← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 98

Sashe 54

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sameeha zan baki lokaci ki zauna kiyi tunani da addu'a, idan har ban kwanta miki ba zan janye daga maganar aurenki domin farin cikinki shi nake so, amma ki sani ina ƙaunarki ina jinki har cikin jini na da ruhina, bana jin na taɓa jin irin ɗanɗanon sonki akan wata mace, ko Mubeena dana sota a baya banji irin haka akanta ba, ki je gida ni zan wuce sai da Safe ki gaida su Umma.

Ya ƙare maganar cikin rawar murya dan sosai yake jin ya fashe da kuka ko zai samu sauƙin yanayin daya samu kansa a ciki, sai a lokacin Sameeha ta ɗago kai sai caraf suka haɗa ido dan akwai hasken wutar mota ɗaya kunna na ciki, wani irin abu ne nan take ya kai sako a idanunsa tamkar walkiya, kuma hakan yayi tasiri a illahirin jikinsu, dan wani shokin ne ya tafi da sauri cikin jijiyoyin jikinsu, wanda hakan yasa Sameeha ta sunne kai tana sauke ɓoyayyan ajiyar zuciya siririn hawaye ya sauka a kuncinta, Ibrahim ya hura iska mai dumi daga bakinsa yana jin wani yanayi na sanyin AC yana ratsa shi tamkar zazzaɓi yake ji, sai ya juya ya gyara zamansa yana jiran ta fita daga motar ya ja, amma sai ya tsinkayi muryanta tana cewa.

Ba sai ka bani lokaci ba domin na amince da aurenka, fatanmu Allah yasa hakan ya zama alkhairi a garemu. Kayi haƙuri da yanayi na yau bana jin dadi ne, idan kaje gida ka gaida mini da Hajiya da kowa sai da safe.

Ta ƙare maganar tana yunƙurawa zata fito daga motar, da Sauri Ibrahim ya buɗe ya riga fitowa ya isa inda take zaune ya tsaya a jikin ƙofa yana dubanta, itama miƙewa tayi ta tsaya suna kallon juna, Ibrahim ya saki miskilin murmushi.

Kina son aurena kika yi da fuska kamar kinga mutuwa, bai kamata matar Ibrahim ta kasance a haka ba.

Kaifa kace baka son mutane susan kaine a nan, ya kamata ka bani hanya na wuce ka koma cikin mota,

Sameeha kowa ma ya ganni in dai dake nake a tare bani da damuwar komai, yanzu dai ki saki fuskarki kuma ki gaya mini me yasa ki fidda kwalla.

Hmmm ka bani hanya na wuce.

Ibrahim sai ya matso gabda ita kamar zaiyi kisin ɗinta, sai tayi baya da sauri ta zauna daɓar a seat, sai ya koma ya risina yana cewa.

Hawayen zan goge miki dan akwai sauran damshinsa a fuskarki, kar ki shiga gida ace na bigeki daga zuwa hira kija mini Yaya Zaidu yace ya fasa bani ke.

Wannan karan murmushi tayi tana cewa.

Tunda nace naji na gani ba wanda zai hana maka ni.

Allah da gaske kike yi? In dai haka ne zo ki shiga gida. Amma dai duk in kina cikin tunanin wani abu ki tuna ni Ibrahim Khalil ina sonki ina kaunar kasancewa dake.

Yana gama faɗar haka ya matsa ya buɗe mota ya shiga ya kunna, Sameeha ta fito ta rufe masa ƙofar ta tsaya jikin tagarsa tana dan murmushi.

Allah ya tsare hanya ya huta gajiya.

Amin matar Khalil ki É—aure ki aje number na a wayarki, kuma inna kira a É—auka kinji ranki yadade.

Ya ƙare maganar yana yi mata jinjina da babban yatsarsa na hannu, sai da ta saki murmushi kana ta juya ta soma tafiya, har ta kusa shiga gida taji ya kira sunanta ta juyo sai ya lumshe mata ido ya buɗe yana sakin kayataccen murmushi, bata san sadda ta mayar masa da murmushin ba kana ya ja mota ya wuce ita kuma ta shiga gida. Sosai Ibrahim ya soma tasiri a zuciyarta, bata taɓa zaton zai kasance mai sauƙi har haka ba, lokaci guda ya yaye mata damuwar Aminu wanda hakan yasa ta shiga gida fuska sake, ko da su Umma suka ganta haka ba wanda ya tambayeta domin sun san dalili, haka ta kwana tana tuna Ibrahim da magnganunsa wanda In ta tuna Aminu sai ta ji ba wani ɓacin rai sosai da take ji kamar ɗazun, Ibrahim ya maye mata gurbin damuwarta, a karo na biyu tana jin sata sake bawa soyayya dama domin ta ƙara kwankwaɗar zaƙinta, dan ga dukkan alamu Ibrahim wayayye ne kuma ɗan zamani, wataƙila ma yafi Aminu iya wasu abubuwan, musamman fannin nuna soyayya a zahiri.

*****

Tum daga wannan ranar Ibrahim ya cigaba da kafa gwamnatinsa a zuciyar Sameeha, tun tana noƙewa har ta soma sakin jiki dashi suna hira, sai dai sunfi yin waya saboda baya zama, a hankali Sameeha ta yakice damuwar Aminu ta fuskanci gaskiya, kuma tun ranar daya kira bai kuma kiranta ba sai dai waya da take yi da yaranta, sannan ta zage sunata shirye shirye duk da ba wani shagali zasu yi ba saboda ita bata ƙaunar bidi'a Umma ma tace ba zasu yi komai dan albarkan aure take buƙata. Shamsu kuwa ya gama samun zuciyar Ikram, sosai yake samun damar zuwa hira kuma bata taɓa jin ta gaji da ganinsa ba dan ta kamu da sonsa na bazata, gabaɗaya ko wani ɓangare shiri suke na biki.

