← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 86

Sashe 7

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran Usman ne ya katse ta, ta na d'auka tace k'awayen ta su fito a mayar da su gida, nan su ka tashi su na tsokanar ta wai za su zo cin kaza da sassafe, ita kuma ta na dariya ta na fad'in ba zai yiwu ba ita da shan wahala su da cin kaza, haka su ka bar ta wasu na ganin kamar ta na son yin kuskure na gani-ganin da take wa Khadija, haka dai gida ya yi shiru ba kowa, ango kuma bai shigo ba sai da dare ya raba sosai, lokacin Khadija ta yi shirin kwanciyar ta ta na kwance a d'akin Bilal da shima ya jima da yin bacci, d'akin ta ya fara shiga bai same ta dan haka ya wuce d'akin Bilal, ta na jin shigowar shi ta rufe ido kamar mai bacci, tashin ta ya yi amma ta nuna kawai ta yi nisa a baccin ta, sai da ya tallabo ta ya kalli idon ta yace "Ki tashi mana ki kalle ni."

Ido rufe tace "To me zan maka? Amarya ce da kai fa."

Sake komawa ta yi ta kwanta, ledojin hannun shi ya kalla yace "To tashi ki d'au leda d'aya anan?"

Juyowa ta yi ta kalleshi duk da dai ba ganin shi ta yi da kyau ba haka tace "Tun fa a gidan mu ina ganin bak'ar leda, kuma nasan kaza ce a cikin ta, kuma ba na sha'awar cin ta, dan haka ko dai ka tafi da ita can za ku fini buk'atar ta, ko kuma ka aje watak'ila idan d'an ka ya tashi da safe ya ci kazar siyar bakin kishiyar mahaifiyar..."

Da sauri ya daka mata tsawa ta hanyar fad'in "Kar ki soma Khadija, wallahi kar ki fara sakawa yaro na banbanci a cikin k'wak'walwar shi tun yanzu, sam ba zan lamunci wannan ba, ke da Haseenah yanzu duk d'aya ku ke a gurin shi."

Juyawa ta yi ta d'auki gilashin ta ta mak'ala ta na murmushi tace "Tun yanzu Abban Bilal? Yaushe rabon da ka d'aga min murya irin haka? Sai yau? Saboda ka yi amarya? Yayi kyau, amma bari ka ji nima na fad'a ma ka, Bilal yaro na ne ban da wata banzar mace da ta shigo gidan nan yau, idan kai ka shirya sadaukar mata da yaron na ka, sai ka bari har a wayi gari, a lokacin ta san komai a kan ka, ma'ana ta gan ka daga ka isai fatar jikin ka, to a lokacin sai na yarda, idan ka fita ka rufe mana d'akin."

Gilashin ta ta cire ta aje ta yi wanciyar ta ta rufe har fuskar ta, da k'yar ya aje d'aya ledar ya fara taka k'afafun shi ya fice daga d'akin, har k'asan zuciyar shi yana jin ba dad'i, kuma ba ya fatan auren shi da Haseenah ya zama silar fara rubuta matsala a tarihin zaman shi da ita, dan Khadija ita ce farin cikin shi, haka ya sallama d'akin amarya ya same ta, da k'yar ya tattara nutsuwar sa ganin Haseenah na neman fahimtar halin da ya ke ciki, ita kuma dad'i ne ya kusa kashe ta saboda ganin halin da ya ke ciki, sun gabatar da duk abin da shari'a ta zo da shi amarya da ango suyi sunyi, bayan nan kuma su ka kwanta dan sauke gajiya, bai yarda ya yi nesa da ita, sai dai tabbas akwai wani bak'on al'amari, in dai har ya na gari bai tab'a raba shinfid'a da Khadija ba ko da kuwa sun samu sab'ani ne a matsayin su na yan adam, dan ko haihuwar Bilal ba su raba shinfid'a ba, haka mai tsohuwar da ta zo ta ke ganin rashin kunyar ta, haka dai ya rumgume ta har bacci ya d'auke shi.

Kiran sallah farko Khadija ta tashi tare da Bilal dan gabatar da sallah, d'akin ta ta koma ta na shirin kabbarawa Usman ya shigo dan ya duba d'akin Bilal bai ganta ba, ba tare da ta had'a ido da shi ba tace "Ina kwana."

Marairaicewa ya yi yace "Ina aka baro sauran mahad'in da ake had'a min da shi?"

"Ban gane ba?" Ta fad'a ta na gyara hijab d'in ta, kallon ta ya yi yace "Kamar Abban Bilal, babban mutum, rabin rai, sarki, jarumin ki, da dai sauran su."

D'agowa ta yi ta kalle shi da murmushi tace "Ina kwana jarumin namiji."

Ta na fad'a ta kabbara sallahar ta, fita ya yi cikin rashin jin dad'i ya nufi masallaci, Khadija na gama sallah da azkar d'in ta kwace ta koma ta yi dan bacci ta ke ji wanda ba ta yi ba, sai da gari ya waye Bilal su ka dawo tare da baban shi, d'akin amarya ya fara wucewa tun da ba ta san tsarin gidan na su ba, kwance ya same ta a kan sallaya ta na bacci, a hankali ya juya ya fita ya koma d'akin *Dije*, ita ma kwancen ya same ta ta na bacci, k'arfin hali ya yi ya tashe ta, ta na bud'a ido ta ya sakar mata murmushi yace "Ammien Bilal, ashe bacci ki ke? Na d'auka ki na madafa ai."

Sai da ta d'auki gilashin ta kafin tace "Yin me a madafa?"

