← Book details Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 98

Sashe 97

Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai na bada adireshin da za a je a kira su. Anan unguwar dosa nake layin jatau babban gida, duk wanda aka tambaya babban gida zai kaiku, sai ya sanar da duk wanda ya samu a gidan yace Hauwa ce tayi accident.

Nurse ɗin tace to kana ta wuce suka aika wani mai sharar gurin da kufin mota ya tafi, kuma anyi sa'a duk su Alhasan suna gida dan a ƙofar gidan mutumin ya same su nan ya isar da sakon Hauwa, cike da damuwa suka shirya tafiya sai Kamalu ya fito da motarsa suka ɗauki mutumin zuwa asibiti. A takaice sune suka ɗauko Hauwa zuwa gidanta suka kira mai ɗauri yayi mata ɗaurin gida sannan suka biya kuɗin komai, Hauwa banda kukan azaba da baƙin ciki ba abinda take yi wato rijiya da bada ruwa amma guga ta hana, ƙiri ƙiri damar da ta samu kenan da zata nuna wa Aminu kurensa amma gashi ta nakasa wanda ta tabbatar da sai tayi zaman jinyar kusan watanni a zaune, hawaye ya cigaba da bin kuncinta tana jin baƙin ciki mai tsanani. Koda ta aika yaronta banki kan kuɗinta sun tadda an yashe dubu hamain ɗin, Hauwa ba ƙaramin takaici ta shiga ba haka dole ta cigaba da jinya Allah yasa suna da Abinci, Baba Saude ita su Alhasan suka yiwa magana ta zauna jinyar Hauwa, Adama kuwa kusan sai dai tazo ta dubu ta ta koma, dan sosai Isyaku ya nuna yanzu ne ya samu jin daɗin aure, kuma ba zai saketa ba aurensu tamkar na zobe ne, Alhasan sune suka cigaba da taimaka musu da kuɗin cefane, da suka sanar da Aminu ya tura musu kuɗi mai coka akan su kula da Hauwa sosai musamman cin nama domin a samu ƙafar ta warke da wuri, duk da sun sanar da Hauwa ba wani farin ciki tayi ba dan a sanadinsa ne ta samu kanta a haka, dan gabaɗaya shi ta ɗaurawa alhakin hakan.

*****

NAJWA.

Tunda ranar da ta yiwa mama rashin kunya Mujaheed ya fita sabgarta dan sati gudan nan sai da yayi mata na amarci, amma fa ko magana basa yi, ita Najwa ta dau zafi shi kuma yana son ya nuna mata bata isa ba, batun abinci kuwa sai dai ta riƙa dafawa kanta a ɗaki dan Junaid ya siya mata gas ɗin, cefane kuma sai dai ta yiwa kanta da kuɗinta, sai ta sa hijab ta fita ta siya duk abinda take so ba tare data tambaye shi izini ba mama da Safara'u kuwa nasu ido dan gabaɗaya ba mai shiga harkarta, a hakane ta samu ta turawa Anty Saleema kuɗi dubu arba'in da biyar dan bata samu tura hamsin ɗin ba saboda kashe kuɗin da ta yi a satin, dan abincin mai kyau fa take ci har da kifi da nama duk ta saya, data sanar da Saleema ta aika mata kuɗi tace ta gansu amma fa kuɗinta data kwashe mata ta gudu dasu to sune ta tura mata harda riba kuma babu taimakon da zata iya mata taa san yadda zata kwaci kanta a gidan mijin dan ba ruwanta, Najwa zata yi magana ta kashe wayarta sosai lamarin ya daki zuciyarta dan bata taɓa kayo zata yaudareta haka ba, har kukan baƙin cikin abin sai da tayi ga kuma damuwar Mujaheed ya daina kwana a ɗakinta, dan tunda Safara'u ta amsa girki bai sake waiwayenta ba, wani sa'ilin sai dai taji muryarsa a tsakar gida dan ko leƙowa ya dubata baya yi, duk da shima dauriya yake yi amma dole ya nuna mata shi na mijine, kuma umarnin mama yake bi dan ita ce ta tsara masa haka.

A hankali Najwa ta kwashi wata a gudan da sati kuma a wannan ƙuncin kaɗaici, duk yadda ta ɗauka lamarin zai yi sauƙi amma ƙara gaba yake yi, ga kuɗin hannunta sun ƙare ya zamana sai dai ta dafa farar shinkafa taci da mai da yaji, data kira yaya Junaid ta sanar masa cewa yayi tayi haƙuri da abinda mijinta ke da shi, dan ba kai tsaye ta fito ta faɗa masa zaman doya da manjan da suke yi ba, sai ya ce zai tura mata katin ɗari biyar ta saka data, daga haka ya kashe wayar Najwa taji hawaye ya cika mata ido, jin kuɗin ya shigo yasa ta kira Inna koda ta ɗauka suka gaisa sai ta fashe da kuka.

Inna ba zan iya zaman gidan nan ba dan Allah koda Mujaheed ya sake ni ki sa baki baba ya barni na zauna a gida.

Wlh Najwa karki fara dan hatta ni ba zaki samu sauƙi a guri na ba, haƙuri za kiyi da duk yadda kika samu kanki. Wai ma meya faru da kike niman ɗaga mini hankali.

