← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 86

Sashe 71

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Yar siririyar dariya ta yi tace "Toh fa Alhaji mai babbar riga, kai da za ka je d'aurin aure kuma me ya had'a ka da bacci? To ka farka idan mafarki ka ke, kai da sake ganin murmushin Nana Khadija kuma sai dai ko a lahira, a lokacin da aka min umarni da na shiga aljanna, to zan iya juyowa na kalle ka dan na ma ka bye bye, to fa zai iya yiwuwa a lokacin ne za ka ga murmushin."

Shi maganar ta dariya ma ta bashi, da sauri ya rik'o hannunta ya matso daf da ita yace "Ki na so ki ce ni kuma zan zauna har sai kin riga ni shiga? Ko kuma nufin ki ni ba ma zan shiga ba?, ai k'afar ki k'afa ta insha Allahu, in kuma ba haka ba to sai dai ki same ni a ciki kewaye da sabbin mata na."

Fizge hannunta ta yi tace "Ka na dukan nawa ne kuma ka ke tunanin za ka shiga aljanna."

Wucewa ta yi ta bar shi nan tsaye ya na ta dariya shi kad'ai, Murtala ne ya k'araso wajen shi yace "Mijin Khadija lafiya ka ke dariya kai kad'ai?"

Hararan shi ya yi yace "Ni kad'ai ka gani a wurin? Ba ka ga wacce na gani ba."

"Na gani kam, ince dai kun sasanta za ta koma?" Kallon shi ya yi sosai yace "Da alama fa sai ka tayani bata hak'uri, ran 'yar aljanna ya b'ace sosai."

Zaro ido Murtala ya yi yace"Wa? Ni! Sam ba dani ba, kai dai da ka mata laifi ka bata hak'uri amma banda ni."

"Au! Yanzu ka na nufin ba za ka tayani ba kenan? To nagode, ai na d'auka zan iya yin zaune gida ma kai kaje har sai ka dawo min da ita, ashe ba haka bane."

"A'a ni ba haka na ke nufi ba, kasan dai maganar nan ta manya ce ba iri na ba, kuma tsakanin ka da Khadija ma ai ba ta b'aci."

Ba jimawa da shigar Khadija mutane aka fito dan tafiya wajen d'aurin auren, daga ciki har da Mama dan dama d'aurin auren take son samu, nan aka shiga motoci aka wuce d'aurin auren, Khadija na zaune d'akin Hajia Nura ya shigo da sauri ya na kiran sunan Hajia, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida yane, ke ba ki je d'aurin auren ba?"

Hararan shi ta yi tace "Wa? Allah ya sawak'e, me zanje na yi a d'aurin auren kishiya, ai ina daga nan ina aika mu ku da addu'a."

"Yawwa hakan ma ya yi ai, addu'ar ita mu ke buk'ata ai." Cewar Nura ya na kallon Hajia da ta fito daga d'aki, cikin k'aguwa yace "Hajia takalma na da na baki jiya na ke nema."

Ledar hannun Hajia ta mik'o mi shi tace "Dama nasan su za ka nema ka ke min wannan kiran."

Bud'ewa ya yi ya saka takalman kafin ya juya zai fita yace "Hajia ku fara tausar min k'irjin ta kafin na dawo."

Haka suka wuce wajen d'aurin aure gidan waliyin Choukra, kuma ba'a b'ata lokaci ba waken yin abin da ya kai kowa wurin, nan aka d'aura auren *Nura Ali* da amaryarshi *Choukra Sabi'u*, bayan taya juya murna da farin ciki ne abokan ango su ka nufi inda za su ci su sha, manyan mutane kuma suka dawo gidan su ango dan cin abinci suma.

Bayan tafiyar 'yan d'aurin aure ne ba jimawa kuma Haseenah ta zo ita ma kamar yanda Usman yace ta zo da wuri, a d'akin Hajia suke zaune nesa da juna amma babu mai kula wani, haka suke zaune Khadija na hira da mutanen da ba su je d'aurin auren ba, Hajia ce ta fito daga uwar d'aki ta kalli Khadija tace "Nana wai kinga Bilal kuwa?"

"A'a Hajia, ya na ina ne?"

"Ai tare da malam su ka shirya su ka fita, kin ganshi kamar shine angon sai rawar k'afa ya ke, saida na gargad'e shi dai kan karya kuskura ya kalli wasu mata."

Dariya kawai ta yi ba tace komai ba har mutane su ka fara shigowa aka fara hayaniya, nan su Hassana da sauran mutane suka fara raba abinci ana kaiwa mutane.

Bilal ne ya shigo tare da malam kai tsaye wajen mahaifiyar shi ya nufa ya zauna kan k'afafun ta, wanda hakan ya yi daidai da shigowar Usman da kwalbar lemu a hannun sai malam a biye da shi, kwantar da kan Bilal ta yi a k'irjin ta tana sumbatar shi tace "Yarima na yi kewar ka fa, kwana uku ka na nesa da ni."

Bilal kenan d'an gata sai kuwa ya sake wani cakume ta kamar zai sa nonon ta a baki yace "Mummy yunwa na ke ji fa."

Lek'a fuskar shi ta yi tace "Ban gane ba, ba ka ci abinci ba ne a waje?"

Cikin shagwab'a yace "Ban ci ba, to duka fa manya ne a wajen."

Murmushi ta yi tace "To yarima na k'arami ne? Yaro ana bikin kawun ka ace ka na rasa abin da za ka ci, to ba ka had'u da Abban ka bane?"

