← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 86

Sashe 62

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya na fad'a ya kashe wayar ya jefa kan kujera, zaune ta yi ta na kallon shi tace "Ya dai babban mutum na ji ka na waya haka kamar ka na fad'a? Kai da wa ne haka?"

Cikin fusata yace "Ni da wannan banzan Nura fa, wai har ni zai kalli tsabar ido na ya na fad'a min magana har ya na ci mi ki mutunci, amma ba laifin shi bane laifi na ne da na sakar mu su fuska har su ke samun damar fad'a min abin da duk ya fito bakin su."

Cikin ladabi tace "To me yace ma ka?"

"Ki barshi kawai, ban san tunawa." Matsowa ta yi kusa da shi ta b'alle mab'allin rigar shi ta sa hannu ta na shafa k'irjin shi ta na fad'in "Na fi ka sanin cewa yan uwan ka ba sa so na, musamman yanzu da aunty Khadija ba ta gidan nan, wallahi gaba d'aya haushi na suke ji, gani su ke kawai laifi na ne ni ce silar barin ta gidan, amma ka sani ba zan tab'a damuwa da hakan ba in dai har ka na tare da ni."

Rumgume ta ya yi yace "Kar ki damu Mummyn beby, babu abin da zai raba ni da ke saboda ina bala'in son ki sosai."

Nura kam shi ma cikin hushi ya aje wayar shi ya ci gaba da aikin da ke gaban shi ya na balbala masifa shima, bai damu ba dan yace ba zai bashi gudummuwa ba, dan dama a shirye ya ke kafin ma ya fara maganar auren, dan haka ya yi niyyar yi wa kan shi komai ba tare da jiran taimakon wani ba, sunyi mai wuyar tunda sun nemo mi shi auren.

Har ya gama abin da ya ke ya dawo gida kowa bai fad'awa abin da ya faru ba, dan Nura mutum ne mai zuciya da kuma rik'o sosai, wannan abun da ya faru ko da an yafi juna zaiyi wuya ya d'ora idon shi akan Usman ba tare da ya tuna wannan ranar ba, uwa uba kuma Haseenah da ya ke da tabbacin ita ce silar faruwar komai, har ya yi wanka ya ci abinci zai fita Hajia tace "Wai kai ya ku ka yi da Fodio da ka je gidan?"

Fuska a had'e yace "Ba komai Hajia, dama wani sak'o ne zai bani na kai wani wurin."

"To ai ni na d'auka ko maganar auren ta ka ce za ku tattauna." Hanyar fita ya nufa ya na fad'in "A'a ba ita bace."

Har ya kusa kaiwa k'ofar fita ta sake cewa "Zo ka kira min shi a waya, ni tun yamma na ke kira ba na gane me ake fad'a, kuma har yanzu bai shigo gidan ba har dare ya yi." Dawowa ya yi ya karb'i wayar ya danna kiran lambar Usman ba tare da yace komai ba, wayar na k'ara a lokacin amma ba'a d'auka ba.

Manne suke da juna basu rabu ba, sai dai ta samo mu su abu su tab'a kawai su yi sallah idan lokacin ya yi, mai gadi bawan Allah sam sun ma manta da a al'amarin shi bare a aika mi shi da abinci, sai dai ya siyo kawai ya ci amma ran shi bai mi shi dad'i ba, a haka har dare ya riske su Usman sai amsa waya ya ke musamman abokan shi na rashin ganin shi yau da ba ayi ba a waje, wani ikon Allah kuma saida su ka yi shirin kwanciya sai ciwon mara ya hana Haseenah sukuni, cikin rud'ewa ya d'auke ta su ka nufi asibitin da aka fara duba ta tun farkon rashin lafiyar ta, suna gaban likita lokacin kiran Hajia ya shigo wayar shi, kasa d'auka ya yi ya mayar da hankali kan abin da likitan ke fad'a cewa ta daina duk wani aikin wahala, in fa ba haka ba zata iya yin b'arin cikin nan, haka aka sallamo su suka dawo aka ce ta ci gaba da shan magungunan da aka bata na farko, tun cikin mota yake fad'in "Wallahi ba za ki k'ara dafa ko ruwan zafi ba a gidan nan, ke baki san yanda na ke son abin da ke cikin nan naki ba, amma bari cikin ki ya k'ara k'wari wallahi k'asar waje zan fita da ke ki haihu acan, dan ni ban ma gamsu da likitocin nan d'in ba, daga yanzu kuma zuwa lokacin zan samo mi ki yar aiki ko kuma Aziza ta dawo nan ta dinga aikin gidan."

Ita dai ta na sauraren shi dafe da marar ta har suka isa gida, da kan shi ya canza mata kaya ya kwantar da ita ya bata magani tasha sannan ya rufe ta da zanin rufa, k'ura mata ido ya yi ya na kallo har bacci ya d'auke ta, wani bala'in tausayinta da kuma son ta ne ke k'ara gyauraya da jinin shi, ta yanda yake jin kamar ya mayar da cikin jikin shi saboda ta samu sauk'i, ya jima zaune kafin ya fito da wayar shi ya ga kiran Hajia, fita ya yi falo ya sake maida kira cikin sa'a kuma Hajia ta d'auka, a d'an kakkauce suka gaisa kafin ta tambaye shi ya yi aiki da magungunan nan, "Sosai ma Hajia, ai duk na yi aikin da su." Cewar Usman fa, tambayar shi ta kuma yi me ya hana shi zuwa yau? Malam ma ya bayar da ruwan addu'a a abashi amma bai zo ba, haka kawai ya tsinci kanshi ya sharara k'arya ta hanyar fad'i "Hajia ai wani abu ne ya d'an taso da ya sa dole sai da na je *katsina*, kuma sai bayan isha'i na dawo ina zuwa na gaji sosai kawai na d'an kwanta, yanzu ma ina bacci ne na farka sai kuma na ga kiran ku."

