← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 86

Sashe 84

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da tabbatarwa tace "Sosai kuwa, me zai hana ni?" Gyad'a kai kawai ya yi ya cije leb'en k'asa, har na wuce na yi saurin dawowa baya cike da tsoro, murza ido na yi ina so na ga wai tabbas shine wanda na ke zato ko kuma dai gizo ne, da mamaki na ce " *Abbas* (jarumin littafin *Sanin masoyi*), ai kam da sauri ya juyo, amma abun mamaki ya na gani na saiya had'e rai ya sake juya min baya, har zan shiga tunanin dalilin da ya sa ya min haka sai kawai na ji andafa ni, juyowa na yi sai kuwa na ga takwarata, cike da farin ciki mu ka rumgume juna ta na fad'in "Takwarata me ki ke anan?"

Raba jikina na yi da nata na sake kallonta ta yi kyau sosai, murmushi na yi na ce "Na zo biki ne ni ma."

Tsaki naji Abbas yaja hakan ya sa mu ka kalle shi a tare, *Sameera* ce tace "Jarumi na lafiya ka ke tsaki?"

Da k'yar yake maganar saboda miskilanci yace "Kinsan ba na son hayaniya, wannan kuma ta tsaya min a kai ta na zuba kamar 'ya'yan kurna."

Tabbas raina ya b'ace yanda Abbas ya nuna ni kamar ya nuna kashi, tab'e baki na yi na ce "Da ace banga lokacin da ka ke wa takwarata 'yar murya ba da sai ka zare min ido, amma tunda har na ga komai to magana ta k'are, wannan shan kunun duk birga ce wallahi."

Kallon Sameera na yi na ce "Takwara idan kun koma gida lafiya ki gaishe min da su Bashir da su Abba da Mama." Da murmushi a fuskar ta tace "Za su ji aunty Meera."

Har zan wuce na ji Abbas yace "Ta na nan har yanzu yanda take kamar za ta fad'i ta na fama da bibiyar rayuwar mutane."

Wucewa na yi na barshi da takwarata tace mi shi "Ba fa na son haka uban yara, duk abin da za ka fad'a mata kamar ni ka ke fad'awa."

Wani kallo kawai ya bita da shi kamar zaiyi bacci, ni kam ina barin nan na shiga neman mutuniya ta, ai kam bansha wahalar ganin ta ba, da gudu na k'arasa na rumgumeta ta baya ina fad'in "Ohhh, my Hajiata."

D'ago kai ta yi ta kalle ni tace "Lah! aunty Meera, ke ce anan? Me ki ka zo yi wurin nan?"

Saida na taushe zuciya ta kafin na ce wani abu *Umar Faruk* (jarumin littafin *Jihadi*) ya fizgoni na yi baya ya na fad'in " Dallah malam sake ta, me ye haka kin wani zo sai kin karya ta."

Ba dan Umar ne ba da sai na mi shi rashin mutumci, amma saina k'yale na ce "To cinye ta zanyi da ka wani taso min haka?"

A tsaurare yace "Ki yi baya ki daina tab'a jikin matata shine kawai abin da na sani."

Rik'e hab'a na yi na ce "Ikon Allah, beby mijin beby, wato wai kai mai kishi ko? To Allah ya kyauta."

"Ya ma kyauta." Ya fad'a ya na kallo na, *Khairat* na kalla na ce "Hajiata ina *Zubaida* ne? kinsan fa fan's sunyi kewarta."

Murmushi ta yi tace "Ta na gida bata jin dad'i ne, kuma ga tsohon ciki da ke jikinta, shi ya sa ta zauna gida tunda tafiya ce mai nisa."

Juyawa na yi na kalli Umar ina dariya, shi kam sai ya had'e rai ya na harare na, saida na fara takawa na ce "Lallai Umar ba dama, wato har yanzu ka na nan ka na tsula tsiyarka, daga wannan ta sauke wannan za ta d'auka, humm."

Juyawa na yi zan wa Khairat magana amma sai Umar ya ciro takalman shi zai jefe ni, da gudu na bar wajen ina dariyar mugunta, kujera na samu na zauna ina sauke numfashi kamar saukar aradu daga gefena aka ce "Aunty Meera ya ki ke?"

Da murmushi na juyo dan na gane mai muryar, da farin ciki na d'aga mu su hannu na ce " *Falmata* (d'aya daga jaruman littafin *Itace k'addarar mu*), lafiya lau, ya ki ke kema?"

"Lafiya lau, me ki ke anan?" Saida na b'ata rai na ce "Abin da ki ke yi."

*Adam* ne yace "Daga tambayar arzik'i malama sai abu ya zama na tsiya."

Hararan shi na yi na ce "Kai ni rufe min baki dallah ban sa da kai ba."

"Ke ni ki ke fad'awa haka?" Ya fad'a a hassale, ni ma a hassalen na fad'a "Eh anyi d'in, me za ka yi?"

Tasowa ya yi ya nufo kaina amma ban gusa daga in da na ke ba, saida ya tsaya gaba na ya nuna ni da yatsa zaiyi magana na ga an rik'e hannunshi daga baya ance "Haba kai kuwa Adam, aunty Meera ce fa, ba ka gae ta bane?"

Sai lokacin na ga mai magana ashe *Marwan* (jarumin littafin *Kawu na ne*) ne, huci ya yi ya sauke hannun shi ya koma mazaunin shi, har ya zauna a kalli Falmata na ce "Fati wai ina d'an uwan ku mahaukaci?"

Cike da jimami tace "Ki bari kawai aunty Meera, har yanzu ya na can babu sauk'i, wallahi duk ya sauya ya zama mahaukacin gaske."

