← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 86

Sashe 58

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh Hajia, ya na ina ne Nuran?"

"Ya na shago mana."

"Shikenan zan kira idan na fita saiya same ni ko can shagon Murtala ne."

Cikin had'e tafukan hannayenta tace "Hakan ma ya yi."

Kallon ta ya yi yace"Hajia me zai hana ku je ku d'auko Bilal?"

Sai lokacin ta kalle shi tace "Ban gane na je ba? Kai me zai hana ka tafiya? Kuma ma ka na nufin ba za ka je ka dawo da mahaifiyar shi ba kenan?"

Cikin b'acin ran an ambaci sunan Khadija yace "Hajia ni babu in da zanje, ita ta tafi saboda ta na so, dan haka taje can ta k'arata, ni yaro na ne kawai matsala ta."

Karo na farko a rayuwa da Hajia ta iya d'agawa Fodio murya, cikin jin haushi tace "To ba zan je ba, ranar da ka shirya ganin d'an na ka sai kaje ka d'auko shi da kan ka."

Kallon ta ya yi shima, amma saboda ran shi a b'ace ya ke da maganar Khadija sai kawai ya mik'e cikin kumburo baki yace "Ni zan wuce, sai anjima."

Da kallo kawai ta bi shi har ya fita daga gidan, girgiza kai ta yi ta na mamakin wannan canjin daga Fodio, mik'ewa ta yi ta shiga d'aki ta na fad'in "Ai kuwa da alama gaskiya malam ya fad'a, amma koma menene zan wa tubkar hanci."

Daga nan wajen malam ya zame, k'ofar shagon ya samu malam zaune akan bacci shi da wani suna hira, har k'asa ya durk'usa ya gaishe su kafin malam ya sallami waccen, mayar da kallon sa ya yi kan Usman da ke durk'ushe yace "Fodio sai yanzu ka zo kiran nawa? To nagode."

"Wallahi Baba..." D'aga mi shi hannu ya yi alamar ba ya son ji kafin ya d'ora da "Jiya na je gidan su Khadija, kuma naji duk abin da ya faru, Fodio ka bani mamaki sosai da na ji ance wai ka d'aga hannu ka daki Khadija, wannan abun kunyar har yaushe da irin shi, duka! Kai a matsayin ka na mai hankali da ilimi, a shekarun ku na k'uruciya haka ba ta faru ba sai yanzu da girma ya fara riskar ku, wanda ya kamata ace yanzu ne soyayya take da tausayin juna, amma ace ka dake ta akan abin da ma k'arya ake mata da sharri, kawai rud'in zuciyar ka ne ka biyewa da kuma wata banzar hud'uba da wasu sakarkari suka ma ka, kasan me ya sa ta karb'i makullin motar? To saboda ta kai yaron ka asibiti ne, yaron da ya wuni da yunwa alhalin ya na gidan uban shi wanda ke wadace da kayan abinci sama da na shekara d'aya, amma wai akan hakane har ka d'orawa baiwar Allah laifi har ka iya dukan ta, ni ko a gani na ko taka Haseenah ta yi ta mayar da gabanta gabas ta yanka ta da wuk'a za ka iya mata uzuri, uzurin kuwa shine za ka duba dalilin da ya sa ta yi haka tunda ita uwa ce, amma ba komai, ka je gidan ka gani yanda ka lalata mata fuska da rashin hankalin ka, tace ba za ta dawo ba kuma na yarda da abin da ta fad'a, dan haka kaje kai da amaryar taka ku cinye kan ku, amma ka sani wallahi Fodio ina jin tsoron ranar da za ka yi nadama, dan alamu sun nuna *kallon kitse ne ka ke wa rogo*, tashi ka bani wuri."

A hankali Usman ya d'ago kai ya kalle shi tabbas ran shi ya b'ace sosai, cikin taushin murya yace "Dan Allah Ba..."

"Nace ka tashi ka bani wuri ko." Cewar Baba, mik'ewa ya yi ya juya zai shiga mota malam yace "Ji nan." Juyowa ya yi ya matso ya sake zubewa durk'ushe, d'orawa ya yi da "Har yanzu ita matar ka ce, kuma d'an ka ya na tare da ita, ban kuma yarda ka ce za ka d'auko yaron nan ba saboda banga alamar zai samu kulawa ba, dan haka umarni ne daga gare ni ya zama wajibi a wajen ka kai mu su kayan abinci da basu kud'in da za su yi sauran buk'atun su, ka ji da kyau?" Ya fad'a da kama kunnen shi.

Cikin sunkuyar da kai Usman yace "Na ji Baba."

"Tashi ka b'ace min da gani." Cewar malam ya na gyara zaman shi, tashi ya yi ya shiga mota ya wuce kamar zai fasa ihu saboda sharudd'an malam, amma kuma ba yanda zaiyi dole ne ya yi hakan d'in.

Yamma sosai Haseenah na kwance d'aki ita kad'ai Mariya ta kira ta, bayan sun gaisa ne take tambayar "Wai ni kam ya ku ka kare da rigimar ku da matar nan? In ce dai Usman ya d'auki mataki?"

Wata shak'iyar dariya ta yi tace "Ai tuni ta kama gaban ta, yanzu haka ni kad'ai ce a gidan, kwananta biyu yau ba ta gidan."

Daga d'aya b'angaren Mariya tace "Ke Haseenah! Da gaske ki ke?"

"Eh mana, zan mi ki k'arya ne?"

"A'a, amma Haseenah ki na ganin abun baiyi yawa ace ta bar gidan?"

