Sashe 98
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Hawaye ne ya soma bin kuncinta, ganin haka shi kuma ya jawota ya rungume, daga haka ya cigaba da lallashinta dama kamar tana niman inda zata yi kuka, sai ta fashe da kuka mai sauti, kuma hakan ya taɓa zuciyarsa sosai da kyar ya samu tayi shuru ya lallaɓata suka tafi asibiti. Koda suka je gwajin farko ya tabbatar Najwa tana da shigar ciki, duk da Mujaheed baya son haihuwa amma kuma yayi farin ciki jin Najwa tana da juna biyunsa, wanda ya tabbatar hakan ƙila yasa ta sauko daga fushinta, kuma hakane dan itama ta yi murna jin nan da wata tara zata ganta da 'ya ko ɗa, haka suka dawo gida bayan ya siya mata magunguna da kayan ciye ciye. Mama koda ta samu labari itama tayi murna dan tana mugun son ganin jikokinta sun cika gida, wannan dalilin na samun cikin Najwa yasa ya kawo shiri a tsakanin Najwa da mama da kuma Mujaheed, duk da mama tace girka fa dole su haɗa amma batun wanke bayi da sharar tsakar gida ta ɗaga mata ƙafa har ta haihu, Najwa hakan bawai yayi mata bane amma dole ta haƙura dan taga in ta cigaba da ja dasu itace zata shiga ƙunci, sannan bata ga alamar zata bar gidan nan kusa ba sannan yanzu kodan abin da ke cikinta zara haƙura har ta haihu, ƙila zuwa lokacin su baba ko auren ya mutu ba zasu koreta ba.
***"*
Bayan wata bakwai.
Ikram ta haihu ɗa namiji yaci sunan baban Shamsu suna kiransa da Waziri ko suce baba ƙarami, ansha shagalin suna ba a magana dan a gidan Hajiya tayi jego ta hana ta koma gida. Bata yi arba'in ba Sameeha itama ta haihu 'ya mace nan Kaduna ta dawo aka yi komai yarinya taci sunan Hajiyarsu Ibrahim, faɗar shagali da irin kuɗin da aka kashe ba'a magana. A lokacin kuma matar Zaidu tana da ciki wata uku, dan wata biyar baya aka yi bikinsa gidan da Ibrahim ya bashi yana unguwar rimi katon gida da mota ya bashi, zuwa wannan watannin Zaidu ya zama alhajin kansa dan Ibrahim ya samar masa aiki a bankin CBN branch ɗinsu dake nan Abuja, duk weekend yake dawowa gurin matarsa. Najwa ta kasa zuwa bikin balle taga kayan baƙin ciki, dan har kuka sai da tayi jin zai yi aure ga kuma tarin arzikin da ya samu tayi dana sani da kaicon rabuwa da shi, sunan Ikram be bata je ba sai a sunan Sameeha ce inna ta matsa mata wanda har sai da ta nuna ranta ya ɓaci yasa ta shirya ta tafi da cikinta daya tsufa dan yana wata bakwai a lokacin, koda taje haka ta dinga raɓe raɓe su kuma sam basu nuna mata komai ba, anan taga yadda ake shagalin masu arziki da yadda arziki yake, haka ta dinga ɗari ɗari ta kasa sakin jiki Ikram kuwa sai janta take tana sakata cikin hidimar, dan walima aka yi kayatacce an raba abubuwa da yawa ciki harda kujerar umara ga wasu daga cikin dangi, inna ma ta samu da inna Rukayya ƙanwar umma da kuma wan babansu Sameeha, da sauran dangi daga cikin na su Ibrahim, sannan an raba atamfofi jakuna da kayan arziki, Najwa sai da ta kwana dan Sameeha ta hana ta tafi, ita dai ido take binsu da shi dan gani take ya kamar da gayya suke yin wasu abubuwan kuma har ga Allah su suna yin komai ne da tsarkin zuciya, kuma su sun mance duk abinda Najwa tayi musu suna son su cigaba da zumuncinsu kamar da, ita ko Najwa kamar ƙara ƙunsa mata baƙin ciki suke dan gabaɗaya mafarkinta tamkar su ta yiwa, haka ta tafi da sha tara na arziki zuwa gida duk da hakan ba wani burgeta yayi ba sai tarin damuwa data samu kanta a ciki, musamman yadda taga matar Zaidu tayi clean ta sauya kamanninta da Sameeha ya fito ga jikinta 'yar duma duma sai ta raina kanta dan ita cikin ta muni ya saka mata ga pimples a fuska da wani haske mara kyau, kuma ta rame saboda wahalar aikin gidansu dan hatta wankinta ita ke yi, ga ba abinci mai kyau, sannan ma wai matar Zaidu tana da motar da take jan kanta yanzu fa da itace a cikin wannan daular, kaico da cizon yatsa kawai ta ke yi dan tasan har abada ta saki damarta.
