← Book details Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 86

Sashe 51

Kallon Kitse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Aishatu ta koma take mita akan amaryar Usman, har akayi sallah magrib da isha'i su ka ci abinci, anan take tambayar Khadija za ta je bikin *Saratu* (kamar jikanya take ga mahaifiyar Khadija), zaro ido ta yi tace "Wai yaushe ne bikin Saratu?"

"Jibi mana." Cewar Aishatu tana shirgar wainar ta, cike da mamaki Khadija tace "Wallahi na manta, kuma Mama ba ta sake tuna min ba, amma dai bara na kira Abban Bilal na fad'a mi shi yanzun nan, dan zan iya mantawa, kuma tafiya ce da ba nan cikin gari ba akwai buk'atar ya sani da wuri."

Saida ta d'auki wayar ta ga kiran shi har uku ba ta d'aga ba, maida kiran ta yi kamar kuma jira ya ke sai kuwa ya d'auka dan ya zazzage kwandon bala'i, cikin sa'a sai Aishatu ta d'aga murya tace "Gaida min shi, ki ce na ga amaryar shi ina taya shi murna."

Dariya Khadija ta yi tace " bara na baki sai ki fad'a mi shi." Bata wayar ta yi, kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu ya sa su ka dinga hira ta na tsokanar shi shima haka kafin Khadija ta karb'i wayar, ta na d'orawa a kunne tace "An wuni lafiya saraki."

"Lafiya lau, anga damar d'aukar wayar?"

Murmushi ta yi tace "Ka yi hak'uri, ina aiki ne a lokacin ban lura ba, yanzu ma na d'auko wayar ne zan nemi izinin ka sai na ga kiran."

"Izinin me kuma?"

"In ba ka manta ba wata biyu da ya wuce na baka goron Saratu? To bikin ne ya taso yanzu ni har na manta ma saida Aishatu ta tuna min."

"Yaushe ne?"

Ta na wasa da yatsunta tace "Jibi, ranar da su Bilal za su koma makaranta."

"Amma ai ba cikin gari bane?"

"Eh hakane."

"Shikenan, Allah ya tsare, zan kira Mama na tambaye ta shirye shiryen tafiyar." Ya na fad'in haka ya datse kiran, ita kam bata wani damu ba tunda dai ya barta, sai wajen tara na dare Khadija ta ma Aishatu kyautar fitar hankali kafin ta bar gidan.

B'angaren Haseenah kam tunda ta ci wainar nan dayawa sai ta tayar mata da zuciya ta dinga kelaya amai, sosai ta galabaita har Aziza ta tashi hankalin ta, dare na sake yi kuma sai zazzab'i da ciwon kai, Hajia su ka kira aka fad'a mata tace su shirya su fad'awa Khadija tunda ita ta iya mota saita kai ta asibiti, ira kuma za ta same su asibitin yanzu, har Aziza za ta tafi wajen Khadija kawai Haseenah ta rik'e hannunta tace kar taje, "Me ya sa to?" Ita ce tambayar da ta mata.

Cikin galabaita tace "Kawai ba na so tasan halin da na ke ciki, ko ta taimaka min ba dan Allah bane, dan ta samu mafakar da za ta yak'eni ne."

Da mamaki tace "Amma Haseenah dan ta kai mu asibiti miye a ciki?"

Kallonta ta yi tace "Aziza in za ki samo mai adaidaita ki samo, in ba za ki sami ba ki bar shi, yanzu haka da yan uwa na za su san ina cin abincin ta wallahi da sun tofa min yawu, mutum fa ba abun yarda bane, kuma ke kinfi kowa sanin ta ai."

"Gaskiya ne kuma." Cewar Aziza jiki a sanyaye, haka suka shirya suka fita a hanya suka yi sa'ar samun adaidaita su ka hau, asibitin kud'i aka kai da ke nan kusa da su ta *Clinique Alheri*, tun kafin su ka likitan Hajia ta k'araso ta na waya da Usman da ta sa aka kira shi take fad'a mi shi, aifa kamar ya taso ya zo ya ke ji ance amarsu ba lafiya, ko da su ka ga likita ya mu su albishir da ta na da ciki amma k'arami, nan dai aka mata allura tare da bata magunguna, bayan sun biya kud'i tsagaga su ka dawo gida da rankiyar Hajia, kwance Haseenah ta yi Hajia ta kalli Aziza tace "Da na ce ku fad'awa Khadija ta kai ku me ya sa ba ku mata magana ba ku ka hau adaidaita?"

Aziza ce "Hajia zan..." Da sauri Haseenah ta mata alama da hannu kan ta yi shiru, duk da Hajia ta gani amma da tace "Me ye ta yi shiru?"

Cike da tausayi tace "Hajia kawai ku bar maganar, tunda dai gashi mun tafi kuma mun dawo lafiya."

Shiru Hajia ta yi da mamaki, kallon ta tayi tace "Kun ci abinci?"

Kallon juna su ka yi sai Haseenah ce tace "Wallahi wata waina ce aunty Khadija ta aiko mana, ko gama ci banyi ba zuciyata ta tashi sai amai."

"Yanzu ta na aiko mu ku da abincin kenan?" Cewar Hajia ta na kafesu da ido, Aziza ce tace "Hajia bata aikowa fa, sai kamar irin wannan ranakun alhamis ko juma'a, shi ma sai in ya na girkin ta ne."

