← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 86

Sashe 56

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh, suna ciki." Mik'ewa ta yi ta kashe duk wutar d'akin ta kile da makulli suka fita, a hankali cikin sand'a ta isa ga k'ofar da za ta shigo da mutum falonta da falonshi ta kulleta kafin suka fita ta d'aya k'ofar, nan ma rufewa ta yi kafin tace Bilal ya kira mai gadi k'ofar gida sannan ya tsayar mu su da adaidaita sahu, ba wahala kam mai gadi ya shigo har in da take ya tsaya yace "Mai adaidaitar na k'ofar gida Hajia."

"Yawwa karb'i nan." Ta fad'a da bashi jakunkunan tace "Ka fitar mana da su muna zuwa yanzun."

"To Hajia." Ya fad'a ya na d'aukar jakunkunan ya jasu Bilal ma ya ja tashi jakar, saida ta lek'o ta hangi motar Usman alamar ya na gidan, saida taga ficewar mai gadi kad'ai ta fito ita ma ta fita, har an yiwa kayan nasu wuri dan haka za ta shiga mai gadi yace "Hajia, lafiya dai ko? Ko tafiya za ku yi ne?"

Juyowa ta yi ta kalle shi tace "Ka yi hak'uri Baba mai gadi, duk da dai abin da ya faru yanzun sirrine na gida na, amma kai ba yau muke tare ba, tunda na dawo sabon gidan nan na tarar da kai, tun Bilal na jinjiri, matsala ce ta faru da tasa dole sai na bar gidan nan na wani lokaci, ku yi hak'uri, na bar ka lafiya."

Ta na gama fad'a ta shiga adaidaitar suka wuce, da kallo ya bisu ya na fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, ita kuma amaryar da abin da ta zo da shi kenan? Wannan wace irin jaraba ce, mata da mijin ta kullum cikin farin ciki, idan ka ji hayaniya to suna wasa ne kamar yanda su ka saba, amma yau gashi su na shirin rabuwa dalilin wata, kai Allah ya kyauta."

Usman na ciki shi da Haseenah bai san tsiyar da ake ba, ba jimawa kam adaidaita ya sada Khadija da gidan su, Mama na ganin su da kaya ta fara salati da sallalami, kai tsaye d'aki ta nufa ta aje kayan ta ta wuce d'akin ta, tashi Mama ta yi tabi bayan ta sai matan yan uwan ta ne su ka bisu da ido, matar Habeeb ce kad'ai ta iya cewa "Aifa lokacin ya yi."

Shiru sauran su ka yi dan suma kawunan nasu a rarrabe suke, kowa da b'angaren da yake saboda suma akwai uwayen gida akwai kuma amare.

Babu abin da Khadija ta b'oyewa maman ta duka ta fad'a mata, duk da taji ba dad'i sosai amma sai bata nuna mata ba, kallon maman ta tayi tace "Dan Allah Mama taimaka min da maganin ciwon kai."

Tashi kawai Mama ta yi ta d'auko ta kawo mata tasha ta kwanta, matar Mansur ta shigo d'akin dan su kwashi labari sai dai ta samu Khadija har ta fara baccin wahala da fuska har yanzu a sumtume, sam Mama ba ta fad'awa 'yan uwan ta ba ko a waya sai dare da suka dawo su ka tarar da wannan abin takaici, lokacin Khadija zazzab'i ya sake rufe ta, Naseer har da k'walla ya yi da ya kalle ta, yanda ya sunkuyar da kai ne ya sa Habeeb dafa shi, goge fuskar da ya yi ne ya tabbatar musu kuka yake, Bashir ne yace "Kai haba dai maza, kuka fa? Ai ba kai ya kamata ka yi kuka shi ya kamata ya zubar da hawaye."

Wasu hawayen ne suka sake taho mi shi yace "Yanzu domin Allah me ya sa Usman ya yi haka? Mufa mun bashi ita ne da tunanin zai kula da ita, me ya sa zai mana haka yanzu? Saboda kawai ana ganin ita marainiya ce mahaifin ta ya rasu."

Sun jima d'akin ta suna tattaunawa in da take kwance ta dunk'ule, saida dare ya yi suka tashi suka koma nasu dak'unan, saida tasha magani kafin ta sake kwantawa, sai dai ba ta yi bacci ba har aka kira sallah asuba, sallah ta yi ta sake komawa ta kwanta ta na istigfari tasbihi da hailala da hannun ta na dama.

Ko da Usman ya fahimci basa gidan haka kawai yaji bai wani damu ba, hakan ya sa ma da safe ko da ya je gida ya samu su Hajia da maganar ya kuma fad'a mu su kar suce za su je su dawo da ita, harda had'a su da Allah akan su barta harta shiga hankalin ta, Bilal kuma d'an shi ne ba ta isa ta raba shi da shi ba, amma malam yace sam ba da shi za ayi haka ba, a k'arshe ma tambayar su dalilin faruwar haka akayi, fad'an Hajia shine "Makulli Usman ya bawa Haseenah ta aje na mota da zai tafi, ita kuma ta tashi fita tace ta bata, shi kuma yace kar aba kowa idan za'a fita a fad'a mi shi zai aiko da wani ya kaisu duk in da za su je, shine ta turmushe yarinya da k'aramin ciki ta karb'i makullin, dalilin hka fa ya kusa sawa ta yi b'ari."

