← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 86

Sashe 13

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bud'a k'ofar motar ta yi za ta shiga sai kuma ta ga Usman sai wani kallo ya ke mata kamar irin ya na jin haushin ta, dan haka ta rufe k'ofar ta zagayo wajen shi ta kalle shi cikin taushin murya da nutsuwa tace "Na ga kamar haushi na ka ke ji saboda abin da ya faru, dan Allah ku yi hak'uri ku yafe min, duk da nasan laifi na ne, amma kuma Allah ne ya aiko, ka gafarce ni idan na b'ata ma ka rai."

Juyawa ta yi ta shiga motar, shi kuma juyawa ya yi ya na jan wani tsakin, bin Mannir ya yi da harara yace "Sai ka rufe bakin to sakarai, har da wani sai yaushe za ta dawo, to uwar me za ta maka idan ta dawo?"

Bai jira me zaice ba ya wuce sabgar gaban shi, tun daga ranar kuma Khadija ba ta sake komawa gidan ba, dan lokuta da dama ta kan ji ta na so taje saboda tsohuwar da tsohon masu kirki da kuma saka mata albarka, amma idan ta tuna Usman sai ta share kawai, a cewar ta wannan ba shi da kirki ko kad'an, gashi da d'acin rai da zuciya, alhalin Usman kuma ba ma mazauni bane, baya cikakken sati a gida bai tafi sabgar gabanshi ba, musamman ma da iyayen ke yawan mi shi magana akan ya yi aure, shi ya sa ba ya son zaman gidan dan duk motsin shi sai suce da ya na da aure da anyi kaza, aure ba shine gabanshi ba, ya na so ya taka wani mataki kafin ya yi aure, shi ya sa ma shekarun shi *talatin da d'aya* ba sa damunshi, k'annan shi mata yan biyu da suke bi mi shi tuni suka hayayyafa a gidajensu, sannan d'aya k'anan shi da suke uwa d'aya ma yayi aurenshi shekara biyu data wuce, k'annan shi mata kuma hudu ne a gidan mazajensu, duk iskancin da suke mi shi ko a jikinshi kam, neman sisi da kwabo yasa a gaba.

*Bayan wata bakwai* Khadija har ta fara karatunta na jami'a (lycée) hankali kwance, ta yi sababbi k'awaye sosai a ciki ne ta had'u da *Barira nagoma* wacce unguwarsu ke kusa da gidansu Usman, duk da Khadija ce ta bige tsohon amma ta manta da abin da ya faru, ranar kawai sun taso daga boko da yamma ta kawo Barira gida akan moton ta, layinda ta shiga dan ya sadata da titi ne ya kawota k'ofar gidan, har zata wuce sai kuma tace bara ta tsaya ta shiga, har ta shiga soron sai kuma ta ji ba ta so ta samu wannan mai d'aure fuskar, da k'arfi ta juya dan ta koma wajen moton ta sai kawai wata yarinya k'arama data shigo da gudu su ka ci karo, fad'uwa yarinyar ta yi ta fashe da kuka saboda buguwa da kanta ya yi da bango, yanda ta tsala kukan ne ya sa Khadija yin saurin durk'usawa ta rumgumo yarinyar ta na lallab'a ta, gidan kuma akwai mutane har da Hassana ma ta zo, kuma d'iyar tace aka bige, da sauri su ka fito soron dan gani me ke faruwa, har da Usman wanda zuwan shi kenan daga *zinder* ko d'aki bai shiga ba, lafiya lafiya? Kowa ke tambaya, Khadija kam tsaresu ta yi da ido sai da Usman ya daka mata tsawa yace "Wai ba tambayar ki ake ba? Me ki ka mata?"

Tsaye ta mik'e lokacin da Hassana ta d'auke yarinyar daga jikin Khadija, kallon tsohuwar ta yi tace "Dan Allah ku yi hak'uri, wallahi ban lura da ita bane, kuma ta shigo ta na gudu."

Hassana ce tace "Ba komai haba, ai yaran kenan, bare ma *Fadila* da bata tafiya sai gudu."

Usman ne yace "Baiwar Allah, in dai har za ki ci gaba da saka wannan gilashin, to fa ki sani wallahi kullum ki na cikin karo da mutane ki na ji musu ciwo, me zai hana ki cire shi ki aje ko kuma ki dinga hutawa? Shi fa gilashi ba dan sakawa kullum bane, yawan anfani da shi ya na b'ata ido, wanda su ka san abun ma za ki ga akwai lokacin da kad'ai suke anfani da shi, amma ba kamar ke ba sai kace makauniya kina ta fama da abu kullum a ido, wallahi za ki ragewa kanki kud'i ne idan idonki su ka samu matsala."