Sameeha tayi arba'in da wata guda Najwa ta Haihu Namiji yaro yaci sunan Abubakar Sadiq, ranar suna Mujaheed cewa yayi ba taro dan lokacin yazo tsakiyar wata bai da kuɗi da kyar ma ya samu ya saya ragon suna, Najwa har kuka tayi dan in har ba ai taro ba ya gama zubar mata da ƙima, dan taci buri a sunanta itama tayi abin arziki koda bai kai na su Sameeha ba, taso ayi shinkafa alale da waina da miya sai drinks, amma ganin hakan ba zai samu ba itama ta amince da ba zata yi suna ba, mama kuwa tace ba zai yuwu ba haihuwar fari dole ayi taro ba dole bane sai anyi ƙarya, zasu yi abinda Allah ya hore musu sannan bata so suyi karanta ga dangin Najwa ashe haihuwarta basu taɓuka komai ba, hakan yasa ta ciro tsohon ajiyarta ta je kasuwar Laraba ta auno masara ta bayar surfe da ɓarjin fate tayi cefane dana zoɓo ta dawo gida, ana gobe suna suka yi aita da yaranta da sauran 'yan uwa na kusa, washe gari suka girka katon tukunya suka sharɓa faten tsaki na alayyahu, Najwa kamar ta ɗaura hannu aka ta tsandara ihu, nan ta kira gida akan ba taro inna tace koda ba taro zata aiko mutane da gararta, dan haka zata aiko su goggo da shinkafa loka goma da kuma cefane zasu zo su girka anan wanda zata sallami baƙinta, to kawai Najwa tace mata dan tasan ƙaryanta ta ƙare.
Bangaren su Sameeha kuwa sun ci burin zuwa sunan Najwa musamman Ikram da bata san ɗakinta ba, hakan yasa da wuri suka haɗu a gidan umma da matar Zaidu suka haɗu suka tafi a motar Ikram dan itace ta jasu har da umma su huɗu, suka fara isa gidan inna suka sauke umma su kuma suka wuce gidan mai jego wajen ƙarfe sha biyun rana, sun shiga lokacin gida ya cika da 'yan uwan su Mujaheed sai sharɓan fate suke yi, ganin mata 'yan gayu yasa sai zuba musu gaisuwa suke su Sameeha suna amsawa suka wuce ɗakin Najwa da suka tadda 'yan uwansu a ciki waɗanda suka yi girkin shinkafa, bayan sun gaisa sai suka yiwa kansu mazauni a uwar ɗakan me jego wanda fuska muzu muzu ko kwallita bata yi ba saboda damuwa, Ikram da bata iya gani tayi shuru tace.
Ke meye haka? yau ranar murna amma kin zauna da fuska sai kace wacce aka yiwa mutuwa, dalla zo in miki kwalliya da ɗauri ki fito a amaryar ƙarni da kyau.
Gaskiya dai Ikram fito mana da mai jego tayi fes.
Cewar Sameeha kuma har zuciyarsu bada cin fuska ko zaulaya suka yi ba, Najwa kuwa sai taga kamar da biyu suka yi mata haka, hawaye ya kawo idonta amma sai ta shanye tana gaishe su suka amsa da fara'a a lokacin ne aka shigo musu da abinci, Sameeha tace.
Nikam ba zanci shinkafa ba ku kawo mini fate na sha na daÉ—e ban sha shi ba shi É—an sha'awa ne.
