Sashe 35
Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aziza ce tace "To ai dole tunda ta gama da shi, in ba kinibibi ba miye ta ke bashi kowane dare ya na sha da sunan shayi? Har da wasu k'ulallen abubuwa kamar kashin shanu kuma bai kai kashin shanu ba na ga ta na sakawa."
"Da gaske ki ke Aziza?" Cewar Rabi'a da duk cikin su tafi tsanar Khadija tun lokacin da ta nemi kud'i wajen d'an uwan ta, ta rik'e abun sosai a zuciyar ta ya na d'awainiya da ita har yanzu, Aziza ce tace "Wallahi kuwa, a madafa ta ke aje abun, kuma ko a gaba na sakawa ta ke."
Cike da makirci Rabi'a tace "Hakan ma wata hujja ce da za ta tona ta, Aziza ya za ayi ki d'auko mana wannan abun?"
Cike da rashin tsoro tace "Abu mai sauk'i, in dai har yanzu ta na aje shi in da ya ke ai zan gan shi."
Hassenah na shiga ta samu Khadija tsakiyar gado da manyan mata sai hira suke ana dariya, cike da fargaba ta yi abin da ya kai ta ta juyo ta fito, wajen su Hassana ta koma su ka ci gaba da hirar su, Khadija kuma na ganin fitar ta ta kalli k'awar ta Hajia Turai Dubaï tace "To kinga amaryar ta wa da har yanzu ki ka kasa zuwa ki gani."
Waro ido Turai ta yi tace "Ita ce kishiyar ki?"
"Eh." Ta fad'a har da dariya, hararan ta ta yi tace "K'arya ki ke wallahi, wannan ce za ta zama amaryar ki? Haba Khadija, ko da dai nasan halin mutanen mu ba kunya ne da su ba, amma taya Usman zai had'a ki da yarinyar can?"
*Umma* Khadija ta kalla tace "Ke da ki ka tabbatar sai ki fad'a mata gaskiya."
Umma ce ta d'ora "Wallahi ita ce kishiyar ta."
"Bala'i." Cewar Hajia Turai cikin d'aga murya bugu da k'ari Allah ya hore muryar sosai, kasancewar irin mutanen nan ne masu ido bud'e da basu tsoron tashin hankali ko hargowa ya sa ta shiga aibata Haseenah ta na shammace ta, tun Khadija na cewa ta yi shiru dan Allah har ta yi banza da ita, hakan kuma da akayi duk a ido da kuma kunnen 'yar k'anwar mahaifiyar Usman (cousine d'in shi), ba ta b'ata lokaci ba wajen fitowa ta fad'awa Hassana da dama akan maganar Khadija suke, amma sai da ta keb'e ta gefe d'aya, Hassana ba ta tanka ba har lokacin da Mariya ta kira Haseenah wai idan ta na gida za ta zo ta kawo mata sak'on wajen malam, nan Haseenah ta fad'a mata ba ta gida amma za ta zo yanzu ita ta karb'a, sallama ta mu su tace ta tafi gida ba ta jin dad'i, ta na samun adaidaita ta wuce gidan Mariya, magani ta bata kala har uku wanda in dai ta yi aiki da su to ta tabbatar mata Usman zai zama na ta, d'aya za ta shafa a marar ta ne ranar kwanan ta ya sadu da ita, d'aya za ta saka a abin sha da ya danganci koko, fura ko kunu, sai kuma d'aya da za ta zuba a k'ofar d'akin Usman ya tsallaka, cike da farin ciki da jin ta yi nasara ta baro gidan ta nufi gida.
Fitar ta ba jimawa Khadija ita ma ta wuce gida dan kama aiki, nan fa su Hassana suka shirya abin da za su fad'awa Usman tare da shirya yanda za su yi.
Bayan sallah isha'i Usman na zauna a majalisar su ana hirar duniya kiran Hassana ya shigo wayar shi, sun tsara ita ta kira shi ne saboda ita ce babba da ke bi mi shi, ya na d'auka ta gaishe shi cikin ladabi ya amsa, cikin taushin murya ta d'ora da "Yah Fodio dama ina son yin magana da kai ne, sai dai bansan ta yanda za ka fahimce ni ba."
Kamar ya na gaban ta ya yi murmushi yace "Ki tak'aita mana wahala to, ki fad'a a yanda zan fahimta."
Gaban ta ne ya sake fad'uwa kafin ta dake tace "Yah Fodio dama abin da ya faru d'azu wajen biki ne gaskiya bai ma kowa dad'i ba, Khadija dai ita ce babba kuma za ta iya rik'e ragamar gidan ka ko ba ka nan, amma abin da su ka yi d'azu da k'awayen ta gaskiya bai dace ba, dan wannan salesalen tayar da masifa ne, wallahi saida mu ka iza k'eyar Haseenah ta koma gida saboda ran ta ya sosu."
Kasanvewar ya na cikin mutane ya sa matsa gefe da su yace "Me ya faru? Me Khadija ta yi ita da k'awayen ta? Hassana ba na son masifa da tashin hankali ke kin sanni."
Cike da tabbatarwa tace "Wallahi gaskiya na ke fad'a ma ka, a d'akin *Zaliha* fa su ka zauna suna ta shammatar Haseenah su na zagin ta ta uwa ta uba, idan kuma ba ka yarda ba ka tambayi *Nana* (cousine d'in su) za ta fad'a ma ka gaskiya, musamman ma wannan k'awar ta ta mai ido tsaye Hajia Turai."
