← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 86

Sashe 47

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da k'yar dai wanda ke mu su shari'a yace kar ta sake zuwa gidan shi, kuma kar wani abu ya samu matar shi, in ba haka ba za ta shiga hushin hukuma, bud'ar bakin ta cewa ta yi "Wallahi kunji na rantse ko, da ace nasan in da ake siyar da k'ank'arar mayu to da na siyo ba dan komai ba sai dan na lashe matar ka, ka sani ba zan sake zuwa gidan ka ba, amma wallahi tallahi na had'u da matar ko sai na ci kakan..., tunda tace ma ka na yi abin da banyi ba kuma ta lak'awa k'awa ta sharri ko, to ba makawa sai ta samu shaidar sanin Hajia Turai, ka dube ni da kyau Usman kai ka sanni, wallahi k'aramin aiki na ne na keta yarinyar nan da wuk'a, kuma a shirye nake da na je duk kotun da aka kira ni dan shari'a akan ta, banzaye kawai daga kai har ita."

😂 _Allah ya kyauta._

Nan aka raba su kowa ya kama gaban shi, amma fa Hajia Turai ta zuba ido da kunne ta na jiran ta ji wani sabga da zai taso wanda zaisa ta had'u da amaryar Usman, Usman kam tunda ya shiga mota ya kifa kan shi yake jin zuciyar shi babu dad'i haka ma yanayin shi, wai me ya faru da shi da har ya aikata wannan abun kunyar? Gashi ya ja bala'in da yafi k'arfin na shi ta ci mutumcin shi son ran ta, Me ya sa ya yi haka to? Me ya sa baiyi bincike ba ko ya duba al'amarin? Amma kuma ya na tunawa da Haseenah sai zuciyar shi ta yi sakayau da ita, domin ya bata hak'uri ya sa ya k'arasa bakin titin da ke ofishin wajen masu siyar da waya, nan fa ya siya mata tsandareriyar waya ta ban hak'uri haka Bilal, dan ya jima ya na si ya siya mi shi dan ya dinga game, saida ya tsaya ya yi sallah azahar kafin ya wuce gidan, har madafa ya same ta ya bata wayar, ta yi murna sosai ta masa godiya, kallon ta ya yi yace "Ina Bilal?"

"Ya na falon maman shi, ba irin lallab'ar da ban masa ba ya fito ya k'i."

Fita ya yi ya na fad'in "Ina zuwa." Ganin ya sa ta bi bayan shi dan kar azo tambayar Bilal wani abu zaiyi, tare su ka shiga ya na kwance da alama ma bacci ya ke ji, zaune ya tashi yace "Abba sannu da zuwa."

Shafa kan shi ya yi ya na zama kusan shi yace "Yarima hutawa ake?"

"Um." Kawai ya fad'a yayin da Haseenah ta harare su ta wutsiyar ido a zuciyar ta tace "Hum! Yarima dai yarima, ku ba ku gaji sarauta ba amma ku lak'abawa yaro sunan yarima, haba dai." Ta k'arshe da yin k'wafa.

Ledar hannun shi ya mik'a mi shi yace "Duba ka ga tsarabar ka."

A hankali Bilal ya ciro kwalin ciki, ya na ganin waya ce ya yi sauri budewaya fito da ita sai shek'i take, dariya ya yi ya rumgume mahaifin na shi yace "Abba nagode, na ji dad'i sosai."

Rumgume shi ya yi cike da so da k'auna yace "Hakan na ke son ji dama."

Karb'ar wayar ya yi ya had'a mi shi da kan shi in da ya janyo mi shi mega (data) daga na shi ma'ajiyin sannan ya nuna mi shi yanda zaiyi ya dinga janyowa duk lokacin da ya ke so, nan fa suka zauna su na ta danne danne a wayar ya na nuna mi shi abubuwa da dama, Haseenah kam in ranta ya yi dubu tabbas ya b'ace, musamman da ya nunawa Bilal yanda zai iya janyo data amma ita saida ya amshi wayar ya jawo mata, haka ta gamo girkin ta kawo tare su ka ci da yaro kamar yanda suke ci a baya a faranti guda, har la'asar ya na gida tare da Bilal saida su ka yi sallah a masallaci kad'ai ya fita yace zaije gidan, dan da safe bai je ya gaishe su ba.

*Hajia Turai* ta na zuwa gida ta'aniya zazzaga bala'i, k'arshe dai shiryawa ta yi a motar ta taje gidansu Khadija, Khadija na falo sun gama girkin rana suna cin abinci ta zo gidan, nan fa ta tashi duk wani mai baccin rana a gidan ta na fad'a mu su wulak'ancin da Usman ya mata, Khadija da ta iya k'awar ta ta shiru ta yi saida ta kalle ta tace "Ke kuma sai magana na ke amma kin min banza, ko har yanzu ki na son mijin na ki?"

Tasan in ba ta bita sannu ba sai sunyi baran-baran, dan haka tace "Haba kema dai bari fad'in haka mana, ai ni tuni na yi wuri na aje shi tunda ya tab'a min ke k'awa ta, kwantar da hankali kinji tawa ki manta da lamarinsu kawai."

"Yawwa yanzu na ji magana, ai na d'aukar har yanzu ki na son komawa gidan shi." Ta fad'a ta na saka hannu cikin kwanon abincin, murmushi Khadija ta yi tace "Haba ina, ai sai a aljanna kuma idan da rabo mun had'u."

Saida ta cika baki da abinci tace "Shegiyar yunwa na damu na, amma wannan mijin na ki ya k'i bari na ci abinci ya aika min da yan sanda gida na, ke kinga bala'i da zafin shi ni da Usman a ofishin yan sanda."