K'ara tusa kanshi ya yi cikin jikin ta yace "Um um."

D'ago kan ta tayi za ta yi magana sai ga Usman tsaye gaban ta ya na fad'in "Yarima yanzu da girman ka za ka hau k'afafu haka?"

Da sauri Bilal ya d'ago ya na ganin Abban shi ne ya yi tsaye ya mak'ale mi shi a wuya, rumgume shi ya yi shima yace "Me ya ke faruwa ne na ga ka na ta zuba shagwab'a haka?"

Khadija ce tace "Bai ci abincin bane, amma kuma kai ga hannun ka nan har da lemu ma ka ke korawa."

Kallon ta ya yi yace "To yanzu shan lemun nawa ya zama haramun ne ko me?"

"Ya zama mana, taya za ka jefa loma bakin ka ba ka san gudan jinin ka ya ci ko bai ci ba." Yanda ta had'e fuska ne ya sa ya ga ko ya fad'a mata shi ma bai ci abinci ba ba yarda za ta yi ba, dan haka ya juya da Bilal d'auke da shi yace "Yarima muje ka zab'i abin da ka ke so ka ci, rabu da mahaifiyar nan ta ka yau tunda safiya ta waye ta tashi da masifa, can ta k'arata da masifarta."

Shiru ta yi sai kallon k'eyar shi da take, shi kam jin ta yi shiru ya sa ya juyo dan ya san ta na nan ta na kumbura, wata irin harara ta dalla masa da tasa shi b'arkewa da dariya yace "Yi hak'uri Hajia, nasan me ye matsalar ki, ki ba ni hak'uri sannan ki lallab'a ni sai na mi ki magani."

Yanda ta motsa bakin ta ya sa ya fahimci me take nufi, dan haka ya mata gwalo yace "Idan kin kamani ki mayar da gabana gabas ki yankani."

Da haka ya fita su ka bar gidan, tun lokacin ba ta sake ganin Bilal ba har biki ya yi biki ana ta bayar da zafi, Haseenah na d'akin Aziza kwance sai narkewa ta ke, sai dai kuma abin ya d'an dameta na yanda kowa baya ma kula ta, sai wanda ya ganta ne dole ya ke iya gaisawa da ita, amma har Aziza sai ta shigo d'akin ta fita ko kallon in da take ba ta yi ba, haka yamma ta yi aka raba abinci, kasancewar a d'aki take ita kad'ai ya sa aka rabe abinci ba'a ma san da ita ba, babu wanda ya damu da hakan sai ma ran su Hassana da ke k'ara b'aci.

Da dare mutane duk sun tafi gidan amarya da ango, Khadija ce d'aki ke gaggauta shirya dan tafiya tare da masu jiranta a waje tunda ta zo da mota, sai Haseenah da tun sallah magriba ta tafiyar ta gida, Hajia na zaune kan katifa gyangyad'i na neman fizgar ta Khadija tace "Hajia bacci ne?"

Kallon ta tayi tace "To tukuna dai."

Saida ta gyara jakarta a kafad'a tace "To ni zan tafi, kuma ina ga daga can gida zan wuce, sai dai gobe idan Allah ya kaimu."

"To Allah ya yarda Khadija, Allah hutar da gajiya, angode sosai Allah ya saka da alkairi, saida safe." Duk ta na maganar ne saboda Khadija har ta kai bakin k'ofa ta na amsa mata, za ta bud'a labulen d'akin Usman ya sallamo, kaucewa ta yi da tunanin ya wuce amma saiya wani tsare ta da ido yace "Hajia ke kuma wannan kwalliyar fa? Duk ta zuwa kallon ango da amaryar ce?"

Kallon Hajia ta yi sai ta ga ita ma su take kallo dan haka ta share shi kawai, hannu ya sa aljihu ya ciro da hankici (hankiciep) ya kai a bakin ta zai goge mata jan baki, da sauri ta ja baya ta na rufe bakin tace "Ya za ka goge min? Yanzu fa na saka shi, kuma ina da bak'o ne a gida."

Wani kallo ya mata yace "Bak'o kuma? Wane irin bak'o?"

Ba alamar wasa tace "Bazawari nn..." Bugun da ya kai mata a baki ne ya sa ta saki k'ara ba ta shirya ba tare da rufe bakin ta durk'ushe kan gwiwanta, Hajia da ta zabura ne ta kalle shi tace "Alhaji meye haka? Me tai ma ka?"

Zaune ya yi akan kujerar da ke iya fuskantar Khadijar ya na hararan ta, cikin d'aga murya Hajia tace "Fin k'arfi ne ko me? Dallah malam ka bata hak'uri ko."

Rai b'ace ya kalli Hajia yace "Hajia ba ki ji me yarinyar nan ta ke fad'a ba ne, ina matsayin mijin ta za tace wani wai bak'o na jiran ta, har da cewa wai bazawarinta." K'wafa ya yi hakan ya sa Hajia kallon Khadija da har yanzu ba ta motsa ba tace "Yi hak'uri kinji Khadija tashi ki tafi abinki, ba zan iya tashi bane saboda k'afafu na amma da na rama mi ki dukan ki, ki yi hak'uri kinji."

D'agowa ta yi a hankali ta sauke ido a kan shi sun mata jawur, murmushi ta yi ta kalli Hajia tace "Saida safe."

Mik'ewa ta yi ta fice daga gidan, ta yi k'ok'ari ta sauke ma su jiran ta a waje gidan amarya amma ita ba ta tsaya ba ta wuce gida.

*A gurguje*
Chapter 71 · 0% Book details