← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 98

Sashe 50

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun dawowarsa daga Kaduna yaran suka dameshi akan ya mamansu me saya bai zo tare da ita ba? sai yace bata nan tayi tafiya, haka suka dinga yi masa naci kullun sai sunyi zancen mamansu, wanda daga karshe Amrah saida tayi rashin lafiya duk na ƙawazucin uwa, baba Saude sai da ta saka baki akan ya yi hakuri ya haɗasu da mamansu ko a waya ne hakan zai rage musu damuwar da suke ciki. Shawararta yabi shine ya cire Number ɗin Sameeha daga blocking jiya ya kirata suka yi magana da yaran, hatta shi yana cikin tsantsar kewarta da son jin muryanta har da son ya ganta, duk da a yanzu ba aure a tsakaninsu, shi ya saka musu a handsfree yana jin muryanta yadda take rawa da kuka duk sai yaji ya karaya yaji kamar ya zaluncesu daya rabata da yaranta tunda ita tace zata iya zama da shi a haka, kuma zaman da yayi da ita ya kula bata ma yarda sha'awarta tana motawa, ko 'yan dabaru da yake yi mata bata wani damu ba wani lokacin sai ya ce zai yi ne take bashi dama amma bata wani damu da yayi ba, yanzu ne yake ƙara jin Sameeha ba zata aikata abinda yake zargi ba duk da akan idonta yaga komai amma zuciyarsa taƙi bashi damar yarda da hakan. Da ita ya kwana harya wayi gari wanda koda yaje aiki da tunanin a zuciyarsa, da ya bar gun aiki ya tsaya ya siya wa yaran ƙaramar waya ya saka musu sim akan su riƙa yin waya da mamansu, dan ya ɗauki alhakinsu daya nima shiga tsaninsu yanzu ne ya gane baya akan daidai. Yana cikin tuƙi kira ya shigo wayarsa sai da yayi parking a gefen hanya kafin ya duba dan yanzu yayi hankali baya ɗaukar waya in yana tuƙi saboda hatsarin daya yi a baya harvya jawo masa silar rabuwa da matarsa abar sonsa. Yana duba wayar yaga Najwa ce dan ko saving number ɗinta bai yi ba ya dai riƙe number ɗin musamman haruffan farko da ƙarshe, yaja guntun tsaki yana shirin kira sai ga shi ta sake kira ya ɗauka suka gaisa sai yayi shuru yaji uzurinta.

Dama na kira na gaisheka ne.

Ok na gode ya makaranta ko bakya zuwa.

Ina zuwa makarantar Hadda amma munyi hutu ina gida.

Masha Allah boko a ina kika tsaya?

Secondary na tsaya amma ina burin inna yi aure zan cigaba.

A wani gidan? Ba dai a gidana ba ko, dan ko matata da muka rabu bata cigaba da karatu ba saboda bana buƙatar haka.

Wani dum Najwa taji ya turnuƙota daya kawo zancen Sameeha, sai da ta haɗiye miyau kafin ta cigaba da cewa.

Kila ita bata da ra'ayin cigaba ne shiyasa amma ni burina kenan na cigaba da karatu dan Allah karka hanani.

Aiko babu cigaba da karatu a gidana kamar yadda na hana Sameeha itama taso cigaba amma saboda na nuna bana so ta hakura, dan haka idan kina so ki cigaba da karatu sai a jinkirta auren koma a fasa ki yi karatunki karna daƙile ki.

Dam dam ƙirjinta ya buga lallai akwai jan aiki a gabanta, ta nisa a hankali.

To ba damuwa na haƙura.

Ya dai fi miki dan ki sani yadda na tafiyar da gidana a baya haka ma zan É—aura a yanzu babu abinda zai sauya mini ra'ayi. Ni ina kan hanya sai anjima ki gaida mutanen gida.

Yana kaiwa nan a maganarsa ya kashe wayar, ya kunna motarsa ya wuce abinsa. Najwa kuwa bin wayar tayi da kallo wani ƙululun baƙin ciki ya tokare mara wuya, ta kalli Nafeesa da suke tare da duk taji hirar da suka yi tace.

Anya Nafeesa mutumin nan zai juyu mini yadda nake so, kin ga yadda yake magana cike da gadara har yana sako mini zancen Sameeha.

Najwa ina ga sai munyi yadda Binafa tace akan mu É—an kauce hanya, Wlh mazan yanzu sai da mallaka balle kinga ke ga a yadda zaki yi auren, ina ma jin tsoro kar ya gane ke ce yace ya fasa ko kuma bayan auren yace zai sake ki.

Nafeesa ki bani mafita wlh kaina yayi murfi ina cikin tsaka mai wuya, ga biyan buƙata amma ba kwanciyar hankali.

Ai samun natsuwarki sai kin kama shi a hannunki Najwa dan wlh ina jiye miki zaman doya da manja da zaku yi da shi. Kawai hakanan zaki É—aure mu nimo Binafa ta rakamu inda za a yi miki aiki ki samu kansa tun kafin ki shiga, in dai kina son zamanki dashi ya É—aure.

Najwa shiru tayi tana tunani dan tunda aka saka ranarta da Aminu bata wani cikin sukuni kullun cikin fargaba da zullumi ga shi kuma yadda yake nuna mata ko in kula ita ke kiransa kullun bai taɓa ɗaga waya ya kirata ba, koda ta yiwa Hauwa ƙorafi tace ta kwantar da hankalinta zai daina ne ta bashi lokaci, ita kam bata ɗaura niyyar yin aurensa ta fito ba, tana so ta aureshi sai mutuwa dan shine cikar zaɓinta wanda kullun take mafarkin samu, ga kyau ga kuɗi ga kuma nasaba sosai take ƙara jinsa a zuciyarta wanda take jin duk wanda ya nima rabata da shi to zata iya yin komai dan ganin bayansa, ta nisa cikin sanyin jiki.

