← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 86

Sashe 32

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya mata yace "Ko ban tambaya ba nasan za ki fara shirya min kan ki ne, dan haka kin samu izini na, sannan..." Ya fad'a ya na saka hannu aljihu ya ciro kud'i, mik'a mata ya yi yace "Ga wannan ko, sai a k'ara ayi kwalliya da kyau."

Sunkuyar da kai ta yi ta rufe ido da hannayen ta, sunkuyowa ya yi ya lek'a fuskar ta yace "Iyeee! Kunya ce wannan? Kin tuna amarcin kenan? To shikenan bara ki gani."

Tsakiyar maman ta ya tusa mata kud'in tare da sumbatar goshin ta yace "Ni na tafi sai na dawo."

Sai da ya ksa kaiwa ga k'ofar fita ta d'ago tace "A dawo lafiya, godiyar kuma na mik'o ta zuwa wani lokacin." Yanda ta k'arashe maganar da fari ya sa ya saki murmushi yace "Ina jira, dan nasan abun zai k'ayatar tunda ke ce za ki yi shi."

Ya na fita ta tashi ta k'arasa shirin ta, tare da Uwani su ka tafi a motar ta gidan kitso da lalle da ma sauran gyaran jiki, kasancewar babu mutane a wurin ya sa aka fara mata abin da ya kai ta, sun jima sosai a wajen, dan sai kusan k'arfe biyar na yamma su ka koma gida ita da Uwani, tun a hanya ta tsaya ta siye salade dan ta ci, su na zuwa gida Uwani ta shiga gyaren shi ita kuma ta shiga wanka, ko da ta gama shiri Uwani har ta fara yankawa, zaune ta yi su na hira su na aiki har magriba, kuma har lokacin ba ta ga Haseenah sai motsin ta da su ke ji a madafa, a haka duka suka gama aiyukan gaban su suka koma d'aki.

Tunda wuri ta yi shirin baccin ta yau saboda ta huta dan gobe ita ce da aiki, doguwar rigar bacci ce a jikin ta da ta sauka har k'asa haka ma hannayen rigar, sanin Usman zai shigo ya sa ta k'i saka komai daga cikin rigar, ma'ana dai babu komai daga ciki bayan rigar, ai kam ta na jin motsin shi ta yi sauri ta mik'e ta fara kai da kawon iska, ya na bud'a k'ofar da sallama a bakin shi, da sauri ya d'ora da "Wai wai wai, kar dai na shigo lokacin da bai dace ba?"

Juyowa ta yi da murmushi tace "Wane lokaci ne bai dace Abban Bilal ya ga Umman Bilal ba?"

Takowa ya yi zuwa gaban ta ya na kallon ta yace "Ba na tunanin akwai lokacin gaskiya."

"Kuma ka fad'a?" Ta fad'a da kafe shi da ido.

Hannu ya kai zai kamo ta ta janye ta zauna kan gado ta na fad'in "Dama ina son magana da kai."

Zaunawa ya yi ya na fad'in "Uhum, akan me?"

Satar kallon shi ta yi tace "Akan maganar kwana ne dama."

Da sauri ya kalle ta yace "Me ya faru da kwanan ki? Ina ce gobe ne ko?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace " Eh gobe ne, amma kuma da matsala."

Gyara zama ya yi ya na kallon ta yace "Matsalar me? Ki yi magana mana dan kinsa hankali na ya fara tashi."

Mik'ewa ta yi tsaye kamar marar gaskiya ta na kallon shi ta na wasa da yatsunta tace "Eh to, gaskiya dai ba na sallah, shi ya sa na barwa amarya kwanan na wa."

"Me?" Ya fad'a ya na tashi tsaye, janyo ta ya yi jikin shi yace "In dai ba b'ata na yi ba ai tunani na lokacin zuwan bak'on ki baiyi ba, me zai sa ya canza lokacin zuwa yanzun? Saboda ya san ina buk'atar ki ne a kusa da ni kome? Ko shi ma haushi na ya ke ji ya na taya ki kishi ne?"

Da sauri ta janye daga jikin shi ta yi baya ta na fad'in "A'a ba ko d'aya, gaskiya na ke fad'a ma ka fa, ka yarda mana."

Had'e fuska ya yi yace "Naga tafin hannun ki."

Da sauri ta mayar da hannayen baya tace "Um um."

Murmushi ya yi yace "Wata kala ce kawai ki ke so ki min kuma na gano ki, dan haka ki ci gaba da min shirye shirye kawai."

Juyawa ta yi ta nufi ban d'aki ta na fad'in "Ni fai na fad'a ma ka na barwa amarya kai, dan yanzu har na saba da bacci ni kad'ai."

Har da gudu ya had'a wajen janyo ta jikin shi ya na shafa ta ya na fad'in "Kenan ba ki yi kewata ba ko kad'an?"

Cikin narkakkun idon ta ta kalle shi ta gilashi tace "Idan ma na yi ko banyi ba, idan ka shigo hannu na za sani."

