← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 86

Sashe 43

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da Usman ya je gidan ya samu iyayen Haseenah har sun zo suma, nan fa mahaifin ta ya nuna ba zai yarda a illata mi shi yarinya ba akan namiji, dab haka yace dole sai an kewaya Qur'ani a gidan, duk wanda ya cutar da wani to Qur'ani ne zai ci shi,😂 (tirk'sahi, Haseenah kin jawo bala'i), da k'yar mahaifin Usman ya rarrashe su ya basu hak'uri yace su bar komai a hannu shi zai d'auki mataki, saboda baya so cin zarafi ko mutumci ya fara shigowa lamarin, sun hak'ura amma sun ce dole a binciki gidan dan ga dukkan alama wani kafi ne a ciki da zai hana ta zama, sun yarda da hakan sosai dan haka ma suka ce zasu tura 'yan uwan Haseenah mata su je su duba.

Hassana da Husseina aka kira suka zo gidan, nan aka fad'a mu su abin da ya faru da wanda zai faru a gaba, gidan Usman suka nufa tare da Haseenah da ta yi shiru ta kasa magana.

Khadija na girkin rana a lokacin ta ga Mariya da kuma *Razina* sun shigo duk da ba ita ce aikin ba, cikin sakin fuska da mutumtawa suka gaisa sosai, ganin za su wuce ciki tace "Ina ga fa ba ta nan, ta fita ina jin."

Mariya ce tace "Eh mun sani, ta na nan ma zuwa yanzu."

"Ahan." Cewar Khadija ta ci gaba da aikin ta, ta na kusan gamawa kuma sai ga Haseenah tare da su Hassana, suma saida su ka gaisa kafin Khadija ta kalli Haseenah tace "Ke haka ake sai ku fita cikin dare babu wanda ya sani, saida safe ya ke fad'a min wai ba kya nan."

Kamar za ta yi kuka tace "Ki yi hak'uri dan Allah." Ta na fad'a ta wuce falon ta.

Kallon su Hassana ta yi tace "Ba ta da lafiya ne na ganta wani iri haka? Ko daga asibiti ku ke?"

Cikin d'age kai Hassana tace "Lafiyar ta lau." Ta na fad'a ita ma ta yi gaba sai Huseeina da ta bi bayan ta, su na shiga Hassana ta zauna kusa da Haseenah ta dafa ta tace "Haseenah, ki fad'a mana gaskiyar abin da matar nan take mi ki kinji?"

Girgiza kai ta yi tace "Ba komai."

"Kin tabbatar?" Cewar Mariya da suka zagaye su, shiru ta yi sai Hassana ce ta kalle su dukan su tace "Ku na ji ko, gaskiya dole a d'auki matakin kare yarinyar nan kafin ta cutar da ita, kunga fa yanzu nuna mana ta yi kamar ba ta san me ke faruwa ba, har da tambayar ko ba ta da lafiya ne kuma daga asibiti mu ke, dan haka Haseenah sai kinyi taka tsantsan sosai."

Husseina ce tace "Gaskiya wannan rashin tausayi da imani ya yi yawa, ace yarinya ko sati biyu ba ta cika ba amma ki na so ki fitar da ita daga gidan, wannan ai zalinci ne, shikenan fa so ta ke ta mayar da ita k'aramar bazawara."

"Haseenah ki na da ciki ne?" Da sauri ta kalli Razina da ta jefo mata tambayar, cikin rashin sani tace "Ban sani ba ni ma."

Hassana ce tace "To ko kin sani kar ki yarda ki bari ita ma ta sani, ko ki na ganin alamu kar ki bari ta gane tunda kinga ta fiki wayo, dan wallahi tasan da ciki jikin ki sai ta kusa kashe ki."

Mariya ce tace "Kisa fa ki ka ce?"

Cike da tabbatarwa tace "K'warai kuwa, ki na ganin ba ta iya wa ne? Wacce suka kwashe shekaru kullum da d'a k'waya d'aya, samun cikin Haseenah fa alama ce ta za ta fara hayayyafa gidan Usman, kinga kuwa dole a d'auki tsatsauran mataki."

"To Allah ya raba mu da sharrin wannan mata mu dai." Cewar Razina.

"Ameen." Su ka ji an amsa daga bakin k'ofa, wa za su gani in ba Khadija ba da kwanukan abinci tsaye, fik'i-fik'i su ka kama da ido cike da rashin gaskiya, cikin takon izza da isa ta k'araso in da suke ta aje kwanukan ta d'ago ta kalle su d'aya bayan d'aya, murmushi ta yi da ya k'ara mata kyau kafin tace "Ina rok'on Allah ya kare ku daga sharrin na kamar yanda ku ka yi fata, wani abu d'aya da na ke so ku gane shine, da ace ina kishi da Haseenah kuma haukan kishi, to wallahi tallahi da miji na bai ma kula ta ba bare har ta had'a kafad'a da ni, da ace za fitar da ita daga gidan nan bayan ma ta shigo wallahi da ba ma zan bari ta shigo ba, dan in ta shigo ai za ta iya yin alfahari da hakan, sannan za ta ga abin da yafi komai daraja a jikin miji na, za ta kwanta akan shinfid'a shi kamar yanda zan kwanta, to miye anfanin barin sai ta shigo sannan na fitar da ita? Ai ba ma za ta shigo ba wallahi da na so hakan, ku ji da kyau."

