Sashe 5
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
To yaya dama um..
Ta faÉ—a tare da yin shuru tana susa kai, Zaidu ya kura mata ido yana 'yar murmushi dan ya san wani abin zata tambaye shi, yace cikin kulawa.
FaÉ—i kanki tsaye karki yi shakka ni É—an uwanki ne mai yi miki duk kan hidimarki.
Dama yau inna tuwo ta mana kuma wlh kasan ni da tuwo bama shiri, shine nake so ka siya mini indomie.
Ai yau kin wuce cin indomie dan ajihuna yana da nauyi, yanzu ki shiga gida zan je na siyo miki abu inna dawo zan kira ki fito ki amsa.
To tace masa tana yi masa godiya, haka ya kunna mashin É—insa roba roba ya wuce ita kuma ta shiga gida tana kwalawa inna kira har sai da ta dangana da É—akin inna ta buÉ—e labule ta ganta zaune a dadduma tana jan carbi, shiga tayi ta zauna har sai da inna ta idar kafin ta kalleta tana cewa.
Wai ke Najwa yaushe zaki yi hankali?
Randa kika aurar dani Inna.
Ta bata amsa tana 'yar dariya, daƙuwa inna tayi mata tana cewa.
Allah ya shiryaki auta, to lafiya kike mini ɗan kira kamar kin haɗiyi ƙarfe.
Inna anty Sameeha ta dawo yau yanzu Yaya Zaidu ke faÉ—a mini.
To ai ke ce baki sani ba amma ni tun É—azun nayi waya da ummansu ta faÉ—a mini.
Laaa shine baki faÉ—a mini ba.
To da ban faÉ—a ba ai gashi kin sani yanzu, kuma É—azun kina islamiyya koda kika dawo na manta
To inna zani gobe In Allah ya kaimu naga gida dan wlh ina son naga daular da Anty Sameeha ke ciki.
Idan kin ga daular me zai kareki dashi? kinga Najwa! kinga ki cire rayuwarki da shegen son kuÉ—i.
Inna kuɗi shine rayuwa ki barni na so su, kuma so kike nayi rayuwa a gida irin wannan, wlh ina fatan na yi auren jin daɗi ba ƙarma ƙarma ba, wani sa'ilin ji nake dama ba a gidan nan aka haifeni ba da a gidan wani hamshaƙi ana halittoni, wlh da duk ba ruwana da cin miyar kuka balle wani koko.
Auzubillahi! Najwa kina da hankali kuwa? da iliminki kike wannan zancen, to ki tuba wa Allah dan maganarki ta kauce hanya. Ni da baki samu ilimin addini ba Allah kaɗai yasan irin rayuwar da zaki taso a ciki. Sannan da kike maganar baki son ƙarma ƙarma ashe yaudarar Zaidu kike yi da kika ce shi zaki aure shi.
Kai inna nifa da wasa duk nake maganata, kina ta yi mini dogon sharhi sannan...
Bata ƙarasa maganarta ba kira ya shigo taga Zaidu ne da sauri ta miƙe tana amsa kiran ta fice, da kallo inna ta bita tana yi mata addu'ar shiriya dan lamarin Najwa yana bata mamaki akan dogon buri da son kuɗi, gata da ilimin addini sosai amma akwai shagala.
Ummu Sultan da Samha ce.
[7/7, 13:04] BuhainatðŸ˜: *ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 4.
Najwa tana fita Zaidu ya mika mata fararen leda guda biyu ta amsa tana washe baki da godiya, suka yi sallama ta shiga gida ta zube ledan gaban inna ta zauna tana dubawa, ledar farko kayan tea ne a ciki sai leda na biyu kuma gasasshiyar kaza ce dankwaleliya da kuma cips da kwai da miyar albarka a cikin wani foil paper daban, Najwa taja numfashi tana sauke shi a hanlaki tare da haÉ—iye miyau.
Allah ya shiryeki Najwa ya rabaki da cutar kwaɗayi, dan na kula shine kawai yake damunki, na tabbatar ke ce kika saka shi wannan siyyar da ba shiri saboda nayi tuwo maƙiyinki.
Kai innata koda na roƙeshi ɗan uwana ne fa, kuma matsayin wa yake a guna ko ba soyayya akwai ƙauna ta jini.
Hmmm ni kwashe kayanki ki tafi da shi É—akinki kafin babanku ya shigo, kin san dai baya son irin wannan abin.
Ai da sauri ta miƙe ta kwashe ledanta ta fice dan ta san babansu bayi da wasa, inna ta bita da cewa.
Saura ki cinye baki aje min ba.
