Sashe 46
Abin Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma ta faɗa tana dariya itama dariya tayi suka yi bisimillah suka soma ci, sallamar Ikram suka ji ta shigo gidan ta dawo daga makaranta, da sauri ta ƙaraso ta cire hijab ta aje a tabarma tana yi musu sannu da gida sai ta wuce kitchen ta ɗauko cokali ta zo da sauri ta zauna tana cewa.
Wlh jikina har rawa yake yi dan yunwa, bari na taya ku ci in mun cinye ma ƙara.
Laifin ki ne baki tsayawa ki karya da kyau, ki dai yi a hankali kar ulcer ta kamaki.
Cewar umma, Ikram dai tattara hankalinta tayi tana ci dan ba tada lokacin mayar da magana. Bayan sun kammala sai Ikram ta kwashe kayan ta mayar kitchen ta shiga É—aki ta cire uniform ta saka riga da siket na atamfa ta fito tana É—aura É—ankwali.
Anty bari na baki labarin iskanci da Najwa tayi min jiya a online da dare, lokacin kinyi barci, nake tambayarta ta fito mana da anko, wai idan ma ta fito da shi meye nawa a ciki, ai sai dai nayi na iyaye dan bana cikin ƙawayenta. Wallahi ko bikin ma in yazo bazan je ba dan tayi kaɗan ta wulaƙanta ni.
Kema banda abinki Ikram idan tana so muyi ai har gida zata zo ta kawo mana, dan haka sai ta sha kuruminta ankonmu daban za muyi yan nan gidan.
A'a ba zai yuwu ba idan kuka yi haka kun biye mata kenan, har yanzu Najwa da ƙuruciya akanta sannan ma kin san bakwa shiri tun rabuwarsu da yayanki amma kika takalo ta, gani zata yi kamar gatse kika yi mata da tambayar. Ni bana son ku saka a ranku dan zumuncinku mai karfi ne, kuma ita kaɗai ce mace a gidansu na tabbatar daku zata yi jiki sosai in hankalin aure ya shiga jikinta.
Hmmm Allah ya kyauta amma Allah Umma bazan yi ankonta ba zan saka wanda Allah ya bani. Yauwa Anty zaki samu zuwa walimar ƙanin Khairy kuwa? dan kamar gobe Lahadi ne ko? in zaki sai ki jirani na dawo daga makaranta mu tafi tare.
Keni ba inda zani wannan sha'ani ne na masu hannu da shuni bazan je ayita yi mini gani gani ba.
Haba Anty wlh kema kin san ba kalar wacce za a kalla bace ayi miki wulaƙanci.
Ba inda zani, bayan an gama taron zan shirya naje gidanta na bata haƙuri nasan zata sauko tunda ban taɓa ma zuwa gidanta ba.
A'a Sameeha yarinyar nan da zuciya ɗaya take tare dake dan sosai take nuna miki so, ina ganin ya dace kije mata koda ba zaki daɗe ba tunda ma kin yi waya da 'yan gidansu ba lallai ayi miki wulaƙanci ba balle kina kama da 'yar uwarsu.
Hmmmm umma tunda kinsa baki zani amma gaskiya bazan daÉ—e ba kinsan ni ban cika son shiga inda ba a sanni ba.
Allah ya kaimu goben lafiya sai ki tafi da motarki in ma rainin ne baki so.
Cewar Umma, Sameeha ta ce cikin murmushi.
Wlh umma sam motar ta fice mini a rai baki ga ko fita zanyi sai dai Yaya ya kaimu tunda shike hawanta.
Wlh Anty da ita zaki kuma ke zaki tuƙa ai ajinki ne wannan ba arowa kika yi ba taki ce, yadda yaya Zaidu ya saka aka yi mata sabon fenti ta ƙara kyau aiko kin goge raini.
Murmushi tayi tana kallon Ikram da take jajjada magana, ta cigaba da cewa.
Anwar da safe in Allah ya kaimu ya wanke miki ita, sai ki sanar da yaya Zaidu anjima in ya dawo yasan zaki fita da ita.
To mama Ikram zanyi abinda kika ce uwar iya tsara zance.
Sameeha ta faɗa tana dariya, wayarta data yi ƙara yasa ta duba sai taga Number ɗin Aminu ne ke kiranta, dam ƙirjinta ya buga sosai dan tasan ya yi blocking ɗinta, sai da wayar ta katse bata ɗaga ba Umma tana cewa.
Waye ya kira naga duk kin sauya kamar an watsawa kaza gishiri.
Umma Aminu ne ya kirani kuma...
Bata ƙarasa maganar ba wani kira ya ƙara shigowa, da sauri ta ɗauka tana karawa a kunne tare da yin shuru, muryar Amrah daya doki kunenta yasa ta miƙe zumbur tana ambaton sunanta.
Amrah! Amrata muryanki ne haka ina Abi kuna lafiya ya makaranta.
Sameeha ta faÉ—a cikin tsantsar murna da farin ciki tana jera mata tambaya, Amrah ta ce cikin murna.
Mamanmu muna lafiya Abba yaƙi bari muzo gunki wai sai mun ƙara yin hutun makaranta, yanzu ma saida nayi masa kuka kafin ya yarda ya kiraki, dan Allah mama ki dawo gidanmu Abba yace wai hutu kike yi a gida, dan Allah ki gama hutun ki zo.
