← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 86

Sashe 15

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gefen damanta ta lalaba dan d'aukar gilashinta amma sai ta ji ba komai, da sauri ta gyara zama zamanta ta ci gaba da lalabawa kowace kusurwa, Usman da ya gama saka kaya a falo ne ya shigo da niyyar d'aukar sallaya ya fice, ta sauko daga kan gadon kenan dan ta lalaba akan coiffeuse (dressing miror), da sauri ya k'arasa gaban madubin inda ya cire ya aje mata, d'auka ya yi ya mik'o mata yace "Karb'i gashi nan."

Hannu ta zura dan dama ga duhun d'aki ga kuma matsalar idon ta, a k'irjin shi ta d'ora hannu da tunnin ta kai hannunta daidai, rik'e hannunta ya yi ya d'ora mata gilashin ta bud'e shi ta saka, kallon shi ta yi tace "Nagode."

Ba wata fara'a yace "Ba komai, laifi na ne da na mi ki nesa da shi."

Jin kiran sallah ya sa yace "Na tafi masallaci, sai na dawo."

Murya k'asa k'asa yace "A dawo lafiya."

"Allah ya sa." Ya fad'a ya na ficewa daga d'akin, fita ta yi ita ma ta d'auro alwala a tsakar gidan ta dawo ta yi sallah ita ma, ta na kammalawa ta koma d'akin ta d'an gyara in da ta kwanta sannan ta shiga wanka, ta na shigowa falon da d'aurin k'irji da hijab ta samu Usman zaune a falon, sinne kai ta yi ta shige ciki dan ta shirya, doguwar rigar shadda ta saka da d'an kwalinta ta fito da tunanin d'ora mu su abin kari, har k'asa ta durk'usa ba ta had'a ido da shi ba tace "Me za'a dafa?"

Kallon ta ya yi yace "Ina kwana?"

K'ara k'asa da kai ta yi saboda kunya, dan ta san gatse ne ya mata saboda ba ta gaishe shi ba, cikin rawar murya tace "I...na, kwa...na."

Tab'e baki ya yi yace "Ba sai kin damu kan ki ba, yanzun nan za'a aiko da abin karin kumallo wa ke inji Hajia."

"Nagode." Tace ta na mik'ewa ta koma d'aki, ba jimawa Mannir ya kawo mu su abinci, sai da ya gama zubawa in da ya dace ya shiga d'akin ya same ta zaune bakin gado yace "Ki zo ki ci abincin."

Tashi ta yi ta sake d'aukar hijabinta ta fita, a tsakiyar falon ta samu ya aje abincin, juyawa ta yi ta kalli teburin da aka siya mata mai kukera shida, matsawa ta yi ta zaune daga gefen shi yanda basa fuskantar junansu, har ta d'auki cokali ta ji yace "Ki ci da hannu yafi."

Kallon shi ta yi sai kawai ta aje cokalin tasa hannu, haka dukansu suke cin abincin a hankali babu mai magana har Khadija ta cire hannu za ta mik'e yace "Zauna."

Zaunawa ta yi ta na kallon shi da sauraren shi, kallonta ya yi sosai ya matsa kusa da ita ya deb'o lomar abincin da hannun shi ya nufi bakin ta, kawar da kai ta yi tace "Na k'oshi fa."

Wani iska ya fuszar yace "Nana Khadija."

Yanda sunanta ya fita daga bakinshi ya tilasta mata kallon fuskarshi ita ma, da sauri ta d'auke nata idon saboda kallon da ya ke mata, d'orawa ya yi da "Ke amana ce a gare ni, ba zanyi duba da yanda auren mu ya kasance ba, dole na sauke duk wani hakk'in ki da ke kai na, jiya ba ki ci komai ba, yau ma gashi ba kici mai yawa ba, anjima aka fara shagalin damu zai iya saka ki jin jiri, dan haka bud'a bakin ki na ba ki abinci, ba wani abu bane a gare ni, ina da burin bawa duk matar na aura abinci da kai na, kuma ke ce wannan matar."

Sake d'aga ido ta yi ta kalle shi, a hankali ta kai bakinta ga hannunshi da ya mik'o mata abincin, sosai Usman ya dinga d'irka mata abincin nan ta na amsa, ta k'oshi sosai, amma ta kasa fad'a masa saboda yanda fuskar shi ke had'e ko kallonta bayayi, lomar da ya saka mata a baki k'in had'e ta tayi, wata ya d'ibo zai saka mata a baki ta k'i bud'a bakin, d'an k'aramin tsaki yaja yace "Karb'i mana, sai na ga cikin ki ya taso, ko ki na so yan biyar su fara jin haushi na tun ba aje ko ina ba?"