"Baiyi ba, tunda ba ni na fitar da ita ba, bansan akan me su ka tattauna ba da har ta bar gidan, kuma shi ma ba na tunanin shi ya kore ta tunda har na ji yace tunda haka ta zab'a matsalar ta ce."

Cikin sanyin jiki Mariya tace "Toh, yanzu me ye abunyi? Ba za ki bashi hak'uri ba ya dawo da ita tunda ya na jin maganar ki yanzu."

Ba tare da tunanin komai ba tace "Abin da na ke so yanzun bai wuce ki zo gida ki same ni ba na baki kud'i ki kaiwa malamin nan ya sake mana wani aikin."

"Wani aiki kuma?" Ta fad'a da k'arfi, cikin sassauta murya tace "Idan fa ta dawo da matsala, so na ke kawai ta ci gaba da zama acan har mala'ikan mutuwa ya same ta."

Cike da gargad'i Mariya tace "Ke Haseenah ba ruwa gaskiya, me ya sa za ki yi haka? Me ya yi zafi? Na ga dai Usman ne kuma kin same shi, ina ganin ai zafi idan ta na gidan za ki fi k'unsa mata bak'in ciki, amma a dawwamar da ita a gidan su gaskiya abun ba dad'i."

Cikin gaggawa tace "Kinga, kedai idan kin samu dama ki zo gidan ki same ni sai muyi magana."

Shirun da Mariya ta yi ne ya sa Haseenah cewa "Ki na ji na?"

Abin da ta lura a lamarin na Haseenah shine akwai alamun rashin kunya, amma saita dake tace "Shikenan na ji, idan na fita gobe siyan kaya zan biyo."

"Ok." Kawai ta fad'a ta kashe wayar, nan ta ci gaba da zama har saida aka kira sallah magrib ta fito, kuma kamar yanda su ka yi da Usman bai dawo sai bayan isha'i, lokacin ta shirya sosai dan dama da kayan kwalliyar ta a cikin jaka, daga nan restaurent *Kebab* suka nufa cin abinci, rayuwa kenan, rayuwa ta juyowa Haseenah kam yanda ta ke so, gashi kuma ta na garata son ran ta, daga nan ma *plaza* su ka wuce suka siyi ice crime da sauran kayan mak'ulashe kafin su ka wuce gida, wangale k'ofa mai gadi ya yi amma ko kallo bai ishi dukan cikin su duk da gaisuwar da ya ke mu su, girgiza kai ya yi cike da takaici kafin ya rufe k'ofar.

*Washe gari* bayan fitar Usman Mariya ta zo gidan, bayan Haseenah ta bata kud'in ta mik'e za ta fita, gwangwanin madara ta gani na *lacstar* aje, kallon ta ta yi tace "'Yar k'anwar tsakura min mana ko a leda ne na d'an kaiwa 'ya'yan ki."

Cikin b'acin rai tace "Ba fa na san haka gaskiya, jiya ne fa na fasa madarar nan, idan na ce na dinga rabarwa ai ba za ta min ko sati ba."

Waro ido ta yi tace "Sati fa? Yanzu wannan sai ki shanye ta a sati ke kad'ai?"

Wata irin dariya ta yi kafin tace "Ai kamar kunu haka nake damata ina sha, kuma shine yace ta zama abinci na saboda ya na son ganin yaron da zan haifa kamar d'an turawa." Ta k'arashe da shafa cikin ta, tab'e baki Mariya ta yi tace "Yanzu ni dai sammin na tafiya ta."

Saida taja tsaki kafin ta samo 'yar leda ta zuba mata cokali uku ta mik'a mata ta na fad'in "Karb'i nan ta isheki, ba na so yace ina almubazzaranci da kaya wallahi."

Ganin 'yar madarar da ta zuba mata ya sa ranta b'acewa ta aje tace "Ki had'a kawai kisha, Allah ya raba lafiya."

Ko a jikin ta ita kam har suka fito farfajiyar gidan Mariya tace "To ai kya bani ko na adaidaita ko?"

'Yar k'aramar jakar hannun ta ta nuna mata tace "Kin ganta wallahi k'ananan kud'i a ciki ita ce jaka biyu (maybe dubu d'aya yanzun, dan farashin kud'in ya sauya), amma ki bari idan ki ka dawo daga wajen malam d'in saina baki."

Saida ta kalle ta sama da k'asa ta fice ko sallama ba ta mata ba, tun a hanya Mariya ta yanke hukuncin ba za ta je wajen malam d'in ba tunda ta lura iskanci ne abun na Haseenah, dan haka ma ta wuce gida kai tsaye ta fara tunanin abinyi da kud'in wanda zai anfane ta, a k'arshe ma dai jarin ta ta k'arawa yawa wajen k'ara siyo wasu kayan gwanjo.

Yamma lik'is saiga Bilyamin ya sallama gidan su Khadija nik'i-nik'i da kayan abinci da na masarufi, hakan baiwa mutanen gidan dad'i ba saboda a ganin su za su iya ciyar da kamar Khadija d'ari ma bare ita kad'ai, amma da Mama ta fahimtar da su sai suka mayar da wuk'ak'en na su, in da Khadija kuma tunanin ta kenan ba zai zo ba ya na nufin na yi ta zama a gida.

Gida Usman ya koma dan sanar da su ya tattauna da Nura kuma za su je neman masa aure, har d'aki ya samu iyayen na shi ya sanar da su yanda ake ciki, ya d'an jima suna tattaunawa akan lamarin kafin ya fara yunk'urin tafiya, "Karb'i nan."
Chapter 58 · 0% Book details