← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 86

Sashe 38

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da gari ya yi haske Khadija ta shiiryawa Bilal abun kari ya ci, shiryawa ya yi Baban shi ya tafi kai shi islamiyya, daga nan kuma asibiti ya wuce ya samu jikin malam da sauk'i sosai ya na ta hirar shi akan gado, ya na dawowa ya gida ya sake kwanciyar shi , Khadija kuma ta shirya dan zuwa ganin Baba, ganin shiru babu wanda ya mata magana ya sa ta kira wayar shi, a lokacin Haseenah ta gama soya k'wai da dankalin turawa ta shirya cikin ado mai kyau, ta na ganin kiran amma ta yi banza da ita, ta na ji ta na gani ta hak'ura da tafiyar sai Hajia ta kira ta tambayi mai jikin tace za ta shigo anjima.

Wani abun haushi shine a lokacin Haseenah ta tashi Usman daga bacci wai sai ya kaita asibiti ta ga Baba, tun ya na cewa bacci ya ke jin har ya wartsake ya tashi ya yi wanka ya shirya, wajen tebur suka nufa su ka cika cikin su kafin yace su tafi, *11:00* cif suka fita daga gidan ba tare da sanin Khadija ba, dan lokacin ita ma har bacci ya d'auke ta daga nan haka ma Uwani saboda shirun ya yi yawa.

Da isar su asibiti ta samu su Hassana zaune a bakin wata bishiya akan tabarma su na ta hira, nan ta zauna suka fara gaisawa, Hajia da ke tsaye da buta a hannu ce ta fara cewa "Yo ina Khadija? Ai na d'auka tare za ku taho tunda ta kira ni."

Kalar Haseenah ta sani kam sai cewa ta yi "Aunty ai ta na gida bacci ta ke, watak'ila sai da rana ta taho."

"Uhum." Cewar Hajiar ta wuce sabgar gaban ta, Rabi'a ce ta fara cewa "Hum! 'Yar hutu ce kinsan, kuma shi ba zai iya tashin ta ba saboda gudun b'acin ran ta."

Husseina ce tace "To kinsan da haka ma miye na wahalar da bakin ki wajen fad'a."

Hassana ce ta kalli Haseenah tace "Haseenah dai ki dage sosai kinji ko da addu'a, kar a shantake ayi ta bacci, dan matar nan da ki ke gani ba Allah ne a gaban ta ba, ke ma wallahi watak'ila tsananin rabo ne ya shigo da ke gidan, tunda ba tun yau ake mi shi maganar k'ara aure ba, amma da an mi shi maganar yanda ki ka san ka zagi uwar shi da uban shi haka ya ke kallon ka, mufa har saida ta kai ya daina sakar mana fuska."

Murmushi Haseenah ta yi tace "Insha Allahu su aunty babu abin da zai faru, Allah ai ba azzalumin bayin sa bane."

Husseina ce tace "Allah sarki yar albarka, Allah ya kare ki daga sharrin ta."

"Ameen." Ta fad'a da murmushi, mik'ewa ta yi tace "Bara na shiga na ga jikin Baban."

Ledar bayan ta ta janyo mai d'auke da kayan marmari kala kala ta d'auka ta wuce, da kallo su ka bita kafin Hassana tace "Wallahi yarinyar tausayi ma take bani, sukuku da ita ba kazar kazar."

Rabi'a ce ta yi tsal tace "Ai ba ki ga abun tausayi ba sai randa mu ka je gidan shegiyar nan ta kusa k'ona ta, wallahi inda kinga ta ma bud'e baki ta yi magana kasawa ta yi sai da k'yar."

Haka su ka ci gaba da tattaunawa har suka fito su ka mu su sallama suka koma gida, saida ya wuce ya d'auko Bilal dan lokaci ya yi kafin su ka wuce gida, k'arar bud'a k'ofa ne da mai gadi ke yi ya sa Khadija farkawa, ta ga motar Usman ce sai dai ba ta ga tare da wa yake ba, Bilal na shigowa ya tabbatar mata da shine ya d'auko, d'aki ya wuce dan cire kaya Khadija kuma ta kalli Uwani tace "Bara na shiga madafar da kai na idan bata fara aiki ba na d'ora mi shi ko indomie ce."

"To." Ta fad'a ta bita da kallo, ba ta samu kowa ba dan haka ta shiga abin da ya kawo ta da gaggawa, saida ta kammala ta fito dan d'auko farantin da za ta zuba, Bilal ta gani ya fito daga d'akin da da ledar bredi a hannu da gwangwanin madara, da sauri ta nufe shi ta karb'e madarar ta na fad'in "Sau nawa zan fad'a ma ka ba na son ka na anfani da madarar nan haka kawai idan ba a cikin shayi ba."

Cikin kukan shagwab'a ya biyo bayan ta ya na fad'in "Mummy yunwa na ke ji fa, ki zuba min ko kad'an ce."

Juyowa ta yi ta kalli Uwani tace "Uwani taimaka dan Allah d'auko faranti a d'akin can ki juyo indomien da na dafa."

"To." Dai ta sake fad'a ta nufi d'akin, Khadija dawowa ta yi ta zauna akan kujera tace "Zauna yanzu Uwani za ta kawo ma ka indomien ka ka ci."

