← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 86

Sashe 45

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk ya gane magana ce ta fad'a mi shi amma haka ya fizgo Bilal yace "Yana nan tare da ni, idan kuma da wanda ya isa ki aiko shi ya k'watar mi ki shi na gani."

Tab'e baki ta yi tace "Hum! Wa ma zan aiko ya k'watar min shi? Ai sai marar kunya irin ka."

Da yatsanshi ya nuna kan shi yace "Ni ne marar kunyar? Ni ki ke fad'awa haka Khadija?"

"An fad'a, da abin da za ka yi ne? Mugu azzalumi, ni dama nasan tunda ka ce za ka k'ara aure nasan abin da za ayi kenan, aikin banza kawai."

Da sauri Bilal ya tsaya tsakiyar su cikin d'aga murya yace "Abba."

Kallon shi ya yi ya d'an shafa kan shi, kamar zaiyi kuka yace "Abba nasha ganin ku kuna rigima akan abubuwa dayawa, amma ban tab'a ganin ku a irin wannan yanayin ba."

Hannun shi ya kama su ka nufi komawa cikin gidan, juyowa yaron ya yi ya na kallon mahaifiyar shi haka ita ma shi ta ke kallo, saida ta ga shigewar su ta juya ita ma dan ba zata tsaya rok'on shi akan Bilal ba, tunda ta haiho shi dai ai ta san ba zai raba ta da shi ba, mai gadi ta barwa kayan Bilal ta fice daga gidan ta hau adaidaita, kai tsaye kuma gida aka aje ta ta shiga ciki cike da kunya da kuma tafasar zuci, kamar yanda har yanzu gidan su ba su daina al'adarsu ba ta taruwa falon mahaifiyar su haka ma yau, da sallama ta shiga duk da taji hayaniyar su ba lallai ta bari su ji ba, ai kuwa ba su ji ba har saida ta shigo d'akin ta aje jakar ta k'ofar d'akin, kowa mamaki ne ya kama shi in da ake fad'in "Khadija, ke ce a wannan daren?"

Ashir ne ya d'ora da "Lafiya dai ko auta? Daga ina ki ke haka k'arfe goman dare?"

Saida ta k'are kallonsu duka taga yan uwan ta ne kafin ta k'arasa shiga ta je gaban Mama ta zauna kanta k'asa, Mama ce ta fara dafa ta tace "Khadija, lafiya na gan ki haka? Wani abu ne ya faru?"

Cikin k'unar zuci tace "Usman ne yace na zo gida sai ya neme ni, Bilal ma na tare da shi."

Mansur ne yace "To me ya sa? Me ki ka mi shi haka da ya d'auki wannan matakin."

Kallon shi ta yi tace "Saboda amaryar shi mana, saboda munyi fad'a da amaryar shi shine yace na taho gida, kuma wallahi ba zan koma gidan shi ba tunda abun shi akwai rashin mutumci, gwara su zauna shi da ita har duniya ta tashi."

A hankali Habeeb ya sa hannun shi ya shafi fuskar ta yace "Yatsu ne fa akan kumatunta, marin ki ya yi?" Ya tambaye ta, saboda idon ta sun rufe ya sa tace "Eh mana, bayan mari ma wace magana ce bai fad'a min ba."

"Mari kuma?" Cewar Ashir ya na sake juyo da fuskar ta, Naseer ne ya katse shi da cewa "Ai kuwa Usman bai nemi zaman lafiya ba, yanzu saboda wata shegiyar yarinya zai mare ki, bari su ga yanda ake rashin mutumci kam."

Mama ce ta katse shi da cewa "Kai miye haka? Wai me ya sa ku ke haka? Me ya sa kuke son mantawa da baya?"

Shirun da su ka yi ne ya sa Mama cewa "Shikenan ita tafi k'arfin a b'ata ran ta kenan? Karfa ku manta shekaru suka yi a tare, shine yanzu daga yar k'aramar matsala za ku wani fara maganar rashin mutumci, to ba na so kunji na fad'a mu ku, kuma ma ita ta fad'a mu ku gaskiyar abin da ya faru? Ita ba babba bace ba? Meya hana ta yi hak'uri da duk abin da ta gani ko ta ji? Ai dama na fad'a mi ki dole sai kin kau da kai musamman yanzu da suke kan ganiyar cin amarcin su, zai iya yin komai saboda giyar da ya ke kurb'a."

Cikin rashin jin dad'i Bashir yace "Amma kuma Hajia har da duka? Koma me ya faru ai ya nutsu ya san me yake, amma tab'a lafiyar ta gaskiya fa ba abin da za mu iya jura bane."

Cikin hushi Habeeb yace "To ni abin da yafi k'ona min rai shine wai akan wata amarya, to k'ara aure hauka ne da zai kwance mi shi kai, gaskiya har da iskanci."

Naseer ne yace " Wallahi magana zan masa, dan ba zai mare ta a banza ba, in ba haka ba kuma to fa abubuwa marasa dad'i ne za su fara faruwa tsakani wanda basu faru ba a baya."

Cikin nutsuwa Ashir yace "Kunga ku kwantar da hankalin ku, yanzu dai ba yace ta zo ba har saiya neme ta? To ai sai mu jira shi har ya neme ta kamar yanda yace, kunga sai muyi magana yanda ya kamata."

"Ni ko ya zo ma ba zan koma ba, Usman ya gama tozartani a gaban d'ana da matar shi, gaba d'aya nunawa ya ke kamar ba mu tab'a zaman mutumci da shi ba, dan haka ko ya zo ma babu in da zanje."