Cikin murmushi yace "Yin girki mana, ko ba za ki mana abin karin kummalo ba? Kinsan fa bak'uwa ce da mu a gidan, watak'ila ita ta na karyawa da wuri ba kamar mu ba."

Gyara zama ta yi tace "Sai kuma aka ce wannan ya zama matsala ta? Me ka ke so na yi? Na je na dafa mata abinci kenan ta ci? To ka yi hak'uri, ban da ra'ayin shiga madafa yau."

Ta na fad'a ta tashi ta shiga ban d'aki, wanka ta yi dan baccin ma ya fita idon ta, Usman kam na fita ya wuce d'akin Haseenah ya d'auko makullin mota dan ya siyo abinci, a farfajiyar gida ya samu mai gadi ya bud'ewa k'anin shi k'ofa ya shigo, musabaha su ka yi kafin k'anin yace "Ango abinci fa Hajia ta ce na kawo mu ku."

"Da gaske *Nura*? Kai amma Hajia ta kyauta wallahi, dan dama duka mutanen gidan a gajiye su ke."

Dariya Nura ya yi yace "Lallai kam, to ko dai za ka d'auke ni ina dafa mu ku abinci har lokacin da za ku huta?"

Hannu ya sa ya karb'i kwanukan ya na fad'in "Dallah ni bani nan ba na son shiririta."

Mik'a mi shi ya yi yace "Dama ba na son shiga ciki saboda ban sanyo manyan kaya ba, kasan halin Dijen nan da son girma."

Kai ya girgiza yace "Allah ya shirya da wannan son girman na ka, wai matar da ta zo gidan nan ka nada shekara biyar a duniya, tun fa ka na yawo ba wando ta ke tare da kai, amma yanzu har ka ke son bud'e mata ido."

"Ni fa matsala ta da kai kenan, yanzu dai sai anjima, sai na zo cin tuwon amarya."

Wucewa kawai ya yi ya shige ciki, ya na shiga a teburin cin abinci ya aje ya d'auko farantai ya jera sannan ya shiga ya taso Haseenah, tare su ka fito ta na sake k'arewa falon na shi kallo, ganin za su wuce teburin abincin ya sa ta tsaya ta na kallon shi, juyowa ya yi shi ma yace "Muje mana."

Binshi ta yi su ka wuce, k'ofar falon Khadija ya bud'a ta shiga, saboda yawan turaren da akewa d'akin ya sa har ya kama d'akin sosai, a hankali Haseenah ta lumshe ido ta bud'e kai tsaye, rarraba ido ta fara ta na kallon ikon Allah, wai, masha Allah, tabbas ba k'arya falon ya had'u kuma ya tsaru sannan ya ga kaya, ba had'i kam nata falon da wannan falon, ta na ganin kyawun falon Usman, amma sai ta ga ashe na shi ma somin tab'i ne, takawa ta fara yi ta ji k'afafun ta ta lumewa cikin shinfid'add'en tappi da ke kai, ta na kallo ya k'wank'wasa k'ofar d'akin tun da ba shi kad'ai bane, amma a wajen Haseenah kawai mulkin da Khadija ke yi a gidan ne ya sa ba ya iya shiga d'akin sai ya nemi izinin ta, jin shiru ya sa ya bud'a a hankali ya lek'a, ganin ta ya yi zaune bakin madubi ta na shafa hoda (powder), "Mu shigo?"

Shine abin da ya fad'a, ta na jin haka ta san ba shi kad'ai bane, dan haka ma ta saki murmushi tace "Ku shigo mana."

K'arasa shiga su ka yi Haseenah na d'ard'ar da satar kallon d'akin, ko dan na ta d'akin sabbin kaya ne a ciki sai warin sabintaka su ke, hakan ya sa taji kamar ta yi kwance a d'akin Khadija, zaune ta yi kujerar da ke gefen kwabar saka kaya (wadrob) kanta k'asa, shi kuma tsaye ya yi gaban Khadija yace "Wannan kwalliya haka matar, wa ake ma ne?"

Tsaye ta mik'e ta na gyara d'an kwalin ta ta juyo ta kalli Haseenah da fara'a tace "Amarya ke da kan ki?"

Ita ma murmushin ta yi tace "Ina kwana?"

"Lafiya lau amarya, kin tashi lafiya?"

"Lafiya lau." Ta fad'a a tak'aice, da murmushi Khadija ta d'ora da "Ya kwanan bak'unta kuma? In ce dai kinyi bacci?"

A birkice Haseenah ta kalli maganar Khadija, hakanne ya sa ta d'an d'ago ta kalle ta ido tsaye tace "Ai Abban Bilal bai barni na yi bacci ba, kin san shi da rigima."

Kallon ta Khadija ta yi ta na wani murmushi irin na babba da yaro tace "Ke ma kenan da ki ka zo jiya, yanzu na san za ki fahimci k'ok'ari na akan mijin ki."

Haseenah kam a zuciyar ta tsaki ta yi, Usman ne yace "To na ji, yanzu dai ai nine rigimammen ko? To nagode, yanzu ku wuce muje mu ci abinci."

Cikin zolaya Khadija tace "Wai har ka gama girkin? Amma gaskiya ka yi sauri."

Hararan wasa ya aika mata yace "Kin d'auka ke kad'ai ce gwana a fannin girki? To ni har lambar yabo aka ban, nuna miki ne ban yi ba saboda tsaro."

Dariya ta yi tace "Ko dai saboda tsoron girki ba."

Takawa ta fara yi tace "Muje to."
Chapter 7 · 0% Book details