Dariya Najwa tayi ta shiga ɗakinta tana gyara zama ta soma cin kazar nan kamar mayunwaciyar zaki. Najwa kenan ga sani ga shagala take ta kenan, yarinya ce mai natsuwa da iya shiga ta mutunci, dan bata saka gyale hijab ne har kasa da safa, nikaf ne sai in zata islamiya take sakawa, shekarar da ta wuce ta kammala secondry bata cigaba ba dan babansu bayi da ƙarfi kuma ma irin mutanen nan ne masu ra'ayi bai yarda tayi boko da ta wuce secondary ba, mazan ne dai suke da garantin cigaba sai dai gabaɗayansu ma sunƙi mayar da hankali ga karatun boko, babbansu Junaid bakaniken mota ne sai mai bi masa Abdullahi ustaz ne yana koyarwa a islmaiya, sai kuma na uku Sadiq tela ne sannan Najwa da yanzu take makarantar haddar alqur'ani tun bayan yin saukarta da shekara biyu da ya wuce, ta haɗa izi ashirin da biyar. Ance mutum tara yake mai cika goma ba to gaskiya itama ta samu naƙasu a fannin yawan buri, tana mugun son rayuwar masu kuɗi da wayewarsu, duk da tana da tarbiyya sosai amma bai hana ta nuna maitar son kuɗinta a fili ba, idan aka ce hidima ta masu kuɗi ne aka gayyaceta to ba karamin bashi muhimmamci take yi ba, shiyasa ko a makaranta kawayenta yaran masu kuɗi ne, sai ta tabbatar da akwai kumbar susa kafin take bada kofar ayi abota da ita, kuma tun tana karama da wannan aƙidar ta taso wataƙila dan ko su talakawa ne yasa take kwaɗayin haka, saboda duk danginsu babu masu kuɗi sai dai masu ɗan rufin asirin Allah, yanzu ne dai da Sameeha ta fita zakka a cikinsu ta zama musu zakaran gwajin dafi, shiyasa Najwa take mugun sonta har hakan yasa ta yanke amincewa da auren Zaidu saboda hakan ne kaɗai zai ƙara mata kusanci da ita kuma ta riƙa shiga cikin masu kuɗi, dan a ganinta Sameeha tana da kawaye masu kuɗi sosai, sannan ta samu gidan kashe kwaɗayinta tunda ta san basa rabo da kaji da kayan daɗi, addu'arta Allah yasa Sameeha tana da sakin fuska da son mutane duk da tasan halinta a da ba tada matsala, amma kila yanzu kuɗi ya sauyata dan wasu in sun samu rana basu iya shanya ba.
***
Washe gari da wuri Najwa ta shirya ta tafi gidansu Zaidu, ta samu har sun gama shiri zasu tafi Zaidu ne ma ya tsayar dasu akan su jirata ta ƙaraso, Najwa ta gaishe su cikin girmanawa kana Sameeha ta ce su wuce dan akwai aiki a gabansu, suka fito Zaidu ya tare sumu napep biyu, Sameeha da yaranta sai Najwa da Ikram a dayan napep ɗin tare da kayanta dan zata kwana biyu a can har sai sun gama kimtsa gidan.
Suna isa bakin gate suka sauka dama Zaidu ya sallami masu napep tun kan su taho, Abi ya buga gate mai gadi ya buɗe yana ganinsu ya shiga yiwa Sameeha sannu da zuwa ya buɗe musu ƙofa suka shiga, tun daga farfajiyar gidan Najwa take karewa gidan kallo tana faɗin masha Allah tana maimaitawa, har suka isa ƙofar shiga falo Sameeha tayi amfani da key ta buɗe musu ganin ba motar Aminu tasan baya nan, suna shiga Najwa ta zube a cushing tana sauke numfashi da wani irin tsantsar murna wanda ya bayyana a fuskarta, saboda yadda falon ya tsaru yayi matular burgeta da hango kanta dama itace ce mamallakin gidan, sam ta kasa danne farin cikin tana cewa.
Alhamdulillah Masha Allah La Kuwwata Illah Billah, Anty Sameeha kin dace da gidan duniya saura na lahira, wlh gidanki tamkar irin gidajen da muke gani a cikin fina-finai, ya tafi da imanina Allah ya sakamu a danshinki, ni kam kamar in dawo nan gabaÉ—aya da zama dan wlh ba karamin kankaro mini mutunci zai yi in kawayena suka ganni a nan.
To Najwa ai ga É—aki nan sai ki kwaso kaya ki dawo mu cigaba da zama.
Ai wlh Baba bazai barni bane kawai amma da sai na dawo, ko da yake ko hutu na riƙa zuwa ina buga hotunan da zan riƙa posting a status, ko ba komai muma muna da gida mai kyau.
Allah ya kyauta miki Najwa ke dai har yanzu ba zaki bar wannan shegen ƙarya da buri ba.
Cewar Ikram tana balla mata hararar wasa, Najwa ta miƙe ta yi tattaki ta isa inda Ikram ke tsaye ta dafa kafaɗarta tana cewa.
Ke me za a fasa ai ina nan akan bakana, dole in yi kwaÉ—ayin kuÉ—i domin cikin talauci na taso, da ace na gaji arziki ba zanta magana irin haka ba, ki barni na faÉ—a koda a iya baki ne na dai furta, kuma kuÉ—i abin so ne ba wanda baya son jin daÉ—i.
Naki dai yayi yawa wlh, yanzu na tabbatar da kin ci sunanki wato ga sani ga shagala.
FaÉ—i ki kara 'yar uwa.
Kun ga, ku bar wannan taƙaddamar ku zo ku fara aiki bana son Abban Amra ya dawo bamu ci karfinsa ba, Ikram ina ga ke zaki shiga kitchen ne ki ɗaura mana shinkafa da miya ki gyara kaza biyu kiyi mana peper chicken.
Cewar Sameeha tana fitowa daga É—akinta data shiga aje jaka, Najwa tayi wani shewa tana rawa da wakar.
Ewe gidan masu kuÉ—i gidan daÉ—i, za muci kaza zamu kaza.
Allahu yahadiki Najwa.