← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 86

Sashe 24

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D'orawa ya yi da "Khadija dai matata ce tsawon shekara goma sha uku, shekara sha uku ba kwana goma sha uku bane Haseenah, kinga kenan k'arshen sanin juna munyiwa kan mu shi ni da ita, a wannan shekarun da mu ka d'auka Haseenah, wallahi, wallahi na rantse mi ki da Allah ba zan iya tuna ranar da zan ce mi ki wannan baiwar Allahr ta min ko da kallon raini ne bare tsaki ko bak'ar magana, Haseenah, kin ganta nan ki tambaye ta kiji yanda auren mu ya kasance, amma sau d'aya ba ta tab'a nuna min k'iyayya ko tsana ba, idan har na ce eh, to eh ne a wurin ta ko da a'a ne, idan na ce a'a haka ita ma za tace a'a, a iya zama na da ita ban tab'a ji ko a labarin ta ba cewa ta na da abokin fad'a ba, d'azu ma na tambayi me ya faru ne saboda shine adalcin da zan iya yi, amma a gaskiya ni nasan Khadija ba ta da tashin hankali ko kad'an, dan haka Haseenah ki kiyaye dan Allah, Khadija dai ita ce gaba da ke a shekaru da ma zuwa gidan nan, kuma nasan kinsan karin maganan da ake cewa *duk wanda ya rigaka bacci dole zai rigaka tashi*, ba na so ki sawa zuciyarki irin tunanin matan yanzu cewa, wai ko shekara d'ari ka samu mata a gidan mijin ta, to wata na shigowa gidan kuma tasan mijin sun zama d'aya, eh tabbas dukan ku matana ne kuma d'aya ku ke, amma ki sani Khadija ta riga kwana a gidan nan har da ma tashi, duk da Allah bai bamu 'ya'ya dayawa ba, amma dai ita ce uwar d'an da ni a yanzu na ke kallo kuma ina jin dad'i, sannan Haseenah duk da ki na ganin kamar kinsan komai a kai na har yanzu da saura, sani na a namiji ba shine sanin da ya kamata kuyi alfahari da shi ba, me na ke so?Me ye ba na so? Me ke sani farin ciki? Me ya ke b'ata min rai? Me yafi saka ni nishad'i da akasin haka? Wannan shine ya kamata ki zage damtse wajen sani, sai maganar makauniya da ki ka kira ta da shi, a gaskiya ba zan b'oye mi ki ba Haseenah rai na ya b'ace fiye da yanda ki ke tunani, me ya sa ba ki yi tunanin larura ce da Allah ya d'ora mata ba, wacce ke ma ba ki wuce ya jarabce ki da ita ba? To wannan ya zama na k'arshe da ko a mafarki za ki sake kiran da makauniya, kin fahimta?"

Haseenah da zuciyar ta ke tafasa ta ke jin kamar ta fashe da ihu, saboda ganin duk ya tattara laifin ya d'ora mata, hakanne ya sa hawaye su ka zubo mata ta d'ago kai ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri, insha Allah za'a kiyaye."

Mik'ewa ya yi yace "Shikenan, sai ki bata hak'uri, da fatan hakan ba zai sake faruwa tsakanin ku ba."

A hankali ta kalli Khadija tace "Ki yi hak'uri aunty Khadija, insha Allah ba zan k'ara ba."

Hannun ta Khadija ta rik'o tace "Ba komai yer uwa, ki gafarce ni nima kinji, sharrin zuciya ne da b'acin rai, amma insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba."

Cire doguwar rigar shi ya yi ya fad'a ban d'aki dan yin wanka, mik'ewa Khadija ta yi tare da hannun Haseenah tace "Ki je ki taya shi wanka, zai iya wuni bai saki maganar nan ba, amma da kin mi shi abin da ya dace sai komai ya wuce."

Tura ta tayi ban d'akin ita kuma ta fita, ta na rufo k'ofar ta jingina a jikin k'ofar ta lumshe ido, a hankali ta ji zuciyar ta na hasko mata mijin ta da Haseenah a ban d'akin, yanda ta san mijin ta da sauk'in kai da raha da barkwanci ta san yanzu har sun fara juyewa, da sauri ta bud'e ido har sun cika da hawaye, "A'uzu billahi mina shaid'anir-rajim." Ta furta ta bar wajen, ta na zuwa ta samu Bilal har ya shirya cikin gajeran wando da riga, *cornflakess* ta d'auko da kofi da madara ta yamutsa mi shi, ba dan ran shi na so ba ya karb'a ya na turo baki, shafa kan shi ta yi tace "Yi hak'uri mana yarima, yau ne fa kawai, kuma yanzu za'a kammala abinci."

Cikin turo baki yace "Mummy ni da wannan abun gwara ki bani ayaba na ci."

"Shikenan to." Ta fad'a ta na mik'ewa, friji (fridge) ta nufa yar k'arama da ke d'akin na ta wacce ita ta siyi abar ta, ta d'auko ayaba biyu da gwanda da ke yanke a faranti ta dire gaban shi tace "To maza ka ci."

Da sauri Bilal ya fara ci dan yunwa ya ke ji sosai, kuma a k'a'ida ya na zuwa gida zai samu maman shi har ta kammala abincin, fita Khadija ta yi ta bar shi ta nufi madafa, sai da ta gyara ko ina kamar babu abin da akayi b'ari a ciki sannan ta d'ora ruwan zafi, cikin sauri ta ke komai in da ta b'areye doya ta zuba sannan ta fara had'a sauce d'in.