Da k'yar ta tura lomar zuwa mak'ogwaro ta amshi wacce ya mik'o mata, ta na fara taunawa sai kawai ta ji amai ya taho mata, da gudu ta mik'e ta fita farfajiyar gidan ta amaye kaf abincin da ta ci, da sauri Usman ya bi bayanta cike da tausayi, dan tunanin shi ba ta cika cikinta irin haka shi ya sa, ruwa ya bata ta kurkure baki ya na jera mata sannu, da kan shi ya had'a mata ruwan shayi tasha, har zai tattare kwanukan ta tashi ta hana shi da kanta ta d'auke, ganin dai ba wata matsala ya sa ya mata sallama ya fita dga gidan, kamar kuma fitarshi ake jira dama sai ga Kaltume da Barira sun zo, dan mama ce tace su zo kafin rana mutane su zo, tun da ba ta da yer uwa mace da za ta iya zuwa kafin zuwan mutane.

*Yau* ma haka aka yi shagalin damu aka gama, da dare kuma Rahama matar Ashir da *Aisha* matar Bashir su ka mata kwalliya kafin su ka bar gidan, har *11* dare ba Usman ba labarin shi, sai kawai bacci ya suri Khadija ba tare da ta shirya masa ba, ta na nan har sai da ya shigo, yanda ya same ta saita bashi tausayi, mayafin jikin ta ya fara cire mata a hankali kafin ya cire mata takalmin k'afar ta, a hankali ya tallabo k'afafun da nufin d'ora su akan gadon sai ta farka, da k'arfi taja baya ta had'e da gadon har tana neman fad'uwa, yanda ta ke kallonshi a tsora ce ya sa yace "Khadija, tsoro ki ke ji?"

Girgiza kai ta yi alamar a'a, tab'e baki ya yi yace "Shikenan, ki tashi ki cire kayan jikin ki sai ki zo ki kwanta."

Ganin ya juya zai fita ya sa tace "Kai fa?"

Juyowa ya yi yace "Ni fa me?"

"Ina nufin ina za ka kwanta kai?"

Murmushin mugunta ya saki ya kalli gefen ta yace "Anan mana, ko ki na so na sake kwana a falo ne?"

Shiru ta yi ba za iya cewa eh ba, saboda kar ya ji ba dad'i, kayan bacci ya d'auka ya fita falo dan canzawa, ita kuma k'in sauya kayan ta yi har ya sake samunta a haka, kashe wutar d'akin ya yi ya kwanta gefe ya na satar kallon ta, ba ta kwanta ba sai ma k'ara rakub'ewa da ta ke, kallonta ya yi yace "Ki kwanta Khadija, daga ni sai ke ne fa a gidan nan, kuma a cikin d'akin da babu wanda zai iya taimakonki, idan na so ai zan iya yin komai a d'an k'ank'anin lokaci, amma ba yanzu ba kinji, ki kwanta ki yi bacci kawai."

Ya na fad'a ya juya mata baya ya na ci gaba da murmushin gefen labb'a, bacci ne kad'ai ya fizgi Khadija yasa ta kwanta ba tare da ta sani ba, sai dai baccin bai je ko ina ba Usmn ya tashe ta yin sallah.

Ko da ta yi sallah ya fita a runfar nan ta samu akwai kayan abinci sosai, sassauk'an girki ta yi har ta gama bai shigo ba, akan teburi ta aje ta shiga wanka, ta na fitowa yau ma kamar jiya zaune ta same shi, d'aki ta wuce ta shirya cikin riga da siket na shadda sun mata kyau, ta gama shafe jikinta da turare za ta fito Usman ya shigo, cak ta tsaya dan ya tare k'ofar fitar, k'asa take kallo shi kuma ya na kallon fuskarta, kamar daga sama ta ji yace "Ki je ki yi kwalliya, ko da ba kya ra'ayinta ni ina so."

Galala ta bishi da kallo kafin ta zauna gaban madubi, da k'yar ta iya shafa hoda (powder) da d'an jan baki ta tashi ta bar d'akin, ta na zaune akan kujera taga fitowar shi, da sauri ta mik'e ta fara zuba abincin a k'aramin farantin da zai wadaci mutum d'aya, zan kujera ya yi ya zauna ya na kallon ta har ta gama zuba mi shi, wani farantin ta d'auka za ta zubawa kan ta yace "Ba buk'atar ki zuba na ki, mu fara cinye wannan."

Ta gilashi ta d'aga manyan idon ta ta kalle shi ta buntsuro faffad'an labb'an ta, zaunawa ta yi ta d'auko cokali za ta saka yace "Na fad'a mi ki ai, ba na cin abinci da cokali, zan so ki saba da hakan, dan ci da hannu ma sunna ce."

Mayarwa ta yi ta aje ta na kallon k'asa, hannu ya sa ya fara ci tare da bismillah ya kalle ta yace "Sa hannun ki mana."

Kamar wacce zai cinye haka ta saka hannu ta na tsakuro abincin tana sakawa a baki, ganin haka ya sa yace "Ki na so sai na baki da kai na kenan?"

"A'a." Ta fad'a da sauri ta na kai wata lomar bakin ta, d'an gyaran murya ya yi ya cire hannun shi ya na kallon ta yace "Nana Khadijatul Kubra."

Kallon shi ta yi jin wani cikakken suna da ya kira ta da shi, a hankali tace "Na'am."
Chapter 15 · 0% Book details