Ta fad'a ta na kallon su dukan su, ci gaba ta yi da cewa "Idan na yi niyyar mallakar Usman ta hanyar asiri ku sani ina da kud'in da zan iya biyan boka ko da na k'asar india ne, idan har na tashi mallakar Usman wallahi zan mi shi mallakar da har mahaifiyar shi ba za ta anfane shi bane, idan mallakar Usman zan mallake shi cikin awa d'aya tak, kuma na hargitsa duk wani lissafi na shi, idan har na mallake shi to sai ya kai matakin da ko bayan gida zai zaga sai ya nemi izini na kafin yaje ga buk'atar shi, ku a matsayin ku na 'yan uwan shi wallahi sai ku zubar da hawaye kafin Allah ya had'a ku da shi akan hanyar har ku gaisa, dan haka ku daina kallo na a matsayin wacce ta mallake shi har take k'ok'arin fitar da wannan yarinyar, ba alfahari ba, amma zan iya cewa Haseenah ba ta kai macen da zan iya kishi da ita ba har na had'a ta da boka ko malam, ko ke ba ki kai matsayin ba." Ta fad'a da nuna Mariya da yatsa, gyara tsayuwa ta yi ta na murmushi tace "Wannan." Ta nuna labb'an ta da yatsa, "Da kuma wannan." Ta kama duka nonuwan ta a hannu, "Sai kuma wannan." Ta k'arashe da nuna k'asan ta da yatsa sannan tace "Su kad'ai ne su ka mallaka min zuciyar Usman a hannu na, tabbas sihiri zai iya anfani a kan shi ta hanyar saka shi ya ci zarafi na, amma idan ki ka ce ya rufe idon shi sannan ya saurari zuciyar shi, to ko shakka ba na yi cewa sunan *Khadija* ne za ki ji ya fito a bakin shi."

Hannu tasa ta ciro gilashin ta ta bushe shi da baki kafin ta mayar ta kalle su Hassana da Husseina tace " *Ku daina wa kitse kallon rogo* idan ku ka aika shi baki zai fahimtar da ku asalin me ye shi."

Juyawa ta yi ta fice abinta ta na jujjuya k'ugu cikin k'arewa tafiyar da sai oga ake wa ita amma yau sun saka ta gwada mu su, har saida ta b'acewa ganin su Hassana ta sa k'afa ta ture kwanon tace "Kar wanda ya ci abincin, dan ba mu san me ta saka ba."

Husseina ce tace "Kinji shegiya, wai so take ta nuna babu abin da take, to ai ko da ki ka ganmu da hak'oran mu talatin ki ka gan mu, dan haka sai ki fad'awa kaji amma zabbi hira suke."

D'akin Haseenah suka shiga in da suka duba lungu da sak'o ba su ga wani abu ba, layar da mahaifin ta ya bayar Mariya ta taka kujera ta jefata bayan ma'ajiyar kaya (drower) ta kalli Haseenah tace "Ko da kin canza zaman kayan d'akin kar ki jefar da abin can ki sake mayar da shi, Baba ne yace a aje na tsari ne."

K'ala ba tace ba har Mariya ta sake d'aga katifar fa a b'angaren hannun dama ta aje wata layar tace "Duk halin da ake ciki kar ki sake ki aza kan ki ba b'angaren da layar nan take ba, kinji ko?"

Da kai kawai ta nuna ta ji, har suka gama aiki su na hira akan Khadija da abin da ya faru, haka suka gama ko sanin tafiyar su Khadija ba ta yi ba, Haseenah na ganin tafiyar su ta d'auke dula layoyin ta nasa su cikin shara, ana haka yamma ta yi ta karb'i girkin ta a hannun Khadija, yau ma saida ta kammala girkin ta d'auki d'an banza gishiri ta zuba ciki, ta gama shiryawa tsaf ta aje komai a muhallin shi.

Kamar jiya yau ma ba su iya cin abincin ba, haka su ka yi 'yan dubaru kowa ya bar wajen, sai dai ran Usman ya b'ace sosai, hakan ne ya sa lokacin da ya shiga yi mu su saida safe, Haseenah kuma da ke son sanin me zai faru ya sa ta biyo bayan shi, ya na shiga d'akin ta tsaya bakin k'ofa ta na sauraren su, ya samu Khadija d'akin ta kwance, fuska ba fara'a yace "Dan Allah zan rok'i alfarma a wajen ki."

Tashi ta yi zaune ta d'auki gilashin ta ta saka kafin tace "Alfarma kuma Abban Bilal, sanin kan ka ne kafi k'arfin kowace irin alfarma a waje na, fad'i kan ka tsaye insha Allahu zan ma ka idan da hali."

Saiwa ya gyara tsayuwa yace "Ba na son sake jin wani abu a cikin abinci idan 'yer uwar ki ta dafa, tunda na lura abun akwai almubazzaranci a ciki, kar fa ki manta kud'i na ke sawa ina siyo abincin nan, kar ku ganshi a zube kamar kayan banza dan an zube mu ku na shekara, ba ku tunanin akwai wanda na safe ma sai sun nemo? To ba na so daga yau, kar a sake kinji na fad'a mi ki."

Juyawa ya yi da fad'in "Saida safe." Da gudu Haseenah ta juya ta koma d'akin ta ta kwanta ta na haki, ya na fita Khadija ma shiru ta yi ta na tunani kafin daga bisani zuciyar ta ta hasko mata mafita ita ma, murmushi ta yi ta kwanta abinta bayan ta sake shafe jikinta da addu'a.
Chapter 43 · 0% Book details