Ikram tace itama shi zata sha matar Zaidu ma haka, sai da Ikram ta yiwa Najwa kwalliya da ɗauri ta fito fes ita kanta data kalli kanta a madubi taga tayi kyau, nan suka saka ta ɗauki jariri suka dinga ɗaukar su har sai da suka gaji kafin Sameeha ta fita da kanta ta ɗebo musu fate suka zauna suna sha, Najwa dai sai kallonsu take taƙi sake jiki dasu balle suyi hira, sai ta zama kurma tana jin hirar da suke yi na business da Sameeha ta fara na sari kaya daga Dubai, Ikram tana cewa ita kiwo zata yi na kaji da kifi a bayan gidanta wanda Shamsu ya ware mata million biyu so take ta yi magana da Yaya Zaidu ya samo mata wanda zai kula mata dasu, Matar Zaidu kam cewa tayi ita shagon Saloon Zaidu yace zai buɗe mata a jikin gidansu dan har an fara gida shagon ma, haka suka dinga hira a tsakaninsu gwanin burgewa, Najwa ko wani irin hawaye taji yana cika mata ido amma dole take shanyewa dan kar su gane halin da take ciki, fuskar yaronta kawai take ta kallo tana shafa gefensa wanda sosai kamanninsa ya fito na Mujaheed, sosai ta kamu da soyayyar yaron wanda take jin zata iya cigaba da zama da Mujaheed dalilin yaron dan itama in tace yanzu bata son Mujaheed tayi ƙarya, kawai dai bayi da wadatar da take so ne, musamman ma yadda taji su Sameeha suna hirarsu ji take dama ita ce amma ƙaddararta a talauci ya zo, duk da itace da kanta ta nesanta kanta da arziki, su Sameeha suka cigaba da hirar bikin Aminu wanda zai auri yar uwar Shamsu, ɗan tuni ya warke sarai ba sauran ciwo, auren ma ba zai samu zuwa ba yana London in an ɗaura ne Sameeha da Ibrahim, Ikram da Shamsu sune zasu yiwa Amarya rakiya zuwa London daga can kuma zasu wuce Saudiya suyi Umara kafin su dawo, Najwa baƙin ciki goma da ashirin yanzu fa da ita ce tare da Aminu a London, ko dan wannan ɗaukakar da ta samu ai dole tayi gogayya dasu Sameeha amma kuma Allah ya ƙaddara aurensu ba zai je ko ina ba.
Su Sameeha leshi mai tsada da atamfa biyu suka bata tare da kayan yaro kala biyar da takalmi ɗaya masu tsada, Najwa tayi musu godiya. Bayan La'asar aka kawo mata gararta buhun shinkafa da su mai da dai kayan da ya dace da tamfofi da kayan yaro, ba ƙaramin gara suka yi mata ba kuma hakan ya ƙara fito da ita sosai a gurin dangin miji. Da su Sameeha suka tashi tafiya ta ce Najwa ta bata account number ɗinta,ta karanto mata nan take ta tura mata dubu ɗari biyu tace.
Nasan ba zaki taɓa tambayarmu abu ba duba da abubuwan da suka faru a baya tunda har yanzu kin kasa sake jiki damu mu dawo kamar da, amma ina roƙonki dan Allah Najwa in kina buƙatar abu ki sanar da ɗaya daga cikinmu, hatta yaya Zaidu wanki ne kuma zai miki duk abinda ya dace, sannan wannan kuɗin dana tura miki ki yi tunani ki fara business dashi In Sha Allah lokaci zuwa lokaci zaki riƙa ganin alert daga gunmu, ki maida komai ya wuce muyi zumuncinmu.
Hawaye kawai Najwa take yi wanda tsantsar damuwa ce da tarin kunyarsu da ke damunta, ta ce ta gode sosai kuma itama komai ya wuce, haka suka yi mata sallama su barta a tsaye tana juya wayarta da mamakin kuɗin da ta tura mata, wannan shine mafarkinta ace ita ce take taimakonsu amma yanzu itace a kasansu kuma tasan har gaban abada sunyi mata nisan da ba zata taɓa kamo su ba sai dai wani ikon Allah, tabbas Abin da ciwo domin yana yi mata ciwo a zuciya wanda ba tada yadda zata yi haka ƙaddararta tazo, da wannan cutar Hassadar zata koma ga Allah dan ya riga ya nuƙurƙusa zuciyarta wanda sai wani ikon Allah ne zata daina jin haka a ranta.
Ƙarshe.
Alhamdulillah!
Allah ya yafe mana kurarren ciki, alkhairin ciki Allah yasa muyi tarayya a cikin ladan. Ameen.
Taku ce
Rahma Kabir
Sai mun haÉ—u a sabon littafina nan ba da jimawa ba In Sha Allah.