Sashe 18
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma yaya Hauwa wannan ba magana bace, karki wasa da damarki dan Wlh in kika bari girmanki ya zube a idona ba zamu kwashe ta daÉ—i ba, tunda ba haifata kika yi ba da zaki rika iko dani dududu shekara biyu kika girme mini, ina kokarin baki girmanki kuma....
Kai Aminu ka daina wannan maganar bana son haka, anzo nan a sulhunta ne ba a yi rikici ba.
Cewar Kamalu, Hauwa ta ce cikin faÉ—a.
Ka barshi ya nuna min ni banda mutunci a idon matarsa taji daÉ—in raina ni, ko da yake ma ta gama raina ni É—in tunda bata É—auke ni a bakin komai ba, to wlh in ita ta shanyeka ni bata isa ba kuma mun barka da ita.
Hauwa bana son sakarci ba hayaniya na kira muyi ba, yanzu dai ko wanne yayi hakuri ya mayar da fushinsa, ke Sameeha kiyi hakuri kuma ina so ki basu haƙuri idan da da akwai abinda kika yi wanda baki sani ba, in dai hakan zai kawo maslaha tunda ke ce ƙarama.
Haba yaya ita da aka muzgunawa itace kuma zata basu haƙuri, ku duba wannan lamarin fa, a gaskiya ni ban kawota dan ku danne mata hakki ba, sune ya dace su bata haƙuri domin kowa ya san gaskiya a bayyane take, yaya Hauwa itace shugabar kawo rikici kuma saboda sun rainata har Adama ta iya saka baki tana gayawa Sameeha magana bata iya tsawatar mata ba, to ni ina son matata kuma nasan halinta ba mai son rikici bace tsawon shekara goma da nayi na ita nasan wacece ita, dan haka Sameeha tashi mu wuce kuma In Sha Allah gobe zamu bar garin nan gabaɗaya sai in sun ganta su nemi ci mata mutunci.
Yana kaiwa nan a maganarsa ya miƙe a fusace dan sosai ransa ya ƙara ɓaci, Kamalu yace cikin faɗa.
Ya zaka ce haka, kana so ka nuna mana mu bamu isa da kai ba ko, to tunda mu ba muda muntunci sai ka tafi É—in.
Gwara dai ya nuna muku Sameeha ta gama da shi, in ba haka ba yana cikin hayyacinsa ne zai gaÉ—i maganganu son ransa saboda mace.
Cewar Hauwa, Aminu yanuna ta da yatsa.
Idan kika kuma faÉ—in magana mara daÉ—i akan matata wlh saina É—auki mataki, domin na kula kin yarda girmanki kare yaci.
Ni zaka faɗawa haka? dan ubanka kama isa ka riƙa fada mini magana haka, mace tana son raba mana zumunci kace kar ayi magana, ni kake dagawa yatsa saboda tsinanniyar matarka...
Ni ba tsinanniya bace wlh, Abban Amrah mu tafi kawai dan banga alamar za a yi sulhu a nan ba.
Cewar Sameeha a fusace data miƙe ta kama hannun Aminu ta soma janshi, su Alhasan suna cewa su tsaya amma ina sunyi gaba, Hauwa tace cikin ɗaga murya.
Taya zai tsaya ya zama jani talau, uwarsa ta bashi umarni ya kama kai ya tafi, Allah ya waranki Sameeha, yadda kike niman bata mana zumunci Allah ya mayar miki da aniyarki, matsiyaciya har gidan ƙananan mutane...
A fusace suka ga Aminu ya dawo ya isa kan Hauwa ya daga hannu zai kifa mata mari, Yaya Kamalu yayi saurin tare shi ya fizgo hannunshi ya sauke masa mari a kuncinsa, Aminu ya dafe kunne yana dubansu. Alhasan yace cikin ɓacin rai.
Allah ya kyauta, Aminu kayi matuƙar bani mamaki ba haka su Abba da umma suka tarbiyyantar damu ba, ke kuma Hauwa kece musabbabin komai saboda kin mayar damu 'yan iska bamu isa dake ba, shiyasa gashi ba aje ko ina ba Aminu yana niman raina ki, kuma da gaskiyarsa dan babu wanda za aci zarafin iyalinsa bai ji haushi ba, dan haka ki fita idanuna kafin in yi miki wulaƙanci.
Shikenan yaya ba za a fadi gaskiya ba zaku yi mini taron dangi, yau ni har Aminu yake niman marina saboda mace..
Hauwa ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, Aminu bai iya cewa komai ba face hakuri daya basu ya juya ya fice daga falon idonsa yayi jajir saboda ɓacin rai, shi mutum ne mai zuciya amma kafin yayi shi sai an kai goro an kai bari. Su Alhasan gabaɗaya suka mayar da fushinsu akan Hauwa, suka yi mata tas tare da tunatar da ita gabaɗayansu arzikin Aminu suke ci, banda Allah yasa shi mai tausayine da dukkansu suna cikin halin rayuwa, koda yaushe cikin yi musu hidima yake bai taɓa gazawaba, dan haka bai cancanci haka daga gunta ba dole ta sauke girmanta suje har gida su bashi hakuri domin shi aka yiwa laifi kuma akan gaskiya yake saboda ita Hauwa ta kasa riƙe girmanta, sannan tayi amfani da kausasan maganar da ya ƙara fusata Aminun har ya nima marinta, suka koma kan matansu suma suka yi musu kaca kaca sai da suka basu haƙuri, kafin suka sauko kana suka ce bayan sallar magrib zasu je gidan Aminu domin ayi sulhu, Hauwa dai dole suka yi mata amma ason ranta ba inda zata, tsana da kuma kiyayyar Sameeha ya ninku a zuciyarsu ita da Laure dan sosai suke jin zasu iya komai dan su fitar da ita a gidan Aminu.