Dole na nima mallaka dan ina son zamana dashi ya ɗaure har abada. Ke ko Hauwa ce ta nima shiga gonata bazan raga mata ba akan Aminu dan yadda na iya rabashi da matarsa yar uwata to da kowa ma zan iya rabashi wlh, kira mana Binafa muji a ina zamu haɗu dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe, tunda da kuɗin da ya tura mini kwanaki ban kashe ba to ga ranar amfaninsu.

Da kyau 'yar gari gwara ayi komai a wuce gurin.

Cewar Nafeesa tana danna number ɗin Binafa ta kira ta tambayeta ina take, Binafa tace tayi nisa sai dai gobe In Sha Allah su haɗu wajen tara na safe a gidansu sai suyi magana, a haka suka kashe wayar ta faɗawa Najwa yadda suka yi, sai suka cigaba da hira gabda magrib Najwa ta bar gidansu Nafeesa daya zame mata jiki kusan kullun sai ta je, dan a nan suke ƙullu duk wata munafurcinsu, a cewarta a gidansu inna tana kusa bata so taji komai.

Washe gari da wuri Najwa tabar gidansu ta isa gidansu Nafeesa, sai wajen goma suka tafi gidansu Binafa, suna zuwa ta shirya dan tun jiya a chart Nafeesa ta sanar da ita inda suke so ta rakasu, sai kawai suka fita a motarta zuwa gidan wani malami dake can Mando, koda suka shiga ba kowa dan haka Binafa ta koro masa bayanin abinda ya kawo su, nan ya yi surkulensa a ƙasa tare da yin zane, yayi surutai marasa kan gado wanda yake muna wannan boka ne ba malam ba, sai da ya gama kafin ya dubesu yana cewa.

Ba zaki taɓa mallakeshi ba sai in an raba zuciyarsa da matar da ya saka dan yana sonta sosai fiye da lissafi, saboda haka ki kawo mana kyallen zanin matar daya saka za muyi aiki da shi.

Najwa taji kanta ya sara mata dan bata san inda zata je ta samu kyallen kayan Sameeha, sai ba tace cikin rauni.

Babu wata hanya dole sai anyi haka.?

Hanga ɗaya ce idan baki samu kyallen zaninta ba to ki kawo warin takalminta guda ɗaya, idan duk baki samo ba to ki saka a ranki bake ba mallake mijinki dan tabbas zaki aure shi amma akwai tarin matsaloli da zasu biyi baya. Zaku iya tafiya idan kin samo abinda muke buƙata sai ki kawo a fara aiki.

Da wannan zancen nasa suka fito suka zauna a cikin mota Binafa tana cewa.

Najwa kina ruwa dan akwai kura, yanzu ya za a yi mu samu abinda boka ya buƙata.

Gidan zanje in samo warin rakalminta dan shi zaifi sauƙin samu, Binafa muje ki sauke mu a kawo ni da Nafeesa mu tafi gidansu.

Kina ganin zaki samu fuska dan kince kin daina shiri dasu.

Zan samu mana dan Umma tana da saukin hali Sameeha ma haka, Ikram ce dai 'yar rainin hankali.

To sai kun dawo mu ji in zai yiwu mu koma gun Bokan a yau.

Cewar Binafa sai ta saka key a mota suka wuce. Tana zuwa kawo ta samu guri tayi parking suka sauka sai ta wuce su kuma suka tsallako suka samu napep suka wuce gidansu Sameeha.

*****

Sameeha.

Sai da suka idar da sallar isha'i kafin suka zauna a falon umma suka shiga firar walima, wanda a lokacin ma suka baje kulolin abinci da kayan ciye ciye suna ci suna hira, a haka Zaidu ya shigo ya same su shima aka cigaba da cafta dashi, sosai suka yaba kirki da karamcinsu umma ta É—aura da cewa.

Gaskiya mutanen kirki ne Allah dai ya saka musu da alkhairi, ni wlh Allah yasa wannan yaro da gaske yake ya turo ayi magana kawai dan na gaji da zancen jiran Aliyu.

Wlh umma nima abinda na faɗawa Ikram kenan, zan bincika Khairy naji ya suke dashi, na san ba zata ɓoye mana komai na shi ba, Allah dai ya tabbar mana da alkhairinsa.

Cewar Sameeha umma ta amsa da amin kana suka cigaba da hira Zaidu yana cewa Ikram ta shiga hankalinta dan ba a yada irin wannan dangi masu mutunci ba irin su Hauwa ba, ai baya fata wata 'yar uwarsa ta faÉ—a ga dangin miji irinsu. Ba dan ma Aminu lokacin a tsaye yake ba da tuni sun kashewa Sameeha aure, nan dai suka dinga mayar da zance har lokacin barci yayi kowa ya kama hanyar gun kwanciyarsa.

Da safe.

Suna gama karyawa sai suka koma barci sai wajen sha biyun rana Ikram ta haÉ—a wanke wanke tana cewa Sameeha da ke haÉ—a wutar gawayi.

Waye zau mayar da kulolin nan Anty Sameeha.?

Idan saurayinki yazo anjima sai mu bashi ya mayar musu.

Kai Anty ya zaki ce haka mutumin da bai samu matsuguni ba.

Zaima samu ne Ikram kuma...

Sallamar da Su Najwa suka yi yasa Sameeha yin shuru har suka ƙaraso cikin gidan fuskarsu ɗauke da murmushi, Ikram kuwa ta haɗe rai ta cigaba da aikinta.
Chapter 50 · 0% Book details