Duk da jin haka yace zaije ya dawo da ita gidan ta, kuma kamar yanda ya fad'a ya cika maganar shi, amma maganganu mabanbanta ya ci karo da su, musamman da suka fad'a mi shi har da duka, har d'akin Khadija aka mi shi jagora ya ganta kwance da k'arin ruwa a hannu, dan tunda ta yi sallah asuba zazzab'i ya sake rufe ta, hakan ya sa Naseer ya d'auko likita har gida aka dubata, sosai suka nuna mi shi b'acin rai da cewa ba za ta koma ba har sai Usman ya dawo hankalin shi, baiga laifin su ba kam dan ya sa dole wata rana zai neme ta, haka malam ya juya rai b'ace da kuma kunyar abin da ya aikata, tun a hanya yace Usman ya same shi gida za su yi magana, da "To Baba." Ya amsa.

*Ku na ganin zaije? Yanzu fa Haseenah ita kad'ai ce.*

Saida ya sake wanka ya shirya yace "Amarya ta zanje gida na dawo, amma ba zan jima ba kinji, ki kula da kan ki."

Kallon shi ta yi ta na k'ara rufe jikin ta da zanin gado tace "Gida kuma? Na d'auka d'azu ka ce min gida ka tafi, ya da wuri haka za ka koma."

Ya na gyara zaman hular sa yace "Eh wallahi Baba ne wai ya ke son gani na, amma na san ba zan jima ba ai zan dawo."

Shiru ta yi a zuciyar ta tace "To idan fa yanzu ma dawo da Khadija za su tafi? Dole na yi wani abu."

Shagwab'e fuska ta yi tace "Yanzu tafiya za ka yi ka barni a haka? Ba ka da matsala kenan tunda ka samu biyan buk'atar ka ko?" K'ok'arin saukowa ta fara daga kan gadon ta na fad'in "Shikenan ai ka tafi."

Matsowa ya yi kusan ta zai kamo hannun ta ta kubce ta shige ban d'aki, bakin k'ofar ya tsaya yace "Haba ke kuwa, kar ki yi hushi mana, kinfa san ba na son b'acin ran ki ko kad'an."

"Ahhhhhhh, wayyo Allah ciki na, marata." Fad'in Haseenah daga cikin ban d'aki, bai tsaya tunanin komai ba ya kutsa ciki ya same ta zaune dafe da ciki alamar fad'uwa ta yi, bai tsaya komai ba ya d'auko ta sai kan gado ya dire ta, kallon ta yake ciki da damuwa ya na rik'e da hannayen ta yace "Garin yaya ki ka fad'i haka? Haseenah karfa ki mana asarar kyautar nan da Allah ya bamu, kinfi kowa sanin lokacin da na d'auka ina fatan Allah ya sake bamu haihuwa, ina son na ga gidan nan ya cika da yara kuma ya zamana ke ce uwar su."

Yanda ya k'arashe maganar kamar zaiyi kuka ne yasa tace "Ka yi hak'uri dan Allah, ni ma santsi ne kawai ya kwashe ni, ban kula ba sai ji na yi na fad'i saboda rai na a b'ace yake."

Kallon ta ya yi yace "To me ya b'ata mi ki rai haka da har ki ke neman ja mana babbar asara."

Cikin turo baki tace "To ba kai ne ka ce zaka fita ka bar ni ba, ni kuma wallahi ba na so ka tafi, satin ka biyu fa baka gari, kasan dai dole munyi kewar ka mu na buk'atar ka a kusa da mu, shine kawai daga ka samu yanda ka ke so sai ka ce za ka fita."

Da rawar jiki yace "Ai dai fitar ce ba kya so ko? To na fasa, kin gani ma? Zan kira Baba na fad'a mi shi ya yi hak'uri zan je anjima, shikenan kinji dad'i?"

Dariya ta yi ganin ya cire hular shi da takalma ya fasa tafiyar, ko farfajiyar gida babu wanda ya lek'a a cikin su suna d'aki suna soyayyar su, hatta abinci sai dai ya kira Bilyamin ya siyo ya kawo mu su, haka dare ya yi amma Haseenah na jikin Usman, da ya yi maganar tafiya wajen Baba za ta fara shagwab'a wai zai barta ita kad'ai, haka ya k'arar da wunin na shi bai je kiran Baba ba kuma bai kira shi a waya ba.

Tunda malam ya ga shiru ya tabbatar da zargin shi na cewa akwai abin da ke damun Fodio, ganin har dare ya yi anyi shirin bacci ya sa malam samun Hajia a d'aki har ta fara bacci ya tashe ta, saida ta wartsake yace "Bacci fa bai kama ki ba, tashi ya kamata ki yi mu duk'ufa da addu'a, dan shakka babu Fodio ba kan shi d'aya ba."

Saida ta k'ara murza ido tace "Malam, ban gane ba, me ya ke faruwa da Fodio kuma?"

"Shiga gaba." Ya bata amsa kai tsaye kafin ya d'ora da "Na yi mamakin da ku ka kasa fad'a min gaskiyar abin da ya faru a gidan shi, kun fad'a min ta karb'i makulli da k'arfi, amma ba ku fad'a min ta karb'a bane saboda za ta kai Bilal asibiti, yaron da aka barwa Haseenah ya wahala saboda babu mahaifiyar shi nan, sannan shi kuma Fodio bai fad'a min ya daki Khadija ba, ke ma kuma ba ki fad'a min ba."

"Duka malam?" Ta fad'a da dafe k'irji, d'orawa ta yi da "Wallahi ban sani ba ni ma, bai fad'a min ba ko alama."
Chapter 56 · 0% Book details