****
Sameeha.
Koda suka fita Sameeha ce taja motar suka koma gida. Suna isa ya wuce falonsa ta bishi a baya tana lallashinsa, hawayen da yake dannewa ne ya sauka akuncinsa yayi saurin shafewa yana yawq cikin dakiya.
Ina so ki haÉ—a kayanku na sawa da komai na amfaninku gobe In Sha Allah zamu bar Kaduna.
To tace masa ta miƙe ta fita dan itama ta gama yankewa gwara ta bishi saboda hakan ne kaɗai zai kawo karshen rikicinta dasu, tana son mijinta tana kuma son farin cikinsa ba zata cigaba da biyewa 'yan uwansa ba su kawo musu tasgaro a cikin zamansu ba. Ta samu Ikram a ɗakinta ta bata labarin abin da ya faru, jikin Ikram a sanyaye tace.
Gwara ki bishi kawai komai ya zo karshe, dan babu amfanin baÉ—i ba rai, tunda su Hauwa ba zasu fasa ba sun riga sun tsaneki, Allah ya shiga tsakaninki dasu, sai ki dage da addu'a, bari na tayaki baÉ—a kayan su Abi.
Tana gama faɗar haka ta fice ta wuce ɗakin Amrah ta fara haɗa mata kaya. Sameeha zama tayi a bakin gado ta rafka tagumi, itama ranta a ɓace yake, ta shiga tunanin me ta yiwa Hauwa da zafi haka data cancanci wannan natsar, wayarta ce ta yi ƙara ta duba taga Umma ce ta kirata, ta ɗauka cikin sanyin murya, kamar tana jira umma ta tambaya lafiya? Sai ta fashe mata da kuka tana bata labarin abinda ya faru, Umma tace cikin lallashi.
Kiyi hakuri ki barwa Allah, ke dai dangin Aminu sune jarabawarki, kuma ma dole su tsaneki tunda kina cikin wadatar da suka kasa danne hassadarsu, dan haka ki tattara kibi mijinki kamar yadda ya faɗa, ai da nan da Abuja baki da hanci ne ko a rana guda zaki zo ki koma, Allah ya shiga tsakaninki da sharrinsu, kuma ki dage da addu'a kina yawan sadaka dan wallahi ki guji mutumin daya nuna miki ƙiyayya kiri kiri, dan bai ki ace kin mutu ba.
Nan dai ta dinga bata baki har ta samu natsuwa tace mata anjima bayan Sallar isha'i zasu kawo Ikram gida daga nan suyi sallama tunda yace jirgin kasa na safe zasu bi, daga haka suka yi sallama. Sai ta miƙe ta soma haɗa kayanta tana jin wani sanyi a ranta akan maganganun da umma tayi mata, itama sai yanzu daga dacewar ta matsa kusa da mijinta su cigaba da rayuwa, dan ta san in tana nan ba zasu taɓa barinta ta samu sukuni ba.
Ana yin sallar magrib su Kamalu suka haɗu suka tawo gidan Aminu, da suka iso kofar gate suka yi parking Sai duk suka fito, Sa'a ta buga gate mai gadi ya buɗe musu sai suka shiga ciki. Koda suka isa falon sun murɗa handle suka ji a rufe sai suka buga Ikram da take falon taje ta buɗe, tana ganin sune ta juya ta koma ciki ta shiga falon Aminu ta sanar dasu zuwansu sai ta fito ta gaishesu ta koma ɗakin Abi da shi ya rage ta gama haɗawa kaya, su Aminu suka fito suka ƙara gaisawa kamar ba komai, nan dai Alhasan ya shiga basu haƙuri kana ya cigaba da yi musu nasiha wanda yasa duk jikinsu yayi sanyi, dan shi kam Allah ya bashi baiwar iya magana gashi da ilimi Masha Allah, nan suka haɗu suka yafi juna Hauwa har da kukan munafurci tana niman gafarar Sameeha tare da basu hakuri, Aminu yace komai ya wuce haka itama Sameeha tace ta yafe, sai kuma suka ɓuge da hira, kiran Sallar Isha'i ne yasa mazan suka fita masallacin kusa da gidan dan suyi sallah, su kuma su Hauwa Sameeha tayi musu jagora zuwa ɗakinta dan suyi nasu sallar a nan, sai ta fito ta basu guri, nan fa suka shiga kashe kwarkwatan ido suna magana ƙasa ƙasa tare da zungura baki akan maƙudan kuɗin da aka kashe a ɗakin, dan hatta bayinta abin kallo ne dan duk sai da suka leka ko ina, da suka idar ne suka dawo falo dama Sameeha tasa Ikram ta dafa jelof ɗin kuskus da soyayyar kaza tsaf tsaf dan zu ci, da su Aminu suka dawo ne suka gabatar musu da abinci dinning su mazan suka ci akai, matan suka ci a nan carpet ɗin falon, bayan sun kammala ne suka yi bankwana dan Aminu ya tabbatar musu da tafiyarsu ba fashi gobe In Allah ga kaimu, basu ja ba dan basa so su tauye shi. Har gate suka yi musu rakiya suka wuce kana suka jero Aminu na cewa.
Ko dai zaki zauna É—in tunda naga komai ya daidaita kuma dama ba son zaman Abuja kike yi ba.
Ƙafata ƙafarka dan gwara na bika nima hankalina zai fi kwanciya.
Su Meehan Aminu masu miji, ko dai ko dai kinyi tunanin kar na samu wata a can ta É—auke mini hankali.
Haba dai Mijin Meeha dan ita kaÉ—ai aka yi shi ehe...