Ta na gama maganar ta ta mik'e ta nufi tsohon d'akin ta da tasan dama nan za ta sauka, Mama ma mik'ewa ta yi ta lek'o k'ofar d'akin ta d'auki jakar ta ta kai mata d'akin kafin ta fito, yan uwan kam sun jima su na tattaunawa dan ransu ya b'ace sosai, in da Khadija ma sam kasa bacci ta yi a daren saboda tunanin sauyin rayuwa, mutumin da ko tafiya zaiyi wacce ta zama dole da k'yar ya ke iya rabuwa da ita, wasu lokuta kuma idan da sarari tare sukan tafi duk in da zaije, ko suje da yaron su ko kuma su bar shi su tafi, amma yau shine ya kore ta daga gidan shi wai saiya neme ta, k'wafa ta yi tare da gyara kwanciya a ran ta tace "Wallahi ba zan koma ba sai ya gane kurensa, har ni nayi kama da macen da zai ce jeki saina neme ki." Wata k'wafar ta sake yi cikin b'acin rai.

A wajen.su Usman kuma da k'yar ya rarrashi Haseenah ta hak'ura da taga Khadija ta tafi, ko da ya kwantar da Bilal ya dawo ya dinga mata abubuwa kamar tsohon bazawari, ita kam har kunya ma ya fara bata, haka dai suka kasance har gari ya waye.

Kasancewar babu karatu a ranar ya sa Bilal shiryawa ya yi zaune a falon mahaifiyar shi ya na kallo, haka yake zaune wurin nan yunwa na gwagwuyar mi shi ciki amma babu yanda zaiyi, d'akin mahaifiyar shine ke da abubuwan ci kuma a rufe yake, har saida ya kai ya fito wajen mai gadi ya zauna ya na kallon hanya, lokacin ne Usman ya gamo shiriritar sa ya fito neman Bilal, ganin shi tare da mai gadi ya sa ya kira shi suka koma ciki, tare suka karya kumallo ya tashi zai fita, kallon shi Bilal ya yi yace "Abba dan Allah ka tafi da ni wajen Mummy."

Cikin d'aure fuska yace "Ni na fad'a ma ka wajen ta zanje?"

A hankali ya girgiza kai, ganin ya juya zai fita ya sa shi k'ara cewa "To Abba ka tafi da ni sai ka aje ni wajen Hajia."

Cikin hassala ya juyo yace "Wai me ya sa dole sai na tafi da kai? Kai ba za ka iya zama gida ba idan ba karatu? To ba can wajen zanyi ba ka zauna tare da Mamar ka."

Kallon Haseenah Bilal ya yi kamar yanda Baban shi ya nuna mi shi ita da hannu, idon shi ne suka cika da hawaye ya sunne kai k'asa, Haseenah ce tace "Kaga dan Allah, ba na son neman magana ni, in har ba zai zauna ba saboda ya na ganin cinye shi zanyi dan Allah ka tafi da shi, dan ba zai yiwu yaro da gidan ubanshi ba a same ni daga ni sai shi a gida ya zama kamar wani maraya, dan gashi tun yanzu ya na nunawa a gaban ka, in ba ma iskanci ba ni d'in bak'uwar ka ce?"

Duk da hararan shi da take amma baisa Usman jin wani abu ba ko kad'an, hakan ne ya sa ma ya nuna Bilal da yatsa yace "Kar ma kace za ka fara min wannan nunkufarcin a gida wallahi, dan ba za ka ji dad'i ba, kuma a gidan za ka zauna kai da ita naga wanda ya isa ya hana."

Hannu ya sa aljihu ya matso kusan shi yace "Ka saki ranka kaji ko, idan zan dawo zan siyo maka abun mamaki."

Kai kawai ya d'an d'aga mi shi alamar to, fita ya yi Haseenah na ganin haka ta kalle shi tace "To d'an masu gida, maza tashi ka d'auke kwanukan nan ka wanke su, dan na lura kai ba'a morar ka a gidan nan."

Hawayen da yaron ke rik'ewa ne suka taho mi shi, mik'ewa ya yi ya d'auki farantan ya nufi madafa da su, ya kai madafar zai bud'a k'ofar ya rasa ya zaiyi, cikin dubara ya zura hannu zai bud'e sai kuwa wani faranti ya fad'o k'asa ji kake "tatssssssss."

Da gudu gudu Haseenah ta taso ta fito waje ta na fad'in "Ka zubar halan? Saboda bak'in hali, dan na saka aiki shine za ka fasa min kaya."

Ta na zuwa ta kalli farantin da ke k'asa ta kalli Bilal da ya kafe ta da ido cike da tsoro, cikin jin haushi da mugunta ta d'aga hannu ta d'auke da mari ta na fad'in "Dan uban ka kai musakin ina ne? Uban ka ne ya siya min da za ka fasa min kaya?"

Kamar saukar aradu taji daga bayan ta ance "Sai dai uban ki wallahi ba na shi uban ba, 'yar matsiyata da ba ki gaji arzik'i ba, talaka 'yar talakawa, wato an samu wuri ko?"

😂😂😂😂 _Bala'i da d'umi d'umin shi, ni kam waye wannan? A cikin yan biyar wa ya fi zafin zuciya? Ku tayani tunani mana mutane na._😉
13/02/2020 à 13:10 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*
Chapter 45 · 0% Book details