Dalla malama bani nima inyi magana da ita.
Cewar Abi daya fizge wayar a hannunta ya ƙara a kunne, nan shima ya shiga magiyar akan ta dawo gidansu, Sameeha kasa daurewa ta yi sai ta fashe da kuka mara sauti tama kasa yiwa yaran magana sai tsiyayar hawaye, sai ta koma ta zauna tana toshe bakinta dan kar suji kukanta, Abi da Amrah sau kiran mama suke yi dan sun koma sun saka wayar a hands free, da kyar ta rarrashi kanta tace.
Kuyi haƙuri kun ji watarana zan zo na ganku, kuma koda ban zo ba Abbanku zai kawo ku tunda ya yi muku alƙawari ku daina damuwa koda bama tare zuciyata tana tare daku, sannan ku mayar da hankali a karatunku domin shine gatanku a duniya, banda ƙawaye da abokai marasa tarbiyya ku riƙa tuno duk abubuwan dana ke faɗa muku akan aboki nagari da kuma mayar da hankali a karatu, ina sonku kuma duk runci zuciyata tana tare daku.
Ta ƙare cikin kuka, Abi ya jefa mata tambaya.
Mama kuka kike yi Abba ya rabamu ko.?
A'a Abi ba kuka nake ba kuma abbanku bai rabamu ba tunda kuna tunani a zuciyarku nima ina tunaku ko ba kwa yi.?
Taf kullun sai na tunaki mama.
Nima ina tunaki mama kusan kullun sai na yiwa Abba kuka ma.
Cewar Amrah cike da yarinta, haka suka ɓata lokaci tana hira dasu, wani lokacin ta yi hawaye wani lokaci tayi dariya abin kallo ta zamewa su umma suna kallon ikon Allah, sunyi kusan minti arba'in suna magana daga bisani taji muryan babansu yana cewa.
Wayar ya isa haka ku bani ita nan.
Mama sai mun sake kiranki kuma muna hutu zamu zo, ki cewa kaka umma ta tanadar mana waina dan shi zamu ci da mun zo mu cika cikinmu.
To to take ce musu tana gyaɗa kai kamar suna ganinta, tana ji ya kashe wayar ta sauke wani numfashi tana mai jingina da bango ta fashe da sabon kuka, wai tsakaninta da 'ya'yanta ne ya zama sunyi nisan da sai da suka shafe watanni bata gansu ba kuma da ranta da labari, haƙiƙa duk wanda da saka hannunsa a mutuwar aurenta ba zata yafe masa ba dan sun farraka mata farin cikinta, a yadda Aminu bayi da lafiya ta ɗauki alƙawarin zama da shi a haka kodan saboda yaranta, tunda Allah ma bai ɗaura mata mugun sha'awa ba kuma ance sa rai da ci shike kawo jin yunwa. Umma ta matso ta dafata.
Duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa Sameeha, Allah yana sane da halin da kika tsinci kanki, kuma zai kawo miki mafita ta alkhairi alfarman Manzon Allah s.a.w ba zaki taɓa taɓewaba In Sha Allah rayuwar sai tayi albarka, ki ƙara haƙuri akwai lokacin da zaki yi dariya duk sai kin manta da wannan ƙuncin.
Maganganun umma su suka ƙara sanyaya mata rai ta goge hawayenta tana cewa.
Amin Umma Allah ya amsa addu'arki.
Ikram ta amsa da amin tare da cewa.
Ku taso mu shiga ɗaki kun san yau asabar lokacin maimaicin Azrah yayi saboda jiya bamu kalla ba yanzu ƙarfe uku.
Tana gama faɗa ta shige ɗaki suma suka bi bayanta dan suna son shirin sosai, kallon da suka fara yasa Sameeha ta ware sai dai tunanin yaranta yana maƙale a zuciyarta sai dai kawai dangana tayi ba yadda zata yi.
.
..
Washe gar, wajen ƙarfe biyun rana Sameeha ta shirya cikin doguwar rigar lashe wanda sabon ɗinki ne da Aminu yayi mata wanda zata saka a bikin Salma sai dai Allah bai nufa zata saka a lokacin ba, kusan dubu sittin da uku yake, bata taɓa saka shi ba sai yau shima dan Umma tace dole ta saka shi tunda sha'anin manya ne zasu, ta saka farin gyale da kuma farin takalmi da jaka, dan leshin orange da fari ne a jiki mai manyan zane, Ikram kuwa atamfa ta saka riga da siket sai ta ɗaura after dressing shara shara a sama mai hula, bata saka gyale ba ganin ta saka wanan kuma a mota zasu gashi ta caɓa uban ado kuma tayi kyau, Sameeha kuwa daga powder sai kwalli sai man baki data saka, Ikram ta kalleta.
Anty dan Allah kiyi kwalliya mana.
Ikram wa zan burge a can? ai kawai mu tafi haka dan kinsan ni kwalliya bata dame ni ba. Umma mu zamu wuce in kin ga mun dawo da wuri bamu samu fuska ba amma in mun jima to fa mun samu tarba mai kyau.
To Allah ya tsare yasa ayi taro lafiya ki gaida Khairy, ina taya su murna.
Zata ji In Sha Allah.