← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 98

Sashe 81

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai Nafeesa faɗan da muka yi dake a falon Amuni ya lalata komai domin yana ciki yaji komai hakan ya jawo mini duka a gunsa da safe kuma ya ɗaukeni har gidansu Sameeha ya tona mini asiri ya kuma sakeni saki biyu a gabansu, yanzu haka ina kano gurin ƙanwar babana Saleema, kowa ya juya mini baya.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, amma banji daɗin faruwar haka ba kiyi haƙuri ki yafe min domin nice naja komai.

Ai dole ki bani haƙuri bayan kin cutar dani, to bari in faɗa mini ni ce nan na turawa yayanki saƙon nan a matsayin Hamisu ne domin tunda na rasa Aminu kema in tona miki asiri da Binafa.

Najwa dama kece kika tona mini asiri? Yanzu na cancanci kiyi mini haka duk iya halaccin dana yi miki.

Wlh Nafeesa fiye da haka zanyi miki domin kin rabani da farin ciki na.

Hmmmm to ai ni gwara ma da kika tona mini asiri domin kuwa gaba takaini yadda kike fatan na wulaƙanta ban yi ba domin Allah ya rufa mini asiri kuma na karɓi ƙaddarata, wannan maganar da kika sanar dani yasa na ƙara fahimtar ke butulu ce kuma dole in raba hanya dake saboda ke ba mutumiyar arziki ba ce, ni na karɓi ƙaddarata kuma ina niman Allah ya yafe mini sannan har gidansu Sameeha zanje in nima yafiyarsu dan ina so nayi rayuwa da mijina cikin salama, daga yau bani ba ke Najwa domin zuciyarki ba tada kyau.

Tana gama faɗar haka ta kashe wayar, na take tayi blocking number ɗin Najwa dan sosai take jin ba zata ƙara barin wata alaƙa ta shiga tsakaninsu ba saboda Najwa ba abokiyar arziki bace. Najwa kuwa kukan baƙin ciki ta fashe dashi da jin takaicin yadda Nafeesa ta samu rufin asiri cikin ƙanƙanin lokaci, taso ta wulaƙanta fiye da ita sai kuma hakan ya zama silar rufuwar nata asirin, dole itama ta yi aure cikin ƙanƙanin lokaci ko zata samu sassauci daga halin da take ciki.

Binafa...
[7/7, 13:04] Buhainat😁: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*

50

Binafa.

Saida suka ɗauki sati biyu a cel ba tare da an turasu kotu ba saboda tsaikon da aka samu daga gurin 'yan sanda na haɗa bayanai, sosai Binafa da Hanan suka shiga cikin tashin hankali ganin yadda aka mayar dasu kamar bayi an tsaresu ba duka ba zagi amma kuma su sauro suna ta sukuwa a jikinsu ga yunwa da ƙishir ruwa, abincin da ake basu sai kace 'yan bursina, da farko ƙin ci suka yi amma ganin yunwa zata yi musu lahani yasa suka fara ci, wannan wahalar da suke ciki yasa Binafa sarewa akan gwara ta sanar da iyayenta a kawo mata ɗauki duk da ta san zata fuskanci matsala dasu amma gwara a rabata da wannan wajen in yaso ko me zasu yi mata to suyi, ita dai ta bar cikin cel ɗin a rufe maganar ko dan kare mutuncin gidansu Iyayenta ma zasu so haka, lokacin da wani ɗan sanda ya kawo musu abincin dare a sannan ne take yi masa bayanin a bata wayarta zata kira 'yan uwanta susan da maganar, ɗan sanda yace su da suka ce ba su da kowa ai kawai su cigaba da zama har lokacin da za aje kotu, Binafa ta nima bashi cin hanci akan in sun fita zata biyashi da tsoka, yace shi ba irin waɗannan 'yan sandan bane da suke ɓarna a cikin aikinsu, dan haka ta kama kanta tun kafin ta ƙarawa kanta laifi kuma wayarta ma bata hannunsu bai san a inda take ba, yana gama faɗar haka ya wuce, jikinsu ne ya ƙara yin sanyi da labarin dan duk yadda suka ɗauka yafi ƙarfin lissafinsu, sosai hankalinsu ya ƙara tashi da damuwar makomar halin da suke ciki dan ba zasu jure zaman gurinba in ba haka ba wani ciwo sai ya shige su. Mako guda da auren Nafeesa a ranar monday aka tafi dasu babban offishin alkali dake nan high court, an gabatar da su tare da waɗanda suke yi ƙara zuwa office ɗin Alkali domin ko za a samu maslaha a daidaita lamarin, amma ana karanto wa Alkali laifinsu yace dole sai an je kotu saboda laifinsu ba ƙarama bace domin ayi musu hukuncin da zai zama izina ga masu irin halinsu dan haka ya tsaida ranar Alhamis zaman kotu, sai ya sallame su aka mayar dasu cel aka cigaba da tsaresu, a wannan lokacin kuka suka fara da dana sanin taɓa yarinyar mutane domin tabbas sune suka jawota jikinsu da kashe mata kuɗi har ta basu haɗin kai suka ɗaurata a hanyar, dana sani ne ya fara rufe su Binafa ta kalli Hanan cikin zubda hawaye.

Ina tsoron duniya tasan me muke aikatawa ban san ya 'yan uwana zasu É—auka ba, ni gwara tun yanzu na sanar dasu komai kafin a kaimu kotu.

Hmmmm ai aikin gama ya gama dan ɓacin suna kam mun gama kirawa kanmu, bawai tsoron dan an kaimu kotu nake ba, Allah yasa kar a kaimu gidan yari dan wlh bazan jurewa wahalar ba.