Kallon Haseenah ta yi tace "Ki fad'awa Aziza idan za ki ci wani abu mai sauk'i saita d'ora mi ki kafin ki sha magani, ni yanzu gida zan tafi dare ya yi."

"To." Ta fad'a ta na yamutsa fuska, Hajia na fita tasa Aziza ta d'ora mata zallar shayi tasha kafin tasha magana, kiran ta Usman ya yi suka dinga hira har saida tace za ta yi bacci, Hajia kuma na fita ko kallon b'angaren Khadija ba ta yi ba saboda ran ta ya sake b'acewa a game da ita, adaidaita ta hau ta koma gida, ba ta yi nauyin baki ba wajen fad'awa malam abin da ake ciki, sai dai shi baiji komai ba a zuciyar shi, sai dai yafi mayar da hankalin shi kan Usman da ya ke d'an ganin canji a tare da shi yanzun, da haka suka kwanta da fatan ganin wayewar gari lafiya.

Tunda safe Hajia ta had'a abin kari ta bawa Nura ya tafi ya kai ma su Haseenah, a lokacin Khadija na madafa da doguwar rigar bacci a jikinta Nura ya shigo, da kallo ta bishi har ya wuce b'angaren Haseenah kai tsaye kamar yanda Hajia ta fad'a mi shi, amma bai jima ba ya dawo dan gaisawa kad'ai ya yi da Haseenah ko jiki bai tambaye ta, falon Khadija ya lek'a sai Bilal kwance akan kujera, baisan da shigowar shi ba yace "Yarima barka da safiya."

Juyowa ya yi yace "Tonton Nura, ina kwana?"

"Lafiya lau, ka tashi lafiya?"

"Lafiya lau."

Ba tare da ya shigo ba daga k'ofar yace "Ina maman ka?"

"Ta na madafa." Ya fad'a da ma sa nuni da yatsarshi, hannu ya d'aga ma sa yace "Ina zuwa to." Madafar ya nufa da sallama, ya na ganin Khadija yace "Uwar gida ran gida, uwar gida sarautar mata, kowa ya shigo gida ke ya tarar, ko mai gida sai kin lamunce ya shigo, sannu da aiki."

Da wuk'ar hannunta ta nuna shi tace "Bansan dad'in baki, fad'i abin da ka ke so na ma ka."

Cikin had'e rai yace "Kamar ya? Ban gane me ki ke nufi ba?"

Kallon shi ta yi tace "Ai dana gan ka gidan ka to da dalili, bugu da k'ari kuma gashi har da min wani kirari kamar marok'i."

Dariya ya yi yace "Lallai uwar gida daban ki ke da kowace mace, cikin sakan biyar har kin fahimci akwai abin da na ke buk'ata ki min ko?"

Hararan wasa ta mi shi tace "Yau da gobe ai bata bar komai ba, karfa ka manta a hannu na ka k'arasa girma."

B'ata rai ya yi yace "Haba kema, basar mana."

"To naji, me ka ke so."

Saida ya matso kusan ta yasa hannu ya na cakurar dankalin da take soyawa ya na jefawa baki yace "Aunty Khadija maganar fa mai mahimmanci ce."

"Uhum, ina jinka."

Saida ya saci kallon ta yace "Aure na ke so."

Da sauri ta dakata daga abin da take ta kalle shi tace "Me? Aure fa ka ce Nura?"

"Eh mana, ko ban isa ba?"

Zaro ido ta yi tace "Ni bance ba, amma dai me zai hana ka bari kad'an k'ara mallakar hankalin kan ka, Nura aure fa ba iya abin da kawai ka ke tunani bane."

Kamar zaiyi kuka yace "To ni me na ce mi ki ina tunani?"

Mirmushin gefen labb'a ta yi tace "Ba ma irin wannan hirar da kai, amma na tabbatar ba zai wuce wutar balaga ce ke fizgarka ba."

"Kinsan me?" Ya fad'a ya na rik'e k'ugu, "A'a sai ka fad'a."

"Mijin ki ma haka yace da na masa magana, wai na bari har nan da ko shekara biyu, a gaskiya kuma ni ba zan iya ba, aunty Khadija wallahi gaskiya na ke fad'a mi ki, na fad'awa su Baba sunce ba ruwansu na fad'awa Usman tunda shine zai min auren, shi kuma yace ba yanzu ba."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yanzu me ka ke so na ma ka?"

Cikin sigar rarrashi yace "Ki daure dan Allah ki taimaka min ki ma sa magana, wallahi nasan zai saurare ki, ni fa har mun gama magana da iyayen yarinyar ma, sunce kawai na turo manya na."

"Babbar magana." Cewar Khadija, "Haba wannan k'arama ce, yanda na san ki da Abban yarima ai sha yanzu mgani yanzu ne."

"Sanin da ka yi mana ada ne wannan." Cewar Khadija a zuciyar ta.

Basarwa ta yi tace "Shikenan kar ka damu, zan jaraba na gani, amma ba lallai ya amince ba tunda har ya nuna bai yarda ba tun farko."

"Zai ma amince in dai ki ka masa magana wallahi." Da haka ya bar gidan ita kuma ta shiga tunanin yanda za ta fara tunkarar sabon Usman d'in ta da maganar nan, ba ma lallai ya saurare ta ba bare har ya amince da abin da Nura ke tsammani.
Chapter 51 · 0% Book details