Khadija da tunda ya fara magana ta kafe shi da ido, sai da ya gama tasa hannu ta cire gilashin tasa hijabinta ta share k'wallan da suka taru a idonta, kallonshi ta yi amma sam ba ta iya ganinshi da kyau, wasu hawayen ne suka sake taho mata, kallonshi tayi tace "Ni ma ba haka kawai na ke sakawa ba, larurar ido gare ni, sai da shi ne na ke iya gani, ku yi hak'uri dan Allah idan na b'ata ran ku, zan wuce ne dama nace bara na biyo mu gaisa, da nasan haka za ta faru da ban biyo ba."

Ta na fad'a ta juya ta na ci gaba da share k'walla, ta na sauke hannunta k'asa ashe har ta kai wajen moton ba ta sani ba, sai kuwa ta kai mi shi karo motonta fad'i ita ma ta fad'a mi shi, duk da taji zafi haka ta tashi, da saurin mutanen cikin soron su ka fito dan taimaka mata, banda Usman da ya kasa motsawa sai kallonta ya ke, Mannir zai taimaka ya d'aga mata moton tace mi shi "Ka bar shi kawai nagode."

Gilashin ta saka ta d'aga moton ta tayar ta wuce, daga wannan ranar ta yanke ba zata sake zuwa gidan ba ko da hanya ta d'auko ta, yayin da Usman kuma ya sha fad'a sosai wajen malam Ali ya kuma ce sai ya je har gidansu ya bata hak'uri, baiyi musu ba yace zaije, dan ya faranta mu su kamar yanda ya saba, a daren ranar yaje gidan ya kuma aika aka mi shi sallama da ita, da farko kamar ba zata fito ba saboda ba ta yanayin dad'i, sai kuma mama tace taje ta gani watak'ila bak'o ne, fitowa ta yi da doguwar rigar shadda da mayafi, ta na ganinshi ta daskare wuri d'aya har saida ya sauko daga kan moton ya same ta, ita dai kallon shi take yayin da yace "Sannu ko?"

Da kai kawai ta amsa tana ci gaba da kallonshi, gyara tsayuwa ya yi yace "Kin yi mamakin gani na ko? Ba abun mamaki bane, na zo ne na baki hak'uri akan abin da ya faru d'azu, bayan dogon tunani da nazari na gane ban kyauta ba, ina afuwar ki dan Allah ki gafarce ni, rashin sani ne da kuma rashin fahimta."

Ko ba komai ta ji dad'i da ya bata hak'uri, cikin taushin murya tace "Ba komai wallahi ya wuce ai."

D'an sunkuyowa ya yi yace "Kin tabbatar ya wuce?"

Kallonshi ta yi da murmushi tace "Na tabbatar."

Saida ya sake nuna ta da hannu yace "Kin tabbata ba za ki sake kallo na a matsayin marar kirki ba?"

Da murmushin da ya fito da hak'oran ta tace "Na yi alk'awari."

"To shikenan nagode sosai da ki ka yafe min."

"Ni ma nagode." Kallonshi ta yi tace "Sai anjima."

Ba ta jira ta ji me zaice ba ta juya za ta shiga kuma sai ta ji oda a bayan ta, ta na juyowa ta ga yayan ta ne Ashir, kashe motar ya yi ya fito daga cikin, "inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un." Cewar Usman, dan har zuciyar shi bai so Ashir ya gan shi k'ofar gidan nan ba kuma tare da k'anwar shi, sai ya d'auka akwai wani tsakaninsu ne, matsawa Khadija ta yi kusan shi ta rik'o hannun shi tace "K'afafu na sannu da zuwa."

Dariya ya yi yace "Yau ko k'afafun nan na ki sun gashi sosai dan sun sha yawo."

"Sai muje nasa aunty *Rahama* ta gasa maka su ai." Ta fad'a ta na jawo shi, zaro ido ya yi yace "Kai, ka kai, ka kai, wa na ke gani kamar Usman."

Murmushi kaxai Usman ya yi kafin Ashir ya ba shi hannu su ka yi musabaha da gaisuwar anjima ba'a had'u ba, saida suka gama ya saki hannun Khadija yace "Auta zan shiga ciki, idan kin gama sai ki zo kiga tsarabar ki."

Turo baki ta yi ta juya masa baya, dariya ya yi ya aza duka a kafad'ar ta yace "Ayi hak'uri, Nana Khadija baiwar Allah."

Juyowa ta yi ta na fara'a tace "Wannan sunan ya fi dad'i, amma wani auta auta kamar k'aramar yarinya."

Kallonta ya yi yace "Um! Wato ke kin girma ko? To ya ki ke dani tsoho."

Tura shi ta yi ya nufi cikin gidan tace "Dallah ni dai ka shiga ciki."

Dariya ya yi ya wuce ya na ma Usman sallama, sai da ya shige ta kalli Usman tace "Ni zan shiga ciki, sai anjima."
Chapter 13 · 0% Book details