← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 86

Sashe 80

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun da bai tab'a faruwa ba shine yau ya faru, cikin d'aga murya tace "A'a malam, kar ka sake ganin laifin ta akan zunubin da 'yarka ce ta aikata shi, wannan yarinyar babu abin da ta aikata, kaga mai laifin nan gaban ka." Ta fad'a ta na nuna Haseenah wacce ta yi k'asa da kan ta, a tausashe yace "Me ki ke nufi da ba ita ce mai laifi ba Haseenah ce?"

Kujerar katako ta janyo ta zauna kusa da shi ta aje jakar hannunta gaban shi, nan ta zayyane mi shi duk abin da taji sun tattauna da kuma zuwanta gidan Khadija yanzu, cikin b'acin rai ya d'auki takalman shi ya tilk'awa Haseenah a baya gashi kam ba ta san da saukar takalman ba, ji ka ke timmm a bayan ta, k'ara ta saki ta dafe baya ganin ya d'auki d'aya takalman ya sa ta shura a guje d'aki, masifa ya dinga zazzagawa takaicin shi kud'in da ya kashe wajen amso mata magani, zagi ya dinga aika mata a d'akin ya na yi ya na kallon kayan da Khadija ta bado.

*Daga ranar* komai ya k'ara canzawa Haseenah, kaf gidan yanzu babu mai kallon ta da mutumci, girki da wanke-wanke ko ga yara a gidan ita ce ke yi, wani lokacin ma mahaifin su har kayan shi ya ke bata ta wanke mi shi, duk a ganinsu horon da za su iya yi mata kenan da zaisa ta shiga hankalinta, wani abu dake damun Haseenah sosai shine rainin da duka k'annan ta suka aza mata, ko kallon su ta yi sai ka ga wata ta kwad'a mata harara, haka kullum take cikin fad'a ita da k'annan ta, ga ciki na ta girma sosai ga kuma rashin kud'i, idan ta tafi awo kad'ai take jin dad'i duk da rashin kud'i ya sa ta canza asibiti, yanzu haka ta na awo ne a asibitin da ke kusa da su asibitin *Ali Chaibu*, a haka ta yi laushi sosai take k'ara nadamar abin da ta yi, gashi Usman ko kiran ta bai tab'a yi ba bai kuma tab'a zuwa ba da sunan ya ganta, ya je sau biyu amma wajen mahaifin ta ya tambayi komai lafiya suka gaisa ya tafi, sai dai duk sati biyu yakan aiko Bilyamin ya kawo mu su kayan abinci da kud'i saboda bebyn shi, har yanzu babu abin da ya rage daga jikin ta na k'iba da ta yi, sai dai fatar ta ta canza sosai ba kamar da ta na gidan ta ba, dan kuwa duk kayan da zai aiko iyayen ta sukan zama na anfanin duka gidan ne, kud'i kuma sai in za ta tafi asibiti ake bata wanda basu taka kara sun karya ba.

Duk lokacin nan da aka d'auka a wajen Khadija ita ma ta matsa lamba sosai kullum maganar Haseenah take wa Usman, ta yi rarrashin duniya ta yi kissar ta yi nisihar amma ya mayar da ita kamar mahaukaciya, akan maganar nan har fad'a su ka yi suka daina magana tsawon kwana uku, saida Bilal ya shirya su kad'ai suka koma magana, amma fa ba ta daina mi shi maganar ba, har tsawa ya mata ya zare mata ido yace idan ta na da zuciya ta daina mi shi maganar Haseenah amma tace ba ta da zuciya in dai akan maganar nan ne, haka kawai take jin zuciyar ta na yin sanyi kullum take son ganin ta dawo gidan ta, ta fad'a mi shi ya sake bata dama ta biyu mana tunda 'yar adam ce ita, amma abun baiyi tasiri ba, har Bilal ta sa ya rok'e shi take yace ya fita a harkar manya ba ruwan shi, izuwa yanzu kanta ya yi zafi akan maganar, hakan ya sa ta samu malam ta kalallame shi sosai, kuma ta yi sa'a ya gamsu da abin da ta fad'a sosai, alk'awari ya mata zan mi shi magana, kuma kamar yanda ya fad'a ya wa Usman magana, amma sai yace shi fa in aka sake matsa mi shi to zai bar mu su garin ita ma Khadijar ta koma gidan su, wannan magana ita tasa malam cewa "A'a Fodio, me ya yi zafi haka, Allah ya huci zuciyar ka, shikenan tunda ba ka so ai."

Cikin b'acin rai yace "Baba Khadija hankali ne bai ishe ta ba, in ba haka ba yarinyar da ta cutar da ita da ni da ku ma amma wai ta dage kai da fata sai an dawo da ita, to tsiyar me za ta mana idan ta dawo?"

Malam dai cewa ya yi "Yi hak'uri to shikenan, zam fad'a mata ta yi hak'uri kawai a bar maganar, Allah ya sa haka shi yafi zama alkairi."

Malam da kan shi yaje har gidan ya fad'awa Khadija dan Allah ta manta da maganar Haseenah ta kula da mijin ta kawai, ba dan haka ta so ba ta nuna shikenan ya wuce, saida malam ya fad'a mata yace idan an sake takura shi fa zai bar gari ne, kai kawai ta gyad'a alamar taji, da dare ko da Usman ya shigo ya na zaune a falon ta tare da Bilal suna kallo Khadija ta fito da kinkimemiyar akwati da cikin ta masha Allah ya fito sosai, saida ta zo gaban shi ta tsaya tace "Malam ni zan tafi gidan mu tunda ka kasa min alfarma d'aya, idan na haihu nima ka zo ka d'auki abin da aka haifa."