Itama Nabila tanata nata shirin saboda tunda taje gurin malamin da Shema'u ta rakata ya yanko mata maƙudan kuɗi tace ba zata iya ba, dan bata yarda tayi asarar kuɗi ba tunda ta samu labarin an gama maganar aure biki ya rage, a kan haka saida suka yi faɗa da Shema'u kan ta bata kunya a gun malam, daga baya ne suka shirya ta cigaba da sabgoginta, domin Ibrahim miliyan biyar ya tura mata akan ta ƙara jali sannan ya ce ta faɗi kuɗin da zata haɗawa kanta a kwati, tace miliyan shida shima bai musa ba ya bata dan a zauna lafiya tunda bata nima ɗaga masa hankali ba, hakan yasa taji aurensa ma bai wani dameta ba tunda ya bata wannan kuɗin, ita kuɗi sune rayuwarta bata yarda tana wasa da su ba, shiyasa sam bata bin malamai a ganinta asara zata yi, tunda gashi bata je gunsu niman sa'a ba amma tana samu kasuwanta yana bunƙasa.

Najwa kuwa danne duk baƙin cikinta tayi ta shiga jikinsu Sameeha dan ayi biki da ita taga duk abinda suke shiryawa, tun Ikram bata sake mata ba har ta mance komai suka cigaba da hidimarsu, duk da a gun Najwa na ciki na ciki.

*****

Biki saura kwana biyar.

A ranar ne aka kawo akwatin su Sameeha wanda set bibbiyu ne, set na farko guda biyar da kit, na biyu kuma uku da kit, babu bambanci a kayan da aka zuba sai zinarin Sameeha da yafi na Ikram tsada, da kuma key motarta da aka saka yafi na Ikram ɗin, gida ya cika da 'yan uwa ana kallon kayan arziki bayan dan ginsu ango sun tafi, Khairy dai tana nan maƙale da Sameeha dan kusan tafi zuwa gidan akan can gidansu. Najwa kamar zata haɗiye rai dan baƙin ciki, jikinta har wani ɗumi ya ɗauka ta kasa tsayuwa sai ta zauna tana kallo yadda ake ɗaga kayan arziki, Inna Rakiya kanwar Umma tace.

Ni wlh nama kasa magana da ganin waɗannan kaya, ina ganin mijin Sameeha yafi na Ikram kuɗi dan wlh sarƙar zinarinta tafi tsada nesa ba kusa ba, ga motar ma sun faɗa. Wai yaya wani miji ne Sameeha ta samu haka? Kunga fa manyan leshi da atamfa da iya ganinka baka san ya zaka daɗi kuɗinsu ba, jama'a ban taɓa ganin akwati haka ba wlh tunda nazo duniya, ko aurenta na farko wane da wannan kaya.

Nan fa kowa ya shiga faÉ—ar albarkacin bakinsa ana ta yaba kaya, umma dai dariya take ta yi ta kasa rufe baki, innar Najwa tace.

Wannan yara ai sunyi goshi suna da ƙashin arziki Allah ya basu, ita Sameeha ta bar gidan kuɗi ta ƙara faɗawa gidan daya fi na baya ma, dan ganin kayan nan ya nuna babban mai arziki ta samu, Ita kuma Ikram ta faɗa gidan sarauta wanda ko a mafarki bamu taɓa zaton haɗa jibi da mulki ba. Kai Alhamdulillahi haihuwa tayi mana rana, ina ma ace yaya yana raye yaga wannan ranar farin ciki haka, Allah ya jikanka yaya Amadu, bayanka tayi kyau wlh.

Ta ƙare maganar tana matsar kukan farin ciki, haka dai kowa yake faɗar albarkacin bakinsa, Najwa kuma tana ƙara shiga tashin hankali na baƙin ciki kamar ta haɗiye rai ta mutu, bata iya jurewa ba ta miƙe ta fice ba tare da an kula da ita ba, ta tari napep ya wuce da ita tana matsar kwalla dan sosai taji baƙin ciki da ƙunci ganin akwatinan su Ikram, bata taɓa zaton zasu kai haka ba, yanzu ne take ƙara raina kanta dan tabbas darajar raƙumi yayi nesa da ƙasa, sun yi mata fincinkau a komai, dan tasan wlh Aminu bai da kuɗin da zai yi mata irin wannan kayan, saboda a cikin arzikinsa da zuciyarta take hasashe bai kama ƙafar mazajen su Sameeha ba, ji take kamar tsiya da talauci a kanta a ka ƙare, sam bata taɓa samun saurayi mai mugun kuɗi ba sai dai 'yan kuci ku bani, ita dai tana ganin kyanta bai amfaneta da komai dan da kyau zai jawo mata arziki da sai ta auri mijin daya taka na su Ikram, amma sai gashi ta ɓige da auren mijin da Sameeha ta bari bisa cin amana, wanda ma bata da yaƙinin zaman auren zai yi mata daɗi, haka ta dinga share hawaye tamkar wacce aka yiwa mutuwa.

*Duk wacce ta karanta mini littafi bata biya ba, ta sani ta karanta da hakkina kuma In Sha Allah sai Allah ya saka mini.*
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

36.

Najwa gidansu Nafeesa ta wuce, ko da ta isa ta samu suna shirin zuwa dinner É—in wata 'yar kanwar Hajiyarsu, amma a yadda Nafeesan ta ganta yasa ta jata É—akinta suka zauna gefen gado tana dafa kafadar Najwa.
Chapter 54 · 0% Book details