← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 86

Sashe 37

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ido kawai ta bisu ba tace k'ala ba, saida su ka fita ta gyara zaman ta, su kuma sun jima bakin k'ofa su na bubbugawa tare da sallama amma shiru, da k'yar Haseenah ta fito cikin riga da wando ta bud'e, saida ta saki wani d'an k'aramin tsaki saboda ganin su, washe baki ta yi ta na fad'in "A'a'a'a, su Aziza ne a gidan mu? Sannun ku da zuwa, ku shigo mana, ashe ku ne ke ta bubbugawa, ina wanka wallahi."

Duk ta yi maganar ne lokacin da suke shiga ciki, zaune su ka yi ita ta wuce ciki, da kallo su ka bita kafin su mayar da kallon su kan telebijin, Usman ta samu kwance akan gadon ta kamar mai son yin bacci, da k'yar ta samu ta rabu da shi ta sanyo hijabi ta fito, nan fa su ka shiga hira dan dama Usman yace kar ta gajiyar masa da kan ta za su fita cin abinci tare, dan haka ba ta damu ba har Aziza ta d'an kalle ta dan ita dama madafar ta ke son shiga, cikin taushin murya tace "Auntyn mu yunwa fa na ke d'an ji."

Hararan gefen wutsiyar ido ta wa Aziza amma a zahiri ta yi dariya tace "Ki ke d'an ji ko ki ke ji?"

Dariya su ka yi tace "To na ke ji, akwai indomie?"

"Kinsan ai ba za'a rasa ba, bara na d'ora mu ku" Ta fad'a cike da k'arfin hali, Aziza ce tace "Ah haba dai amaryar mu, ina mu ina saka ki aiki, yayan mu fa na d'aki, dan haka ki bar mana komai ni zan shiga da kai na, ko kin manta gidan nan ba bak'o na bane."

Cikin dariya Haseenah tace "Na sani kam, ai yanzu ma ina jiran ranar da za ki sake kawo mana ziyara ne."

"Zan zo, amma sai an koma makaranta (school) dan yafi dad'i, saboda yafi kusa kuma nafi jin dad'in zama a lokacin."

K'awar ta ta kalla tace "Ina zuwa *ma chérie.*"

Wucewa ta yi Haseenah ma ta shiga ciki dan ganin mijin ta, Aziza na shiga kai tsaye wata yar drower ta bud'a, cikin sa'a kam ta lalabo abin da ta ke nema, murmushi ta yi tace "Yawwa, na samo shi." Ta na fad'a ta saka a k'asan siket d'in ta kafin ta fara had'a indomie, cikin k'ank'anin lokaci ta gama ta fito da ita a cikin faranti, su Haseenah na zaune ta aje tace "To to bismillah, ba zan jira kowa ba fa."

Haseenah kallon indomien ta yi sosai yawunta ya tsinke, sai dai kuma a k'oshe take bare ta ci, sai dai ta na mamakin yanda suke dafa indomie haka gwanin kyau da dad'i, ga dukkan alama ma Azizar ta koya ne a wajen Khadija tunda kamar babbar yar ta ce a yanda ta samu labari, ba ta ci ba sai kallon su da take su na hira har su ka kammala, sun tashi tafiya ta shiga ciki ta d'auko kud'i sosai ta basu su hau adaidaita, haka su ka fita cikin jin dad'i da kuma samun nasara wajen Aziza, ko takan Khadija ba su bi ba bare su mata sallama, su na shiga adaidaita aka fara aje k'awar Aziza, daga nan ita kuma gidan Hassana ta wuce, ta na zuwa ba ta yi k'asa a gwiwa ba wajen bata wannan abun, saida ta k'are ma sa kallo sosai ta kalli Aziza jiki a sanyaye tace "Aziza kinsan me ye wannan?"

Kai ta girgiza tace "A'a, amma dai shine ta ke zubawa a shayi, wani lokacin ta daka wani lokacin kuma ta saka a haka."

Tsakin jin haushi Hassana ta yi tace "Wannan fa minana ce, k'wallon ta ne wannan kafin a daka ta zama gari."

"To miye shi d'in?" Cewar Aziza, cikin jin haushi tace "Ana had'a maganin mata da shi, watak'ila akwai wani anfani da ya ke da a jikin namiji ne da ya sa take sakawa."

*Hotiho, ki koma makarantar mata*

Dafe kai ta yi tace "Me ya sa ma banyi tunanin haka ba? Tun farko ya kamata musan ba za ta tab'a aje wani abu muhimmi a madafa ba, bugi da k'ari ita fa k'awar Kaltume ce."

Cikin rashin jin dad'i Aziza ta baro gidan ta koma gida, ta na zuwa gida ta samu malam ba ya jin dad'i zazzab'i mai tsanani, ya sha magani amma har yanzu rawar d'ari ya ke, hakan ya sa aka kira Usman da a lokacin ya ke gida tare da amarsu, cikin gaggawa ya canza kaya ya fita zuwa gidan, ya na zuwa kuma asibiti su ka nufa da shi aka ba shi agajin gaggawa, an bashi taimakon amma kuma ya na buk'atar jini, nan fa yaran su ka shiga layi dan a gwada nasu a k'ara ma sa, gwajin farko aka gane na Usman ya dace da na shi, ba'a b'ata lokaci ba aka kwasa aka k'arawa malam, sun jima a asibitin su na kai da kawowa har dare ya yi sosai.