A hankali ya matso kan shi ya na son had'e bakin su da sauri ta fizge daga gare shi, juyawa ta yi ta nufi ban d'aki ta na juya mazaunai da gayya, lumshe ido ya yi ya d'an cije lab'en k'asa ya bita da kallo, ta na shigewa ya matsa bakin k'ofar yace "Ni zan wuce sai da safe, ki kula min da kan ki dan Allah."

Shiru ta yi har ya fice daga d'akin, ta na jin ya fita ta fito dan dama ba komai ta ke yi ba, kashe wuta ta yi ta zauna bakin gadon ta yi addu'o'in da ta saba yi kafin ta cire gilashin ta ta kwanta abin ta.

**************

Bilal na zaune tare da duka iyayen shi yan uwan mahaifiyar shi da kuma kakar shi, dan har yanzu ba su daina had'uwa a falon mahaifiyar su ba suna hira, hira ce ta yi hira har ta sa Bilal fad'a mu su fad'an da mahaifiyar shi ta yi da kuma auntyn shi, rashin jin dad'in abun ya sa Naseer cewa "Ni wallahi dama nasan sai anyi haka, dan tun ranar da suka samu sab'anin nan nasan yarinyar nan ba ta da kunya, in ba rainin hankali ba taya za ki bud'e baki ki ce wai ina anfanin yaro a cikin gidan uban sa? Wallahi ta yi wasa ni sai na ci uban wanda ya d'aure mata gindi ma."

Mama ce ta katse shi da cewa "Kamar ya ka ci uban ta? Matar mutane za ka daka har gidan ta? To ba na son sake ji daga yau, ku na so ace ku na taya 'yer uwar ku kishi ne?"

Naseer d'in ne dai ya d'ora da "Hajia ba ki san me ta ke mata bane, ranar fa har kuka ta saka ta da hawaye, ce mata ta yi wai makauniya, ki ji fa Hajia, ni tunda na ke ban tab'a jin wanda ya kira ta da makauniya ba."

Ashir ne yace "Makauniya fa? Khadijar ce makauniya?"

"Wallahi haka ta fad'a mata shegiyar figaggiya."

Habeeb da Bilal ke kwance kan k'afafun shi ne yace "Wallahi ni tun ran kan amarya da na ga idon yarinyar nan a tsaye da kuma k'awayen ta masu ido tsakar ka nasan dama za ayi haka, amma dai ta kiyaye b'atawa auta rai, dan ba lallai mu d'auka ba."

Bashi ne ya karb'e da "Ba maganar ba lallai bane, magana ce ta ba zamu d'auka ba ko kad'an, wallahi ba za ta shiga gidan ta ba kuma ta nemi ta raina ta, dan haka dole Usman ya sake zagewa wajen tsayawa akan gidan shi, in ba haka ba kuma to zamu ziga ta ta dinga jibgar ta mu kuma a shirye mu ke da mu tsaya mata a kowace kotun duniya."

Tsaki Mama ta yi ta mik'e ta nufi d'akin ta ta na fad'in "Saida safen ku, tunda naga dukan ku babu mai hankalin da zaiyi magana ta hankali har kai da ke babba a ciki."

Nan ta bar su suka ci gaba da tattaunawa akan al'amarin gidan da kuma 'yer uwar su, bacci Bilal ya yi Habeeb ya kwantar da shi kafin suma su ka nufi wajen na su matan tare da tattara k'ananan yaran su da su ke tare da su anan.

*****************

Washe gari ma Haseenah ce ta shirya abin karin kummalo, Usman da kan shi ya zo ya kira ta dan su ci tare amma tace wallahi ba za ta je ba, tunda dai har ta nuna abata kwanaki ita ma ta ci amarcin ta to ta bata, su biyu kad'ai su ka karya haka da rana ma da ta gama girkin aikowa ya yi aka d'aukar ma sa, tun k'arfe uku na rana Khadija ta shiga madafa ita da Uwani da wasu matasan 'yan mata biyu yaran mak'wabtan su, hakan ya sa gidan ya kaure kamar su na aikin wata hidima, kowa da abin da ya ke yi, Haseenah na iya hangen su ta k'ofa sai tsaki take da hararn su, cikin hukuncin ubangiji sai gashi zuwa k'arfe shida sun kammala komai sun gyara wurin kamar ba su yi aiki ba, a falon shi ma gyara su ka shiga yi in da Khadija ta sa suka gyara zaman komai da ke d'akin zuwa wata kusurwar ta daban, amma uwar d'akin shi da kan ta ta shiga ta yi gyaran, koda aka fara kiran sallah tuni har sun kammala musamman da ya zama akwai masu kamawa, ko da su ka yi sallah duka yaran abinci ta zuba mu su suka ci su ka k'oshi, sannan ta had'a su da kyautar turare wai su shafa tunda yan mata ne, har Uwani ma ba ta bari ba sai da ta mata, haka yaran su ka tafi bayan ta had'a su da jikka jikka, hakan ya sa duk abin da suke in dai ta tura a kira su to ko ba su yi niyyar tahowa ba iyayen za su ce su zo, saboda irin alherin da ta ke mu su, su na tafiya ta shiga uwar d'akin ta ita ma ta d'auko wasu robobi da blanda (blander) ta zauna gaban frigo (fridge).
Chapter 32 · 0% Book details