← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 98

Sashe 26

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bononza N300 saura yau da gobe In Sha Allah, zuwa monday zai koma asalin kudinsa N400. Labarin Sameeha ce wacce yarinyar kanwan babanta take son aure mata miji ta karfin cin tuwo, sai dai Sameeha ba tada masaniyar haka domin Najwa ta wasa wukarta wajen yi mata bita da kulli, cin dunduniya, makirci da zagon kasa dan ta samu damar fitar da Sameeha cikin sauki ba tare da an zargeta ba ta kuma aure mijinta cikin sauki. ABIN DA CIWO. Idan baki karanta freepages season 1 ba ki tuntubeni a number ta pc 09034940106. Duk wanda yasa kudinsa ya siya ba zai taba nadama ba domin zaki karu da ilimin zamantakewar rayuwa, babban tunatarwa ce sosai dan wani lokacin muna zaton wuta a makera ne sai mu tsinceshi a masaka.

Ko me zai faru? Ga Aminu yana hanyar dawo wa dan yana gabda shigowa gida...

Sameeha taci magani a cikin abincinta bata sani ba ta soma shiga wani yanayi na maye...

Binafa da Hanan suna cikin gidan wanda gabaÉ—aya shirinsu na safiyar asabar ne, sai kuma ga kuma Aminu yana hanyar dawowa. Me zai faru?

Shin burin Najwa yana cika? Ya ƙarshen ta zai zama?

Su Binafa suna cin sanara akan Sameeha kuwa?

Ya bikin Salma sai kazance da Su Hauwa suka ci burinsa.?

Burin Hauwa yana cika kuwa akan aurawa Aminu Najwa da kuma sakin Sameeha da take so yayi.?

Ya ko wanne yake karɓan sakamakon karshensa.? Sai mu tara a cigaban wannan labarin don samunsa kai tsaye har zuwa ƙarshe In Sha Allah.

Pay N300 to 0106956864
Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a tura MTN card N300 a 09034940106, masu so ta pc su tura N600. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

18.

Jamila.

Data shiga É—akinta da plate É—in abincin da Sameeha ta zuba mata sai ta cewa su Binafa.

Kunga ta zuba mini abincin kuma da maganin da na zuba mata a ciki.

Ki samu leda baƙa ki saka a bola, idan maganin ya fara aiki a jikinta ko ɗaga ƙafa ba zata iya ba dan haka ki shiga kitchen ɗin ki dafa mana indomie muma za muci.

Cewar Hanan data bata amsa, Binafa ta jefa mata baƙar leda data ciro a jakarta sai Jamila ta ɗauka ta juye taliyar a cikita ɗauke naman ta goge inda ya shafi abincin jikin zaninta ta fara ci dan in ta hakura da taliya wlh ba zata iya haƙura da naman ba, zancen data yi kenan a zuciya ta samu guri ta zauna tana yagar naman, Binafa ta kalleta tana cewa.

Naman ma ba zaki iya haƙura da shi ba?

Barni naci wlh gida babu makota sai ɗai-ɗai tun tana suyarsa nake haɗiye yawu, kuma na goge inda ya taɓa abincin kafin na soma ci.

Ƙuda dai gurin kwaɗayi yake mutuwa, watarana sai in kashe kanki abanza saboda kwaɗayi. Sai wani cakal cakal kike yi gwanin ƙazanta.

Cewar Hanan tana balla mata harara, Jamila ta haÉ—iye wanda ta tauna ta tsaya galala tana kallonsu tare da runanin ko dai maganin mutuwa suka sakawa Sameeha a abinci, nan take cikinta ya karta ta ce cikin tsoro.

Ko guba kuka sa na saka mata a cikin abincin?

In shine ma ai kin riga kinci sai dai muce Allah ya jikanki.

Cewar Binafa data ɗaure fuska, a zabure Jamila ta miƙe tana salati babu inda jikinta baya rawa, ga sauran naman a hannunta ta kasa ci balle ta yar.

Ke karki ɓata mana aiki ki yi mana shuru da wasa muke yi, taya zamu baki guba ki saka mata kuma mu zauna zaman jiranta ai tuni zamu cikawa bujenmu iska.

Cewar Hanan, Jamila ta haɗiye miyau kwad tana sauke ajiyar zuciya sai kuma duk taji naman ya fice mata a rai, haka ta haƙura ta saka shi cikin ledan data zuba taliya ta ɗaure, ta shiga bayinta ta wanke hannu, sosai ta basu dariya haka suka shigayn dariyar ciki ciki dan kar a jisu. Lokacin da suka ji motsin Sameeha ta fito daga kitchen sai suka zabura suka miƙe tare da shigewa bayi dan kar ta leƙo ta gansu, sai da suka tabbatar ta shiga ɗaki kafin sula fito lokacin sun samu Jamila ta fita da plate da kuma ledan abincin, suka zauna a gado suna kallon juna.

Hanan anya zan iya jurewa sai asuba zamu far mata, gaskiya a matse nake.

A'a Binafa mu dai bari zuwa lokacin dan kar mu ɓata shirinmu dan kinsan barci mai nauyi zai iya ɗaukemu bayan kura ta lafa, gwara mu yi barci yanzu sai mu saka alerm da zai tashe mu da asubahi.