Yanda Khadija ta santa tasan yanzu ma saita sake dawo da labarin baya, hakan ya sa Khadija cewa "Haba k'awa ta rabu da su kinji, ci abinci dai yanzu muje d'aki akwai hira."

Wata dariya ta yi "Hahahaha, haka na ke son ji k'awa ta, ki barsu kawai wallahi lokaci na zuwa da saiya dawo da k'afafun shi ya neme ki, wallahi saiya durk'usa har k'asa ya na neman afuwarki, ita kuma wannan tsinannar ko, haba, yo an fad'a mi shi mu na wasa ne, ai iskancin ma ba haka kawai mu ke yin shi ba, wallahi ko uban..."

Tabbas Khadija tasan cewa za ta yi uban shi dan ita ba damuwa bane gare ta, dan haka ta rufe mata baki tace "A'a k'awata, surukina ne fa, dattijon arzik'i ne babu ruwan shi."

"Hakane kuma, ai da ina so na mi ki misali da gyatumin shine."

Duk abin da suke fad'a mamar Khadija na gefe na saurarn su, dariya kawai take ba tare da sanin su ba, haka suka gama sun shiga d'aki nan ma kuma Salamatu ta zo wacce Khadija ta fad'a mata a waya tana gida, aifa d'akin Khadija kamar zai tsage saboda hargowar da suke yi, har k'arfe biyar na yamma suna gidan nan kafin suka tafi.

A wajen Usman kuma ko da ya je gida bayan sun gaisa da Hajia ta tambaye shi ya iyali, nan fa ya kora mata bayanin abin da ya faru daren jiya, Malam da shigowar shi kenan ya rabka salati ya na fad'in "Fodio, me na ke ji kana fad'a haka? Ka ce ta tafi gidan su sai ka neme ta? Me ka ke nufi da haka? Fodio ba ka ji kunyar fad'in maganar nan ba dan Allah?"

K'asa ya yi da kan shi baice k'ala ba, malam ne ya d'ora da "To tashi ka fita, kuma da anyi sallah isha'i ka zo ka d'auke ni k'afar ka k'afa ta muje mu dawo da ita, ni ba za ayi wannan haukan da ni ba kaji na fad'a ma ka."

A hankali ya mik'e ya saka takalmin shi zai wuce ta gaban malam ya kalle shi da kyau har ya fita, kallon Hajia ya yi yace "Anya kuwa yaron nan lafiyar shi k'alau?"

"Ni ma dai abin da na ke tunani kenan, ya na wasu abubuwa kamar ba'a hayyacin shi ba." Cewar Hajia da ke k'ok'arin d'auke tabarmar da ya tashi akai.

"Ai kuwa sai a d'auki mataki tun kafin abu ya yi nisa, amma in ba haka ba taya ma zai ce Khadija ta tafi gida saiya neme ta."

"Gaskiya kam."

K'arasa shiga d'aki malam ya yi ya na fad'in "Allah ya sawak'e."

Kamar yanda ya fad'a ana sallah isha'i ya dawo gidan ya d'auki malam, basu zame ko ina ba sai gidan su Dijeh wajen biko, karo na farko a rayuwar su da haka ta faru, sallama su ka yi tun farfajiyar gidan aka amsa, Ashir da kan shine ya mu su iso falon Mama, dan dama suna nan zaune dukan su, matansu ne suka fito tare da yara aka bar mazan tare da Mama sai Khadija da ke d'aki ta kan iya jiyo maganganun da suke.

*'Yata kawai ki koma*😉
14/02/2020 à 16:55 - 💋😘💋: 💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑
*KALLON KITSE*
_(Ake wa rogo)_
💑💑💑💑💑💑💑💑💑💑

_SAMIRA HAROUNA_

*Litattafan marubuciyar*

*1* _KAUSSAR_
*2* _D'AUKAR FANSA_
*3* _BA SO BANE_
*4* _AUREN HAD'I_
*5* _SANIN MASOYI_
*6* _JIHADI_
*7* _K'ANGIN RAYUWA_
*8* _ITACE K'ADDARARMU_
*9* _KAWU NA NE_
*10* _MAATA_
*11* _KALLON KITSE..._

*SADAUKARWA GA*

_MATAN FARKO_ 🧕🏼 *(UWAYEN GIDA)*

🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
_(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah)_🤜🤛

```Fatan alkairi masoya```

_Bismillahir rahamanir rahim_

*25*

Saida ya gama fad'in abin da ya faru kafin ya d'ora da "Wallahi Mama Khadija ta bani mamaki, wai ni Khadija zata kalla ta dinga fad'awa duk abin da ya zo bakin ta, saboda kawai na mata kishiya saita raina ni, ko kuma dan na mata magana akan abin da tayi bata kyauta bane, wannan abu ya b'ata min rai sosai, shine dalilin da ya sa nacr ta zo gida saina neme ta, banyi haka dan cin mutumcin ta ko cin zarafinku ba, sai dai nasan dole anan akwai wanda za su fad'a mata kuma ta saurare su, dan naga yanzu kishi ya rufe mata ido gaba d'aya."

Malam ne yace "Kai dallah rufewa mutane baki, koma menene ai sai kayi hak'uri, duniyar nan uban waye baisan halin mace ba akan kishi, ko kai kana ganin kamar uwarka ba ta da kishin ne, ita kan ta mahaifiyar ta ta da ka ke magana akai ai tasan zafin shi, kenan sai ka yi hak'uri ka d'auke kan ka dukansu na d'an lokaci ne za su yi, in banda rashin hankali irin na ka da can farko ta ma ka haka kafin zuwan amaryar?"
Chapter 47 · 0% Book details