Tab'e baki na yi karo na farko da na ce "Allah ya yaye mi shi, *Fadjimata* kuma Allah ya mata rahama."

"Ameen." Ta fad'a ta na mayar da kallonta gaban ta, sai lokacin na kalli Marwan na ce "Marwan ina aunty na take?"

Da yatsa kawai ya min ishara zuwa bayana, ina juyawa na ga *Wafa'atu* bayana da tulelen cikinta masha Allah, da farin ciki na mik'e na rumgume ta na ce "Aunty Wafa'atu ashe Allah ya nufa."

Ita ma da farin ciki tace " allah ya nufa Meera, addu'ar ki data fan's d'in ki ta same mu har inda muke, gashi yanzu Allah ya sa nima ina d'auke da cikin wata bakwai."

"Kai to Allah ya raba lafiya aunty wafa'atu."

Da "Ameen." Suka amsa su dukan su, sai lokacin Wafa'atu tace min "Amma me ki ke yi anan? Ke ma Khadija ce ta gayyace ki."

Raina ne ya b'ace da tambayar sai kawai na yi gaba na bar su tsaye, ina cikin tafiya naji anyi magana cikin shagwab'a ance "Aunty Meera shine ko ganin mu ma ba kya yi."

Juyowa na yi sai kuwa naga *Raheenat* (jarumar littafin *K'angin rayuwa*) ce, saida na gama kallon mutanen da ke tare da ita, ita da *Sameera* suna manne da juna haka ma *Abdul hakeem* da *Sadiq* suna jone sai tattaunawa suke, matsawa na yi dan mu gaisa amma Abdul hakeem sai cewa ya yi "Ke me ya kawo ki nan?"

Baki bud'e na ce "Abdul hakeem yaushe ka zama haka kuma? A sani na dai ka na da taushin zuciya."

"Sanin baya ki ka min, ai yanzu abin ba sauk'i, dan haka b'ace min da gani kafin ran ki ya b'ace." Yanda ya ke maganar ya sa na tsora ta na juya zan tafi Sameera tace "Haba takwarata, yaushe ki ka zama mai tsoro ne haka har da wannan zai tsorata ki."

Abdul hakeem ne ya kalli Sadiq yace " aboki na ka sa matar nan taka ta yi shiru kafin na fitar mata da jini a baki."

Kallon Sadiq Sameera ta yi tace "To sa na yi shiru d'in, ina jira."

Wuk'i-wuk'i Sadiq ya yi da ido kafin ya kalli Abdul yace "Aboki na ka yi hak'uri, ba zan iya ma ka komai ba gaskiya, wannan matar da ka ke gani ina tsoron bala'in ta."

Wata dariya Sameera da Raheenah su ka yi harda tapa hannu, ni kam dariya na yi na yi kafin na ce "Wai ina yara na ne?"

"Suna gida." Cewar Raheenat, juyawa na yi na ce "Sai anjiman ku."

Kallon Sadiq na yi na ce "Ka gaishe min da bazawarar nan taka."

Waro ido ya yi ya kalle ni ya kalli Sameera, tasowa yayi zai min magana sai kawai takwara ta jawo rigarshi ya koma ya zauna tace "Dan Allah ya toni asirinka shine za ka bud'e mata ido."

Abdul ne ya kalle ni yace "Kedai anyi guba wallahi, to yanzu dad'in me ki ka ji?"

Kallonshi na yi na ce "Ka mantabi guba ce lokacik da ka ke sawa ina rubuta labarin soyayyarka da sabuwar budurwarka."

Kallon shi Raheenat ta yi ,dariya na yi na wuce gaba ina ganin bala'i ya b'arke tsakanin Sadiq da Sameera, Raheenah da Abdul dan fa ita ta yarda bazawara yake nema tunda a ganinta ina bibiyar rayuwar mutane, ta teburin da Adam ke zaune na wuce nan ma cewa na yi ya gaishe da budurwar shi, a tak'aice saida na bi duka ma'auratan d'aya bayan d'aya ina hura mu su wuta, kuma babu wacce ba ta yarda ba saboda ganin ba zan fad'a mu su abinda ba haka bane, kafin ka ce me wajen taron ya fara d'aukar gumi saboda muryoyin dake tashi sama, musamman Kaussar da Khairat da Sameera ta Abbbas, sosai suka rufe ido wai ana cin amanarsu, da dai abin ya k'i sauk'i sai gashi ina niyyar sulalewa na bar wurin na ji ance "Aunty Meera barka."

Ina juyowa da sauri naga teburin cike da jaruman littafin *Aure*, da farin ciki na k'arasa muka gaisa kafin na kalli matan na ce "Ina yaran?"

*Fatima* ce tace "Suna gida aunty Meera."

Sai *Rauda* da tace "Ai sun fara wayo yanzu." Kallon Laure nayi da kanta ke k'asa duk take jin ta a takure, murmushi nayi na ce "Lauratu sarauniyar kunya, to Allah ya mayar da ku gida lafiya, ni na yi gaba wajen nan ba zai zaunu gare ni ba."

"Me ya sa?" Cewar *Iro*, kallon shi na yi kafin na ce wani abu *Siryanu* yace "Akwai bala'in data had'a tunda kaji haka."

*Imam* ne yace "Ko kuma tsokana ba, kasan Meeran mu da tsokana fa, watak'ila akwai wanda ta harzuk'a."

Ban tsaya saurarensu ba na fece ba su ma san da tafiya ta ba sai gani sukayi bana wajen.

😂😂😂😂😂
Chapter 84 · 0% Book details