Ba wai rantsuwar da ta yi ba ce ya sa ya yarda sai anbaton sunan Hajia Turai da ta yi, matar ba ta da wata d'abi'a da zai ce ba ya son mu'amular ta da matar shi, sai dai irin matan nan ne da masu da kimtsi, komai ya zo bakin ta fad'a ta ke sannan ba ta tsoron bala'i da mace kl namiji, hakan ya sa ma har yanzu ta ke zawarci babu mijin aure sai duniyar ta da ta ke ci da tsinke, nisa da tunanin da ya yi ne ya sa ya kashe wayar bai ma san ya kashe ba, zunbur ya mik'e ya fad'a motar shi ya nufi gida.
Tsaf Khadija ta gama shirya komai ta aje a muhallin shi ta shiga wanka, jin babu motsin ta ne ya sa Haseenah tabbatarwa yanzu ta na wajen shiri, ta falon ta ta shigo na shi falon cikin sand'a da rashin gaskiya, kai tsaye k'ofar uwar d'akin shi ta nufa da k'ullin maganin ta, ta na zuwa ta bud'e ledar tasa yatsu biyu kamar yanda aka fad'a mata, barbad'awa ta yi tare da kiran sunan Usman, sau uku ta zuba kuma a kowane zubawa sai ta kira sunan shi, da sauri ta rufe ledar ta koma falon ta da sauri cikin tsoro, ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke kafin ta dafe k'irji ta yi murmushi, Usman da ke hanyar shi ta zuwa gida ne ya ji wani bala'in sarawar kai kamar an buga mi shi guduma, da k'arfi ya take motar ya tsaya ya dafe kan shi, ya jima a haka sai da ya ji motoci na mi shi odar ya ba su hanya kad'ai ya dawo hayyacin shi ya taka, Khadija na d'aki ta gama duk wani shirin ta ta mik'e ta na d'aura d'an kwali ta ji an bud'e k'ofa da k'arfi, juyowa ta yi dan ganin waye wannan, ganin Usman a wani yanayi da ita dai ba ta tab'a ganin shi a ciki ba ya sa ta d'an kalle shi da mamaki, ganin nufota kawai ya ke ba magana ya sa ta k'ara yin baya da in'i'na tace "A..Abban...Bil."
Ba ta k'arasa ba yace "Khadija akan me ku ka ci zarafin mata ta a gidan biki cikin mutane?"
Mamaki ne fal a idon ta, rarraba ido ta fara yi sai motsa baki ta ke ta na so ta yi magana amma ta kasa, nuna ta ya yi da yatsa yace "To daga yau kar haka ta sake faruwa, idan ba haka ba kuma ran ki zai b'ace, sannan Hajia Turai ba na son ki sake mu'amula da ita, kinji na fad'a mi ki."
Bai jira me za tace ba ya fita daga d'akin ya nufi d'akin Hassenah wacce ta buga tagumi ta na jiran ta jime zai faru, ya na ganin ta da wannan tagumin sai ya ji tausayin ta a tunanin shi akan abin da ya faru ne, ita kuma ba ta ma san me ya faru ba, zaune ya yi kusan ta ya kalle ta yace "Amarya ta, dan Allah ki yi hak'uri kinji akan abin da ya faru, insha Allahu na mi ki alk'awari hakan ba za ta sake faruwa ba."
Cikin rashin fahimta tace "Me kuma ya faru? Akan me ka ke magana?"
Jannyo ta ya yi jikin shi ya na shafawa yace "Idan ke ba ki fad'a min ba ai Hassana ta fad'a min, amma kamar yanda na fad'a mi ki ne ba zai sake faruwa ba in Allah ya yarda."
Shiru ta yi a k'irjin shi ta na tunanin me ye ya faru to? Jin ta yi shiru ya sa ya d'agata daga jikin shi da cewa "Zan shiga wanka, amma ki tabbatar kin fito mun ci abinci ba sai na zo da kai na ba."
Da kai kawai ta ma sa alamar to, fitowa ya yi ya nufi d'akin shi, ya na bud'a k'ofar ya tsallaka ya sake jin gaban shi ya tsinke ya fad'i tare da sarawar kai, hannu d'aya ya saka ya dafe kai ya rintse ido sosai, da k'yar ya iya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Gaba d'aya jikin shi ne ya yi sanyi a haka ya cire kayan shi, zai shiga wanka Khadija ta yi sallama a d'akin ta shigo, shiru ya mata kamar bai ji ta ba har ta tsaya gaban shi, wani abu ya ke ji a zuciyar shi da bai tab'a jin irin shi ba tunda ya ke da ita, amma da ya ke sabon abu ne sai ya taushi zuciyar shi, a hankali ta rik'e kunnuwan ta cikin taushin murya tace "Ka yi hak'uri *sadauki na*, na karb'i kuskuren da k'awaye na su ka yi, kuma zanyi yanda ka ce da yardar Allah."
Ba fara'a a fuska yace "Ya wuce." Ban d'aki ya nufa ta yi saurin rik'o hannun shi ya juyo, marairaicewa ta yi tace "Ka tab'a wanka da kan ka idan ban taimaka ma ka ba?"