Bazan iya ba Hanan, ko kaɗan zanje na ragewa kaina zafi in yaso sai na ƙara tara na asubahin.

Hmmmm Hana tace sai ga Jamila ta dawo cikin É—akin tana cewa.

Na fita ta ƙofar kitchen naje babban bolan gidan na saka abincin dan kar ta gani a boln kitchen da safe ta tuhumeni.

Kinyi kyan kai 'yan mata, ki bari zuwa anjima saiki dafa mana indomie.

Ina tsoron karta gane na É—iba kinsanta akwai bin diddigi.

Idan kinga ta damu da hakan ba, dan matsalar dake gabanta yafi indomie. In kuma zaki kwana da yunwa ba damuwa mu zamu iya fita mu samu abinda zamu ci.

Cewar Binafa, Jamila bata ce komai ba ta koma ta zauna duk abin duniya ya isheta, duk a takure take da zaman ɗakin saboda su, sannan cikin tsananin fargaba take akan kar Allah yasa asirinsu ya tonu, duk ta ƙosa su gama su tafi duk da bata san asalin me zasu aikata ba a gidan.

Wajen ƙarfe goma saura, Binafa ta fara hamma sai ta miƙe tana cewa.

Nasan zuwa yanzu maganinmu ya fara aikinsa bari in dubata in dawo, zuwa anjima sai mu shiga kitchen ɗin muga me zamu dafa dan na kula wannan baƙin tsoro ne da ita gwara ta kwana da yunwa akan ta dafa mana indomie.

Muje tare dan ban yarda da wasa tare ci bambam ba. Nasan ki sarai wlh kamar yunwan cikina.

Hanan tace haka sai suka fito falo shuru ba kowa ga hasken fitilan ba a rage ba balle a kashe, suka dunfari É—akin Sameeha babu fargaba ko tsoro dan sun san hakkarsu ta cimma ruwa tunda taci maganin.

***
Sameeha.

Lokacin data hau kan gado sosai take jin barci har ya fara kamata, amma bayan mintuna sai ta farka firgigit kamar an tsikareta data, buɗe ido sai taga ɗakin na juya mata, tayi yunƙuri zata tashi amma ta kasa saboda wani nauyi taji jikinta yayi mata, ga kuma kanta da take ji yana juyawa tamkar an sauya ta, dan gani take kamar lilo ake da ita, haka ta dinga juyi a gado shima sai da tayi da gaske take iya mirginawa. A cikin wannan yanayin su Binafa suka shigo ɗakin, Sameeha tana ganinsu taji ƙirjinta ya buga tare da tunanin meya kawo su gidanta a wannan lokacin, sai ta soma nazari ko mafarki take yi dan sosai ta gane fuskarsu tunda ɗakin da haske sosai. Ganin sun dunfaro ta yasa ta ware idonta don ta tabbatar da ba mafarki bane.

Su waye kuuu? Me ya kawo ku?

Ta faɗa cikin muryan maye, ganin sun hau kan gadon yasa tayi saurin yunƙurawa amma ta kasa tashi, hakan yayi matuƙar bata mamaki ganin duk jikinta ya saki lokaci guda, nan take ta fara zargin akwai abinda taci ko tasha wanda ya haifar mata da haka, tunawa da ta barwa Jamila girki yasa zarginta ya faɗa akan ta saka mata wani abu a abinci wanda hakan ya hasko mata an shirya mata gadar zare, kaico ta fara yi da dana sanin sakaci da tayi na sakewa da Jamila lokaci guda, tunda tasan su Hauwa ba son zamanta a gidan suke yi ba. Binafa ce ta fara cire hijab ɗinta ta yasar a ƙasa, itama Hanan haka tayi jikin Sameeha ya fara rawa domin ta gane inda suka dosa, idan sun kai hannu jikinta sai ta ɗago hannu ta ture tana ƙoƙarin kai musu duka sosai suka yi mamakin jarumtarta sai dai sun bayar jininta yana da ƙarfi, Hanan ta kaiwa hannunta duka.

Wlh ko kinƙi ko kinso sai mun huta dake. Shegiya sai shegen kyan jiki. Binafa ko kinji yadda fatarta ke da silɓi.

Hmmm cikin hutu take ba dole komai yaji ba.

Ta bata amsa hakan yasa suka fara kokarin cire mata rigar barcin amma Sameeha ta hana su ta shiga kokawa da su duk da tana a kwance.

Aminu.

Motarsu ta tsaya a bakin gate ya sauko tare da briefcase É—insa ya juya yana cewa driver.

Ka tafi da motar ka nimo mana mai cikin daren nan koda na black market ne, dole ya kasance mun samu full tank nasan kuɗin dana baka zai isheka, saboda da ƙarfe bakwai nake so mubar garin nan. Da anyi asuba ka zo.

To yace masa sai ya wuce shi kuma Aminu ya buga gate mai gadi da ya fara gyangyaÉ—i a benci ya tashi firgigit ya zo jikin gate É—in bai buÉ—e ba ya shiga tambayar waye, Aminu yace.

Ka buÉ—e mai gidan ne.
Chapter 26 · 0% Book details