To sunƙi bamu ma haɗin kai balle na kira gida a kawo mana ɗauki, nasan dadyna zaiyi komai dan a rufe maganar, sai ma yanzu ma nake ganin wautata da na nima ɓoye maganar duk da a da ina hangen zan iya magance matsalar da kaina, ashe kuɗi basu isa su kwacemu ba, muna cikin babbar matsala fa Hanan.

Binafa ta ƙarasa maganar tana matso hawaye cike da tsantsar damuwa, haka suka dinga mayar da magana wanda tarin dana sanin da suke ciki suke fitarwa.

Kotu.

Kamar yadda Alkali ya sanar ranar Alhamis aka shiga kotu, wanda su Binafa sunyi matuƙar mamakin ganin mutanen da suka taru, ciki har yayanta Hassan da Yaya Taju dama sauran yayyinta da kuma wasu a family ɗinsu maza, wanda take tunanin ya aka yi suka san tana gurin, kuma komai da yake faruwa Hassan yana da masaniya domin DPO yana sanar dashi saboda sun amsa bumber ɗin juna, tashin hankali gobarar gemu! Domin kuwa Binafa samun kanta tayi da jin tsoro da fargaban tonuwar asirinsu a bainan Nasi, hawaye ya soma zarya a kuncinta ta sunne kai jikinta ya ɗauki ɗumi tare da kaɗawa tamkar zazzaɓi take ji, Hanan kuwa da yake babu nata a gurin bata damu ba sai damuwar hukuncin da za a yanke musu take yi dan bata fatan a yanke musu zaman gidan kaso bata shiryawa hakan ba, kowanne dai da abinda ya dameta. Sai da aka fara gabatar da wani ƙara na masu bashi daga bisani aka gabatar da ƙaran su Binafa, haka aka tisa keyarsu aka sanya a cikin wajen amsa tambaya, nan Hassan ya fara ɗauka a wayarsa a ɓoye dan yayi alƙawarin nunawa iyayensu wannan abu tunda bai sanar dasu ba sai iya 'yan uwansa maza da wasu maza cousin ɗinsu, nan aka gabatar da Baristan masu ƙara ya miƙe yayi bayani tare da gabatar da kansa, Alkali ya buƙaci ganin baristan su Binafa, aka sanar da ba su da shi nan take ya wakilta wani daga cikin lauyoyin gomnati akan ya tsaya musu, cikin ƙanƙanin lokaci aka fara gudanar da komai. Aka ce ranar wanka ba a ɓoyon cibi su Binafa basu wahalar da Shari'a ba sun amsa laifinsu, hakan yasa alkhairi ya yanke musu hukunci kamar haka.

An yanke musu tarar kuɗi million huɗu da rabi sannan da zaman gidan yarin na shekara biyu tare da aiki mai tsanani, idan kuma basu bayar da kuɗin tara ba da za a bawa yarinyar da suka cutar, to zasu yi zaman kaso shekara shida shida. (Wannan hukuncin daga alƙalamin marubuciya ce Rahma, ban tsaya na yi bincike kan case irin nasu ba na yanke hukunci ne domin gajarce ɓata lokaci, da kuma sauƙaƙa ƙarshen labarin.)

Kuka suka fashe dashi domin ba suyi zaton wannan hukuncin ba, su bayar da taran kuɗin bai dame su sai zaman gidan yari ne ya ɗaga musu hankali sosai, nan Alkali ya ce za a iya ɗaukaka ƙara tare da sallamar case ɗin, haka aka tasa ƙeyar su Binafa aka fito dasu farfajiyar kotu, duk da Hassan yayi ƙoƙari sosai dan kar a bawa 'yan gidan tv da radio damar shigowa, sai dai duk da haka ansamu wasu sun ɗauki hotunan su Binafa a wayarsu, Binafa ta tsaya gaban 'yan uwanta ta tsuguna tana rusa kuka da cewar su ceceta su ɗaukaka ƙara a samar musu lauyan da zai karesu su fita daga wannan case ɗin, tasan suna da kuɗin da zasu yi mata haka, kuma in dady ya sani zaiyi wani abu su taimaka su sanar dashi, Hassan ne yace cikin ɓacin rai.

Wlh ko dady ya sani to ni da kaina zan hana ya taimake ki Binafa, domin ina so jikinki ya gaya miki ki gane Allah ɗaya ne, wataƙila zaki dawo cikin hankalinki ki daina yin ƙazantacciyar rayuwar da kika zaɓarwa kanki, ina mai tabbatar miki da nasan kina gurin 'yan sanda da komai da ke faruwa, ban sanar da su Dady ba saboda azo wannan gaɓar da zaki muzanta asirinki ya tonu kowa yasan wacece ke, dan haka kisa a ranki zaman gidan yari wajibi ne a gareki babu taimakon da zaki samu a gunmu sama da abinci da ɗan abin buƙata a gidan, pyan sanda ku wuce da ita.

Dan Allah yaya dan son Manzon Allah s.a.w kayi mini rai ka fitar dani a wannan kuncin, wlh tallahi nayi maka alƙawarin ba zan sake aikata komai ba na tuba na tuba na tuba.

Ta ƙare cikin wani irin gunjin kuka dan ko miƙewa da kyau ta kasa. Hassan ya ce cikin dakiya.

Binafa baki tuba ba tukuna sai kin ganki a gidan yari kina bin layin abinci a nan ne zaki tabbatar da yadda ake tuba. Abokai mu wuce kar mu ɓata lokacinmu a nan.
Chapter 81 · 0% Book details