Cike da gamsuwa Hajia tace "Ah to shikenan, saida safe, Allah hutar da gajiya."

"Ameen Hajia, nagode, saida safen ku." Ya na fad'a ya kashe wayar ya shiga uwar d'akin shi ya canza kaya kafin ya dawo d'akin Haseenah.

Washe gari da safe kafin malam ya fita saida ya sake bayar da ruwan addu'a, Hajia dai ba ta ma fad'a mi shi na jiya na nan ba kawai ta amsa, sai kuma akayi sa'a Usman ya zo gidan, shi ma kuma ya zo ne da maganar Aziza ta koma can da zama ta na taya ta aiki, kasancewar ba sabon abu bane ya sa Hajia cewa idan malam ya zo za ta fad'a mi shi, idan ya amince saita kira a fad'a mi shi, nan ta d'auko ruwan duka biyu ta bashi ya shanye kafin ya fita, daga nan wajen Murtala ya nufa su ka d'an tab'a hira har ya na tsokanar shi wai amarya da uwar gida sun hana shi fita ko ina, nan ya kalle shi ya tab'e baki yace "Wace uwar gida kuma da ba ta nan?"

Da mamaki Murtala yace "Ban gane ba ta nan ba, to ta na ina?"

K'ara tab'e baki ya yi yace "Ta na gidan su mana."

"Gi me?! Murtala ya fad'a da k'arfi har da dafe k'irji, a wulak'ance ya kalle shi yace "Gida na ce, gidan iyayen ta, ko tafi k'arfin zuwa gida ne?"

Kai tsaye ba tare da fargaba ba Murtala yace "Ta fi k'arfi, wallahi in dai Khadija ce tafi k'arfin haka aboki na."

Sake tab'e baki dai ya yi yace "Sai kuma ka yi kan ka ake ji." Dafa shi Murtala ya yi yace "Wai dan Allah in tambaye ka mana? Ka na nufin ta tafi gidan su saboda ganin damar ta? Ko kuma kai ka kora ta gida? Ko kuma ma dai wasa ka ke min?"

Cikin hassala yace "Ya zan ma ka wasa da wannan maganar, wai ita Khadijar nan me ku ke d'aukar ta ne da ba za'a hukunta ta ba?"

Wani kallo Murtala ya ma sa yace " Mun d'auki Khadija a matsayin rayuwar Usman, sannan Khadija ita ce sirrin duk wata nasara ta Usman, kar ka manta da haka aboki na, duk abin da ka zama yau Khadija ta taka muhummiyar rawa a zuwan ka wannan matakin, amma gaskiya abin da ka yi yanzun kasa ni kai na na fara jin kunyar had'uwar da ita da iyayen ta da kuma 'yan uwan ta, shin aboki na yanzu da wane irin ido za ka iya kallon Ashir idan kun had'u ko da bisa hanya ne?"

Cikin b'acin rai ya kalle shi yace "Da wane ido fa, da idon da ya ke kallon na shi 'yan uwan matar wacce ya saka lokacin da zai k'ara aure, Rahama ba, ka tuna da ita? To ai gwara ma ni tunda ba sakin ta na yi ba, kuma ita ce ta d'auki kayan ta ta tafi ba ni nace ta tafi ba."

Murmushi Murtala ya yi yace "Kafi kowa sanin dalilin da ya sa Ashir ya rabu da Rahama, ta yi ikrarin in har ya k'ara aure to ba shi ba kwanciyar hankali, sannan daga lokacin ta dinga nuna raini akan mutanen da suka fi komai daraja a wurin shi, mahaifiyar shi da kuma Khadija, wulak'anta su da ta fara yi ta na kallon su kamar sune ke zugashi ya sa ya kasa jura ya sallame ta, amma kai kuma fa? Fad'a min tayar ma ka da hankalin da ta yi."

Tsaki ya yi yace "Kaga, ni ban zo nan ba saboda jin wannan maganganun, kawai..."

Dafa shi ya yi cikin nutsuwa yace "Me ya ke damunka aboki na? Fad'a min miye matsalar mana? Khadija ce fa, matar nan da ba ka son komai sama da ita, ina wannan soyayyar? Ina wannan k'aunar? Ko da yake ma bai kamata na tambaya ba, nasan har yanzu ka na son ta."

"Ba gaskiya bane, ni yanzu ba na son ta." Ya fad'a ba alamar wasa, murmushi Murtala ya yi yace "Ka rufe idon ka, sannan ka saurari zuciyar ka ita kad'ai, kar ka bari wani tunani ya shiga tsakanin ka da zuciyar ka, ina tabbatar ma ka hoton Khadija za ta gani."
Chapter 62 · 0% Book details