Ya na zuwa kai tsaye d'akin shi ya wuce, a can Haseenah ta same shi har ya shiga wanka, shiga ta yi su ka yi wankan har su ka fita, cikin shagwab'a ta kalle shi tace "Ni fa yunwa na ke ji."

Kallon ta ya yi sosai, ya na ji kamar ya tuhume ta akan rashin tambayar shi lafiyar mahaifin shi, amma kuma sai ya share yace "Ki yi hak'uri, me ki ke so ki ci yanzu?"

Cikin tiro baki tace "Abu mai dad'i na ke so."

"Kamar me?" Ya sake fad'a ya na d'aukar wayar shi a gaban madubi, "Koma meye." A cewar ta ita ma.

Waya ya yi Bilyamin ya sa ya kawo mi shi duk abun buk'ata, har ya gama shiryawa ita ma haka, suna zaune ya ji ya gagara samun nutsuwa saida yace "Ba ki tambayi jikin Baba ba, kamar abun bai dame ki ba, har da jini fa aka k'ara ma sa, kuma nawa aka d'iba." Ya k'arasa da nuna mata hannun shi da aka d'ibi jinin.

Kallon shi ta yi cikin rashin jin dad'i take ta k'ak'aro hawayen k'arya tace "A ganin ka ban damu da ku bane ko me? Kasan halin da na shiga saboda rashin dawowar ka da wuri? Duk da ana fad'a min wayata babu kud'i amma bai hana ni kiran lambar ka ba saboda tunanin ko za su duba girma da soyayyar da na ke ma ka su aika kira na a wayar ka, amma a haka ka ke cewa ban damu ba? Lallai ma."

Mik'ewa ta yi irin ta yi hushin nan za ta fice, Usman kam sai ya ji kamar ta na zuba ma sa ruwan zafi wannan kukan da take, da sauri ya rik'o ta ta fad'o kan sa ya shiga rarrashi, da k'yar ta yi shiru tace ya wuce, lokacin kuma Bilyamin ya kawo mu su abinci, da kan shi ya fita ya amso tare da bashi kud'i yace ya rik'e canjin, dawowa ya yi ya kawo mata amma kafin ta zuba yace "Bara na shiga na ga yarima, nasan yanzu dai ya yi bacci."

"Amma fa idan ka jima ba zan jira ka ba." Ta fad'a ta na nufa kan teburi ta d'auko faranti, baice komai ba ya fice, ai kuwa a falo ya samu Khadija ita kad'ai zaune, idon ta akan telebijin amma da gani kasan hankalin ta ba nan ya ke ba, da sauri ta zabura ta sauke idon ta akan shi, shi ma ita ya ke kallo amma da wani irin yanayi na tsana da haushi, mik'ewa ta yi ta nufe shi da k'arfi ta fad'a kan jikin shi ta sauke ajiyar zuciya ta na sake rumgume shi sosai, cikin muryar kuka ta furta "Na yi kewar ka Abban Bilal."

A hankali cikin dubara ya raba ta da jikin shi ya na d'an k'aramin tsaki ya kalne ta yace "Me ye na kuka kuma?"

Kamar wacce ya mara sai ta sake fashewa da kuka saboda bak'in cikin da ke zuciyar ta, sunkuyar da kai ta yi k'asa ta na jiran ta ji ya janyo ta jikin shi ya gara rarrashi kamar yanda ya ke, amma sab'anin haka sai cewa ya yi "Wai me ye na kukan dan Allah yanzu cikin daren nan? Wani abu aka mi ki?"

Girgiza kai ta yi cike da mamaki ta na kallon shi, cikin jin haushi ya d'ora da "Shine kuma za ki tasani gaba ki na kuka, ba na son koke-koken nan ni wallahi, haka kawai da girman ki da komai ki tsaya ki na kuka, ke ba duka ba, ba zagi ba, salon jawa mutane magana."

Wani tsaki ya kuma yi kafin yace "Ina Bilal ya ke?"

Khadija da bakin ta ke bud'e kamar k'adangare zai shiga ciki ta nuna mi shi k'ofar d'akin Bilal, cikin hararen ta yace "Ya yi bacci ne?"

Saida ta zura hannu ta cikin gilashin ta ta share hawaye tace "Eh."

Juyawa ya yi rai b'ace yace "Saida safe."

Har ya bud'e k'ofar kuma ya tsaya yace "Baba ba shi da lafiya ya na asibiti,ku yi k'ok'ari da safe ku je ku ga jikin shi."

Fuskar ta kad'ai ta nuna mi shi damuwar da ta shiga a lokacin, saida ta matsa kusan shi tace "Me ya samu Baba? Ya jikin na shi yanzu? Ina fata fai da sauk'i?"

Sharewa kawai ya yi yace "Da sauk'i." Kamar ansa shi dole, zai fita ta sake cewa "Ka tabbatar ya na lafiya? Gaba d'aya ba na jin dad'in jiki na."

Sama da k'asa kawai ya kalle ta ya wuce abin shi, daskarewa ta yi a wajen ta na tunanin abin da ke shirin faruwa da su koma ya faru d'in, ta jima tsaye kafin ta kashe wuta ta wuce d'akin ta, alwala kawai ta d'oro ta zo ta kabbara sallah, tun daga nan ta fara kaiwa Allah kukan ta tana neman agaji da mafita, sai kusan *uku* na dare bacci ya d'auke ta, kuma ana kiran sallah ta farka ta taje ta tashi Bilal shim, Usman da kan shi ya zo ya tafi da shi suka shiga masallaci.
Chapter 37 · 0% Book details