Inna baya mini magana ya daina kwana a É—akina tun sati É—aya dana yi a gidan, rabon dana saka shi a ido har na manta, sun mayar dani saniyar ware hatta mahaifiyarsa ba mai shiga hurumina.

Haba Najwa da abinda kika aika, na tabbatar ba zasu yi miki haka kurum ba, idan ma laifi kika yi musu ki basu haƙuri ki zauna a ɗakinki Najwa, yanzu fisabilillah ke kullun burinki ki baƙanta mana rai, tunda muka aured dake bamu samu kwanciyar hankali ba kullun maganar mu da fatanmu ki zauna a gidanki.

Inna girki suka ce dole sai mun haÉ—a na gidan, sannan har da shara da wanke bayin waje bayan ni ina da komai a É—aki, dan nace ban yarda ba shine suka yi mini haka.

Hmmmm Najwa kenan, meye aibun ayyukan bayan duk kin saba yinsu a gida, in dai wannan ne hakanan zaki yi haƙuri kiyi yadda suke so a zauna lafiya, na tabbatar idan kinyi haƙuri watarana zai zama tarihi.

Najwa kasa magana tayi sai kuka mai sauti, Inna data kasa jure kukanta saita kashe wayar cike da tsantsar damuwa, itama sam bata ji daɗin hukuncin da suka yanke mata ba ganin ita akwai komai a ɗakinta, amma tasan in dai da Mahaifiyarsa suke zaune dole ne ta bijiro da abinda yafi haka ma, dan iyayen miji wasu akwai iko da nuna isa wanda in da akan 'ya'yansu ne mata ba zasu zo uwar mijinsu ta takura su haka ba, ƙiri ƙiri suke nuna bambanci da nasu 'ya'yan, tamkar su matan da aka auro musu kamar ba 'ya'yan wasu bane, taja guntun tsaki tana cewa.

Allah ya kyauta ya rabamu da son zuciya irin na wasu iyayen mijin.

Sai ta miƙe ta cigaba da aikinta amma damuwar Najwa yana maƙale a zuciyarta. Najwa kuwa kwanciya tayi a doguwar kujera tana matsar kwalla daha haka kuma sai zazzaɓi ya rufeta dama tun safe data tashi tq ji jikinta ba daɗi, sauran shinkafar jiya ta ɗumama ta karya dashi wanda taji kamar zuciyarta tana tashi bata iya cinyewa ba tasha ruwan lipton ta aje sauran. Tana nan kwance har zuwa la'asar wanda barci ne ma ya ɗauketa, kamar a mafarki taji wani abu ya tokare mata numfashi da sauri ta tashi sai kuma ta fara kakarin amai ta zura hannunta a baki sai aman ya biyo baya, nan ta dinga yinsa kamar zata amayar da hanjin cikinta. Mama dake zaune a tsakar gida tunda taji aman ta miƙe ta leƙa ɗakin Safara'u.

Ke zoki duba yarinyar nan kamar amai fa take yi.

Wa? wai Najwa? Ina jin ta, wlh bazan duba ba Mama tunda ba tada mutunci.

Amma ai rashin lafiya ya kori komai.

Ni fa bazan dubata ba kar ma naje ta zageni kinsan ta ba mutunci ne da ita ba.

Mama bata ce komai ba ta juya ta koma mazauninta sai ta É—auki wayarta ta duba numbern Mujaheed ta kira shi, koda ya É—auka ta sanar da shi aman da Najwa take yi, tace in yana kusa yazo ya dubata dan bata so ta shiga tayi mata rashin kunya, Mujaheed ji yayi kamar ta saka shi a aljanna dan dama dauriya kawai yake yi daya share Najwa, dan sosai yake jin sonta, ga kuma zumanta daya lasa sau É—aya bai kuma É—anÉ—ana wa ba, kuma a yadda yaji Najwa tafi Safara'u sosai dan É—anÉ—anonta daban ne, dan haka cikin sauri ya kashe wayar mama ya shiga cikin gida ya sanarwa Hajiya matarsa ba lafiya sai ta sallame shi ya wuce.

Mujaheed yana shigowa gidan É—akin ya nufa dan ko tsayawa yayi magana da mama bai yi ba, ya samu tana kwashe aman da tsumman É—ankwalinta, Najwa duk da ta san da shigowarsa amma ta basar ta cigaba da abinda take yi har ta gama ta shiga bayi ta wanke hannu ta fito suka haÉ—a ido, sai kawai ta É—aure fuska ta samu guri ta zauna, yadda ta É—an rame tayi haske yasa Mujaheed yaji tausayinta ya taso ya zauna a inda take ya kamo hannunta.

Najwa meke damunki gabaÉ—aya kin sauya?

Ban sani ba, dan Allah ka fita daga ɗakin nan bana son ganinka tunda na zama abin wulaƙanci daga ina nimawa kaina 'yanci.

Kiyi haƙuri amma kema kin san baki kyauta ba mahaifiyata fa kika yi wa rashin kunya, ke in aka yiwa taki haka zaki ji daɗi. Yanzu tashi za ki muje asibiti dan na kula ba kida lafiya.

Babu ruwan ka da rashin lafiyata, dama jikina kake so tunda ka samu biyan buƙata na zama abin wulaƙanci.

Najwaa ki daina faɗar haka dan kaza tana tsakurar 'ya'yanta badan bata son su bane, nayi miki hakane domin ki gane baki kyauta ba. Kiyi haƙuri .
Chapter 97 · 0% Book details