Cikin turo baki ya aje bredin ya zauna in da ta nuna masa, Uwani kuma na shiga ta samu Haseenah tsaye ta d'auki indomien nan ta na juyeta wajen da ake zuba ruwan datti, da sauri tace "Kai, aunty amarya Umman Bilal ce ta dafa ta yanzu."

A wani gatsine ta juyo ta kalle ta tace "Wacece hakanan kuma?"

Shiru Uwani ta yi dan ba ta san me za tace ma ta ba, hakan ne ya sa Haseenah zuwa ta shak'i wuyan rigar Uwani tace "Me na fad'a mi ki? Bance ba na son sake ganin ki a madafar nan ba idan ina girki? K'azama da ke kawai ki dinga cud'anya cikin mu sai kace kema wata matar shi ce, dallah fice min daga nan."

Yanda ta tura Uwani da k'arfi sosai ya sa ta yi baya kan ta ya had'u da bango, fitowa ta yi dafe da kan ta ta samu Khadija ta fad'a mata komai, Khadija ta so ta yi magana kan abin da ta yi sai kawai ta share ta sa Uwani ta d'auko gas d'in ta suka kunna, ruwan d'umi ta fara d'orawa Bilal ta had'a mi shi shayi sannan ta sa Uwani ta d'ora tukunya ta je madafar da kan ta ta d'auko duk abin da take buk'ata suka d'ora na su girkin.

Haseenah na ganin haka ta shiga d'akin ta ta samu Usman kwance da waya ya na dannawa, cike da nuna b'acin rai ta yi tsaye tace "A gaskiya abin da ake min ba na jin dad'in shi ko kad'an domin Allah."

Zaune ya mik'e yace "Me ya faru kuma? Waya tab'a min zinariya ta?"

"Ba na son tashin hankali da rigima, ina so na zauna da kowa lafiya, amma aunty Khadija ta na so ta kawo wata b'araka a tsakanin mu ta hanyar raba girkin ta da nawa, saboda Allah ba dan neman magana me zaisa ta d'ora girkin ta bayan ga shi can na d'ora?"

Da d'an mamaki ya kalle ta kafin yace "Amma ai na d'auka na hana ta, me ya sa ba ta ji abin da na fad'a ba."

Hanyar fita ya yi yace "Je ki ci gaba da aikin ki, zan je na gani da kai na."

Kai tsaye b'angaren Khadija ya nufo, ya na zuwa bai same su a wajen ba amma tukunya na saman gas, ai kuwa kamar hauka sabon kamu sai ya sa k'afa ya hanb'are tunkuyar, k'arar dungurawar tukunyar ne ya sa Khadija da ke falo suka taho a guje ita da uwani dan ganin meya faru, ganin Usman tsaye ya na huci ya sa Khadija kallon shi da mamaki tace "Abban Bilal, lafiya? Me ya faru?"

Da yatsa ya nuna ta yace "Ban fad'a mi ki kar ki sake d'ora min girki a gida ba in har ana girki? Ko raina ni ne ki ka yi shi ya sa ba ki d'auki abin da na fad'a da mahimmanci ba."

Cije leb'e Khadija ta yi ta rintse ido lokaci d'aya kuma ta bud'e ta kalle shi tace "Na ji, ka yi hak'uri ba za'a sake ba."

"A sake ma a gani, wallahi ran ki zai b'ace, aikin banza kawai mace ba ka isa ka fad'a mata ta ji ba." Duk ya yi maganar ne ya na komawa in da ya fito, Uwani ta kalla tace "Ki gyara wuri ki mayar da komai muhallinsa."

"To." Uwani ta fad'a jiki a matuk'ar sanyaye dan ba ta yi tunanin shine ba, falo Khadija ta zauna zuciyar ta na suya, wani b'angaren kuma kamar ta fashe da kuka amma ta na tausar zuciyar ta, dan in har abin da take tunani shine ke faruwa a yanzun, to fa zaifi ta adana hawayen ta dan zasu fi mata anfani nan gaba kad'an, haka suka zauna jugum da su Bilal har ya yi bacci ya tashi saboda lokacin islamiyya ya yi, har ya shirya ya yi sallah babu abinci daga wajen Haseenah, Usman kuma tunda ya gama masifa ya bar gidan har yau bai dawo ba, suna zaman jiran shigowar shi sai ga shi ya zo, Bilal ne ya fita ya same shi a farfajiyar gidan yace " Abba na shirya lokaci ya kusa."

Shafa kan shi ya yi yace "Yarima har ka shirya? Gashi kuma yunwa na ke ji yanzun, amma muje na aje ka na dawo."

Shiga su ka yi ya fara baya-baya ya na fad'in "Da alama sai na samar ma ka dreba (driver), dan Bilyamin ma ka ga aure zaiyi, ba za mu dinga takura shi ba wajen kai ka makaranta idan bana nan."

K'ala Bilal baice ba har ya sauke shi a makaranta, juyowa ya yi ya dawo gida, Khadija na ganin mai gadi ya bud'e ma sa k'ofa ta fito, tsaye ta yi har ya fito daga mota ya kalle ta yace "Lafiya dai?"

"Lafiya lau, dama akan maganar duba jikin Baba ne, ka ga har yamma tayi ba mu je ba, shine na ce ka mana izini mana idan na kammala girki sai mu tafi da ita ba sai mun jira ka ba."

Cike da rashin damuwa yace "Kar ki damu, kije kawai idan kin gama, ita ta tafi tunda safe ai, ni na kai ta."
Chapter 38 · 0% Book details