sai dariya da shewar su Haseenah ita da Zeinab wacce daga makaranta take ita ma ta ratse nan, tashi ta yi ya nufi d'akin na ta ya k'wank'wasa k'ofa duk da bud'e take, shiru su ka yi kafin tace "Waye?"

A hankali ya yaye labulen ya kalle ta yace "Aunty sannu, ni ne."

Fuska a d'aure tace "To, yaushe ka shigo gidan?"

"Na jima zaune a falo, yanzu ma dan na ce ku bani kaya na ne zan canza wannan."

"Ka je idan na fito zan baka kayan." Ta fad'a ta na mayar da hankalin ta kan Zeinab, har ya juya zai fita tace "Kai zo nan."

Dawowa ya yi jiki a sanyaye ya tsaya gaban ta, kud'i ta mik'o mi shi tace "Ka wuce maza kaje ka siyo min katin waya na airtel."

"To." Ya fad'a ya na karb'ar kud'in ya fice, ta k'aramar k'ofa ya bi zai fice mai gadi yace "K'aramin Alhaji fita za ayi?"

"Eh." Kawai ya fad'a a tak'aice ya na zura duka hannayen shi biyu cikin aljihun doguwar rigar shaddar shi wacce ka na gani kasan ta ji kud'i, a k'afa ya taka har ya iso bakin titi, ya jima tsaye kafin ya samu ya tsallaka saboda akwai ababen hawa sosai a wajen musamman da ya zama ranar farko ta komawa makaranta, siyowa ya yi ya dawo gidan ya kawo mata, falo ya dawo ya zauna amma bai jima ba aka fara kiran sallah, tashi ya yi ya fita a panpo na daf da shigowa gidan ya yi alwala ya tafi masallaci, daya dawo wajen mai gadi ya zauna shi ya na sauraren redio shi kuma ya na kallon hanya, tsawon lokaci ya d'auka nan zaune kafin ya ji cikin shi na neman agaji, cikin gidan ya koma ya samu su Haseenah har yanzu a d'aki amma su na cin soyayyen k'wai da indomie, ga lemu a gefe suna korawa mai sanyi, cikin muryar tausayi yace "Aunty abi..."
Chapter 52 · 0% Book details