_Tukunya ta d'ora ta zuba mai, bayan ya yi zafi ta zuba silalallan naman ragon da ke fridge wanda ya ji albasa attarugu da maggi, soya shi ta yi sosai ya soyu kafin ta kwashe, albasar da ta yanka mai yawan gaske ta zuba a cikin man, haka ma tumatiri d'anye da ta yanka da fad'i ta zuba a ciki, rufewa ta yi ta fara b'are tafarnuwa, zuwa lokacin albasa da tumatir sun rusuna sosai, kayan k'amshi da gishiri ta zuba kafin ta jajjaga ataru da tafarnuwa da poivron kafin ta jujuya sosai, maggi ta saka da yan ruwa kad'an sannan ta sake rufewa, a lokacin kuma doyar ta ta silala ta juye ta a mataci kafin ta zuba ta in da ya dace, komawa ta yi kan miyar nan ma komai ya yi daidai, k'wai ta d'auko guda uku d'anye ta fasa shi cikin wata k'aramar roba ta kad'a shi sosai, cikin miyar ta zuba ta na motsawa saboda kar ya yi gudaji-gudaji, ta na zubawa kuma ta kawo soyayyen namanta ta zuba sai ta rage wuta dan ta k'arasa dahuwa, doyar ta d'auka ta kai kan teburin d'akin Usman ta dawo ta juye miyar bayan ta fitarwa da mai gadi na shi, tsaf ta jera su akan teburin._

Ta juyo za ta fita dan yin wanka ta ji fitowar su daga d'akin, juyawa ta yi ta kalle su da murmushi tace "Barka da fitowa."

Sai da ya kalli teburin yace "Barka baiwar Allah."

Haseenah ta kalla tace "Amarya ki yi hak'uri na yi karambani, na kammala mi ki girki amma fa mai sauk'i ne, ban san ko zai birge ki ba."

Ta wutsiyar ido ta harare ta amma sai ta yi murmushi tace "Haba aunty Khadija ya ki ka wahalar da kan ki? Gashi kuma da fitar da zaiyi yanzun abinci ne zai siyo mana."

Da mamaki Khadija ta kalle ta tace "Siyowa kuma, haba dai amarya, gidan nan cike da abinci Allah ya hore, ga kuma mata ma su rai da lafiya, amma ya fita siyo abinci, a'a gaskiya sai dai in da wata larura."

Usman da ke kallon ta da murmushi ne ya taka ya isa ga kujera ya ja ya zauna, tangale hab'a ya yi ya kalli dukan su yace "Ku taimaka ni ku zuba min abincin to na ci."

Haseenah da ranta ya gama b'acewa saboda abin da Khadijar ta fad'a d'akin ta ta nufa tace "Aunty kawai ta zuba, tun da dama ita ta yi girkin, ni wanka zanyi."

Da sauri Khadija tace "Ni ma fa wankan zan yi." Amma ina Haseenah har ta fita ta shiga k'ofar da za ta sadata da na ta falon, abu d'aya da Khadija ta fahimta shine Haseenah ba ta ji dad'in abin da ta yi ba, ita kuma ta yi ne saboda ita ce silar zubar mata da girkin da ta d'ora, juyawa ta yi ita ma za ta tafi sai kuma ta juyo, idon su ne suka had'u da na Usman da ke kallonta, kamar yanda tasan ba ya iya shirya kansa da kyau in ba ita ta taimaka masa ba, hakan ta ke da yak'inin ba zai iya zuba abincin nan ba in ba wani ya zuba masa ba, dawowa ta yi ta zuba mi shi ta zauna nesa da shi tace "To maza ka bada himma."

Kwab'e fuska ya yi yace "In dai ba za ki ci ba ni ma haka."

Kallon shi ta yi tace "Gaskiya sai dai ka jira Haseenah ta zo ku ci, wanka yanzu kawai na ke son yi."

Rumgume hannaye ya yi a k'irji yace "Da alamar maganar ki ke so."

Wata dubara ce ta fad'o mata dan haka ta mik'e tace "Shikenan to ina zuwa, bara na kira Bilal."

Ta na fita ta samu Bilal a falo tace "Bilal, tashi mahaifin ka na jiran ka ku ci abinci, ina zuwa yanzu ka ji."

"To Mummy." Ya fad'a yana nufa falon, wanka ta shiga shi kuma ya na zuwa Usman ya rumgumo shi jikin shi ya na fad'in "Yarima na ya ka ke?"

Baice komai ba ya kalli Usman d'in ya na turo baki, lab'e baki Usman ya yi yace "Ko dai yaro hushi ya ke da baban sa ne saboda bai je d'aukar shi ba?"

Sai lokacin ya saki fuska yace "A'a Abba, bacci na ke ji."

Duk da girman yaron amma haka ya zaunar da shi akan cinyar shi yace "To idan mun ci abinci sai ka yi baccin ko?" A tare suka saka hannu su na cin abincin su na hira, har sun ida su na nan zaune suna ci gaba da hirar su irin ta d'a da uba Haseenah ta shigo, kallon ta Bilal ya yi yace "Sannu aunty."

Da murmushi har kunne ta amsa da "Sannu yarima, ya ka ke?"
Chapter 24 · 0% Book details