D'auke kan shi ya yi daga kallon ta ya na kallon telebijin kamar bai san ta na yi ba, juyawa ta yi da jakar Bilal ya zabura zai tashi Usman ya rik'e shi ya fad'a jikin shi, cikin kunne ya rad'a mi shi "Bari kaga yanda zanyi da ita, ko k'ofar gida ba za ta je ba."

Har ta kai bakin k'ofa amma ba ta ji ana tsayar da ita ba, juyowa ta yi ta kalle shi ta tsaya cak, cikin d'aure fuska ya sa hannu aljihu yace "Kai na manta, zo karb'i kud'in adaidaita mana."

Lalaba aljihu ya ke kafin yace "Hajia banda canji, karb'i makullin mota ta ki tafi da ita gobe zan je na d'auko."

Ya k'arashe maganar da jefa mata makullin gabanta, haushi ne ya kamata sosai ta d'auki makullin ta juya ta fita, a hankali take tafiya da tunanin ko zai zo ya hanata amma shiru, k'wafa ta yi ta juyo da sauri cikin jin haushi ta dawo falon, zaune ta same shi yanda suke hankali kwance suke kallo, da sauri ta k'araso wajen shi ta d'auki akwatin dama ba komai ciki ta jefa mi shi a jiki tana fad'in "Hamago kawai, kenan dama so ka ke na tafi na bar ma ka gidan saboda ka gaji da ni ko? To babu in da zanje wallahi mutu ka raba ni da kai, sai na yi takabarka da yardar Allah."

Tunda ta fara magana Usman ke dariya har da d'aga k'afafu ya na rik'e ciki, d'auke akwarin Bilal ya yi ya shiga d'akin ta da shi, Usman na ganin haka ya fizgota ta fad'a jikin shi ya rumgume ta yace "Ke a haukanki kin d'auka zan zauna hakane har ki bar gidan nan? Ai kafin ki isa gida zansa a sato min ke a dawo da ke."

Cikin kukan shagwab'a ta kalke shi tace "Abban Bilal dan Allah kayi hak'uri ka dawo da ita, wallahi tausayi take bani sosai inna tuna rayuwar da take, wannan ita kad'ai ce alfarmar da na ke nema a gurin ka, ka taimaka ka dawo da ita gidan nan mana ta haihu gidan mijin ta, kullum ina aunata da kaina sai naga idan ni ce ya zanyi ace zan haihu gidan mu, babu dad'i ko kad'an wallahi, dan Allah babban mutum ka taimaka mata kaji, na maka alk'awarin za mu zauna lafiya da yardar Allah."

Tun tana magana ya mayar da kallon shi ga telbijin, saida ta gama ya kalle ta yace "Khadija me ya sa ki ke son takura min akan magana d'aya? Me zaisa ba za ki bar maganar ba tunda har na ce ba na so? Me ta mi ki a rayuwa na alkairi da har ki ke son dawo da ita cikin rayuwar mu?"

Cikin muryar tausayi tace "Wallahi babu komai, na dai fad'a ma ka dalili na kawai, Abban Bilal shekara nawa mu ka d'auka muna neman haihuwa, amma zuwan Haseenah gidan nan sai gashi Allah ya azurtani da nawa cikin nima, watak'ila hakan ya faru ne saboda hak'urin da mu ka yi da kuma tsarkake zuciya ta da na yi wajen zama da ita, ba ka tunanin yanzu idan na sa ka dawo da ita Allah ya sake mana wata rahamar ta hanyar da ba mu yi tsammani ba?"

Ganin ya yi shiru alamun maganganunta na ratsa shi ya sa tace "Za ka iya tuna a cikin karatun da ka ke koya mana kai ka bamu labarin abin da ya faru tsakanin *sayyidi na Abbakar* da *musd'ahu* mai hidima gare su kuma wanda su ke d'aukar nauyin shi, Musd'ahu na d'aya daga cikin wanda suke yayata k'azafin da akawa *Nana Aisha (RA)* cewa ta yi zina, a lokacin da ran sayyidi na Abbakar ya b'aci ya kori Musd'ahu daga gidan shi tare da cewa ba zai sake d'aukar nauyin shi ba, me Allah yace akan haka, Allah ya na son masu yafiya, idan ka yafe kuma sai ka manta da komai, sannan ka k'ara da kyautatawa, to hakanne ya kamata ya faru a yanzu, ka yafe mata gaba d'aya, sannan ka manta da abin da ya faru ka daina tunawa, kyautatawar da za ka mata kuma bai wuce ka dawo da ita d'akin ka ba ta haifi abin da ke cikin ta ba ta kuma raine shi gaban ka, kar kaga ka na keyawa da masoyan ka za su kula maka da d'an da za ta haifa, rik'on yaro sai uwar shi, duk wanda kaga bai rayu da mahaifiyar shi ba dan hakan na mi shi dad'i bane, dan Allah miji na, Usman na Nana, ka saurari matarka mana ka tuna had'uwar ku ta farko da ita da kuma yanda zaman ku ya kasance, saika yanke hukunci."
Chapter 80 · 0% Book details